Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Barca ta bai wa Neymar damar tafiya PSG
  2. Dan kwallon bai yi atisayi ba
  3. Cinikin zai kai fan miliyan 198
  4. Man United na neman Aurier
  5. Chelsea na son sayen Drink Water
  6. Liverpool ta lallasa Bayern Munich 3-0
  7. Bolt zai yi ritaya a watan Agusta

Rahoto kai-tsaye

Daga Naziru Mikailu da Mohammed Abdu

time_stated_uk

Nan muka kawo karshen shirin

tare da fatan za ku tara a ranar Alhamis domin jin wani sabon shirin labarin wasannin kai tsaye.

City ta bukaci a sayi Iheanacho fam miliyan 50

Daily Telegraph ta ce Manchester City ta tsaya kai da fata a kan fam miliyan 50 za a biya wajen sayen dan wasanta Iheanacho.

Kai tsaye
Getty Images

Iheanacho na daf da komawa Leicester City

Jaridar Leicester Mercury kuwa cewa ta yi, Leicester ta kammala duba lafiyar dan wasan Manchester City, Kelechi Iheanacho mai shekara 20, wanda ya amince zai karbi fam miliyan 25.

Kai tsaye
Reuters

Peaty ya ji dadin bajintar da ya yi a Budapest

Adam Peaty ya ce ya ji dadi duk da matsin da ya sha ya kuma jagoranci Burtaniya a gasar linkaya ta duniya da aka yi Budapest.

Peaty ya ci lambar zinare uku a wasannin, ciki har da wadda ya lashe a tseren mita 50 da ta mita 100.

Kai tsaye
Getty Images

Roma ta karrama Totti

Roma ta karrama tsohon dan wasanta Francesco Totti ta hanya harba rigar da ya sawa kungiyar zuwa sararin samaniya.

A ranar Talata aka harba wani kumbo a Guyanan Faransa dauke da riga mai lamba 10 ta Totti wacce ya sawa Roma a wasan karshe da ya buga da Genoa.

Dan wasan mai shekara 40, ya yi wa Roma wasa shekara 24, daga baya ya rataye takalmansa a watan Mayu, zai kuma karbi aikin darakta a kungiyar.

Kai tsaye
Roma

Athletics

Zakaran tseren Olympic wanda ya ci zinare takwas Usain Bolt ya ce zai so ya ci gaba da wasannin tsere bayan gasar duniya da za a yi a Landan.

Sai dai Bolt mai shekara 30 ya ce ya yi fama da rauni a shekarun baya, kuma lokaci ne da ya komata ya yi ritaya. A ranar 4 ga watannan Landan za ta karbi bakuncin wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya.

Kai tsaye
Getty Images

Football

A ranar Alhamis za a buga kwantan wasan mako na 27 a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria tsakanin tsakanin Kano Pillars da Rivers United.

Kano Pillars tana ta 10 a kan teburi da maki 44, ita kuwa Rivers United ita ce ta 16 da maki 41.

Plateau United ce ta daya da maki 58.

Kai tsaya
LMCNPFL

Griffiths zai buga wa Celtic wasa

Ana sa ran dan kwallon Celtic Leigh Griffiths, zai fafata a wasan cike gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai inda zasu kara da Rosenborg, bayan da ya warke daga raunin da ya yi.

Kungiyoyin biyu sun tashi wasa babu ci a karawar farko da suka yi a Celtic.

Messi ya yi wa Neymar ban kwana

A kokarin da PSG ke yi na kokarin daukar dan wasan tawagar Brazil Neymar a bana daga Barcelona, tuni abokin wasansa Lionel Messi ya yi masa ban kwana.

View more on instagram

Damben Nuran Dogon Sani da Garkuwan Shagon Alabo

United na son Leander Dendoncker

Jaridar Manchester Evening News ta ce Manchester United tana son sanin jin bahasi kan dan wasan Anderlecht, Leander Dendoncker mai shekara 22, sai dai ana ganin ba za ta sayi shi a bana ba.

Kai tsaye
Getty Images

Hearts ta nada Daly kocin rikon kwarya

Kungiyar Hearts ta sanar da cewar ta nada Jon Daly a matsayin kocin rikon kwarya.

