Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Neymar na son ya koma PSG tare da Coutinho
 2. Sanchez zai fara atisaye a ranar Talata
 3. Labaran da jaridun Turai suka wallafa kan tamaula
 4. Mcllroy ya raba gari da mai yi masa hidima

Rahoto kai-tsaye

time_stated_uk

 1. 'Alex Sandro ba zai bar Juventus ba'

  Daily Star cewa ta yi kocin Juventus Massimiliano Allegri ya shaidawa Chelsea cewar ba zai sayar mata da Alex Sandro ba.

  Kai tsaye
 2. Inter za ta yi zawarcin Sadio Mane

  Daily Express ta wallafa cewar Inter Milan ta Italiya na son taya dan kwallon Liverpool, Sadio Mane mai shekara 25, wanda za ta taya kan fam miliyan 35.

  Kai tsaye
 3. Diego Costa na neman kungiya

  Dan wasan Chelsea, Diego Costa ba zai yi atisaye da 'yan kwallon Chelsea ba domin tunkakar kakar da za a fara, bayan da yake ta neman klub din da zai koma da taka-leda in ji Marca.

  Kai tsaye
 4. 'Bolt zai zama abin koyi ga matasa'

  Usain Bolt zai dace da aikin koci idan ya yi ritaya, in ji mai horar da tawagar Jamaica Glen Mills.

  Bolt zakaran gasar Olympic wanda ya ci lambar zinare takwas, zai yi ritaya bayan gasar tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya da za a yi a Landan a watannan.

  Mills ya ce Bolt zai zama abin koyi ga matasa a fagen wasa.

  Kai tsaye
 5. 'Klopp ba zai sayi dan wasa mai buga tsakiya ba'

  Jaridar Independent ta ce tsohon dan kwallon Liverpool, Jamie Carragher ya ce Jurgen Klopp ba zai sake sayen dan wasa mai buga tsakiya ba a bana, duk da kin sayar masa da Naby Keita da RB Leipzig ta yi.

  Kai tsaye
 6. Coutinho zai ci gaba da zama a Liverpool

  Kai tsaye
 7. Karen Bardsley ba za ta buga wa Ingila wasa ba

  Mai tsaron ragar tawagar kwallon kafar mata ta Ingila, Karen Bardsley ba za ta karasa wasannin cin kofin nahiyar Turai ba, sakamakon raunin da ta yi.

  Bardsley ta yi rauni ne a karawar da Ingila ta ci Faransa a wasan daf da na kusa da na karshe, kuma Siobhan Chamberlain ce ta canje ta a fafatawar.

  Ingila za ta buga wasan daf da karshe da Netherlands a ranar Alhamis, tuni tsohuwar mai tsaron ragar Ingila, Rachel Brown-Finnis ta ce tana sa ran Chamberlain za ta taka rawar gani.

  Kai tsaye
 8. Paris za ta karbi gasar Olympic ta 2024

  Mahukuntan birnin Los Angeles din Amurka, sun sanar da cewar an ba su izinin karbar bakuncin wasan Olympic na shekarar 2028.

  Hakan kuma na nufin birnin Faris din Faransa ne zai fara karbar fafatawar da za a yi a 2024 kenan.

  Kai tsaye
 9. Autan Mai Turare a wakar da ya yi wa Horo

  Video content

  Video caption: Autan Mai Turare a wakar Ashiru Horo
 10. Sharapova ta doke Brady

  Maria Sharapova ta doke Jennifer Brady da ci 6-1 4-6 da 6-0 a gasar Stanford West Classic, bayan jinya da ta yi.

  Sharapova wadda ta dawo atisaye a cikin watan Afirilu, an hana ta wasa wata 15 sakamakon samunta da laifin shan abubuwa masu kara kuzari da aka yi.

  Kai tsaye
 11. An ci tarar Nathan Redmond

  An ci tarar dan kwallon Southampton, Nathan Redmond fan 1,000, bayan da aka sameshi da laifin gudun wuce sa a a cikin motarsa ta Range Rover wadda ta take fan 80,000 in ji Daily Mail.

  Kai tsaye
 12. Fernando zai koma Galatasaray

  Dan wasan tawagar Brazil, Fernando na daf da komawa Galatasaray daga Manchester City.

  Dan kwallon mai shekara 30 ya koma taka-leda a City daga Poto kan fam miliyan 12 a shekarar 2014.

  Fernando ya buga wa City wasa 101, ciki har da 27 da ya murza-leda a kakar da ta kare, bai kuma halarci wasannin atisayen da kungiyar ta yi a Amurka a Yuli ba.

  Kai tsaye
 13. Takaitattun Labaran Wasanni

  Video content

  Video caption: Takaitattun Labaran Wasanni
 14. Jesus Navas ya koma Sevilla

  Dan wasan tawagar kwallon kafar Spaniya, Jesus Navas ya sake koma Sevilla daga Manchester City, kan yarjejeniyar shekara hudu.

  Kai tsaye
 15. Jagaba wajen cin kwallo a gasar Firimiyar Nigeria

  Bayan da aka buga mako na 32

  Kai tsaye
 16. Ter Stegen da Gomes sun koma atisaye

  'Yan wasan Barcelona Ter Stegen da kuma Andre Gomes sun koma atisaye a kungiyar bayan da aka duba lafiyarsu.

 17. Yawan wasa kwallo bai shiga raga ba

  Gasar Premier Nigeria bayan mako na 32

  Kai tsaye
 18. Fiorentina za ta dauki Emre Mor

  Fiorentina za ta taya dan kwallon Borussia Dortmund, Emre Mor kan Yuro miliyan 10 in ji jaridar La Nazione, sai dai kuma Dortmund za ta bukaci kudin da aka taya dan kwallon.

  Kai tsaye
 19. An ci kwallo 626 a gasar Firimiyar Nigeria

  Bayan da aka kammala wasannin mako na 32 a gasar Firimiyar Nigeria, a karshen mako an ci kwallo 626 a wasa 318 da aka fafata.

  Kuma kwallo 482 kungiyoyin da suka buga wasa a gida suka ci, yayin da zura 144 a waje.

  Plateau United ce ta daya a kan teburi da maki 58, sai Mountain Of Fire ta biyu da maki 55, Akwa tana ta uku da maki 51.

  Kai tsaye
 20. Monaco za ta maye gurbin Mbappe

  Rahotanni na cewa Monaco na shirin maye gurbin Kylian Mbappe da dan kwallon Ajax Kasper Dolberg.

  Real Madrid ce ke son daukar Mbappe dan wasan tawagar Faransa.

  Kai tsaye