Kocin shi ne zai ja ragamar kungiyar a wasan makon farko da za ta kara da Celtic mai rike da kofin gasar Scotland a ranar Asabar.

Daly wanda ya horar da matasan kungiyar 'yan kasa da shekara 20, ya maye gurbin Ian Cathro wanda Hearts ta kora bayan da ya kasa taka rawar gani.

Sturridge ba zai buga wa Liverpool wasa ba

Daniel Sturridge ba zai buga wa Liverppol gasar Audi Cup da za ta kara da Atletico Madrid idan an jima ba.

Dan wasan ya yi rauni a fafatawar da Liverpool ta ci Bayern Munich 3-0 a daren jiya. Sai dai Liverpool ba ta yi shirin auna raunin da ya ji ba.

Kai tsaye
Getty Images

Dole PSG ta biya kudin Neymar a dunkule

Barcelona ta shaida wa Paris St-Germain cewa dole ne ta biya fan miliyan £198m a dunkule idan har za ta sayi Neymar.

Da safiyar ranar Laraba ne dan wasan na Brazil tare da rakiyar mahaifinsa da kuma wakilansa suka shaida wa Barcelona aniyarsa ta barin kungiyar, a wani taro da aka yi a ofishin kulub din.

Kuma kungiyar ta bashi damar tattaunawa da kungiyar.

Neymar
Getty Images

'Sanchez ba zai buga Premier ba idan ya bar Arsenal'

Times ta wallafa cewar Arsene Wenger ya shaida wa dan wasan Arsenal Alexis Sanchez mai shekara 28, cewar ba za a sayar da shi ga wani kulob din da ke buga gasar Premier a wannan kakar ba.

Kai tsaye
Getty Images

Tottenham ta so ta dauki Morata

Kocin Tottenham, Mauricio Pochettino ya sanar da tattaunawar da suka yi da dan wasan Chealse Alvaro Morata kan ya koma Tottenham da wasa, sai dai dan kwallon mai shekara 24 ba ya son yin takara da Harry Kane. In ji jaridar Daily Mail.

Kai tsaye
Getty Images

Barca ta yi karin haske kan Neymar

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fitar da sanarwa kan halin da ake ciki game da dan wasan kulob din Neymar, wanda ta bai wa damar barinta domin komawa PSG.

Sanarwar ta yi bayani kamar haka:

Nerymar
Getty Images

Da safiyar ranar Laraba ne dan wasa Neymar Jr bisa rakiyar mahaifinsa da kuma wakilansa suka shaida wa Barcelona aniyarsa ta barin kungiyar, a wani taro da aka yi a ofishin kulub din. Dan gane da kwantiraginsa, Kulub din ya shaida musu cewa akwai yarjejeniya da aka kulla wacce ta nemi a biya su Yuro miliyan 222, kuma a lokaci daya za a biya kudin. A daya bangaren kuma, wato kan batun garabasar da ke cikin yarjejeniyar da aka kulla lokacin da ya sabunta zamansa, kulob din ya jaddada cewa tana nan a ajiye har san an cimma matsaya kan wannan batu. Har yanzu dan wasan na nan a matsayinsa na dan Barcelona. Sai dai an ba shi da damar kin yin atisaye domin ya tattauna makomarsa.

Barcelona

Za a fara gasar tsalle-tsalle da guje-guje a Landan

A ranar 4 ga watan Agusta zuwa 13 ga watan za a fara gasar tsalle-tsale da guje-guje a Landan.

Kai tsaye
Getty Images

Ivory Coast za ta iya karbar bakuncin kofin Afirka

Shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara ya ce kasarsa ba ta bukatar yin hadakar karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2021.

Shugaban ya ce Ivory Coast za ta iya karabar bakuncin kasashe 24 da za su fafata a gasar.

Hukumar kwallon kafa ta Afirka ta bai wa Ivory Coast damar karbar bakuncin kasashe 16, amma a watan Yuli ta kara mambobin da za su kece raini a gasar zuwa 24.

Suna da filaye da dukkan abubuwan da ake bukata wajen karbar gasa, za kuma su ci gaba da bunkasa su har 2021.

Alassane Ouattara
Kai tsaye
BBC Sport

Takaitattun Labaran wasanni

Rawar da Neymar ya taka...

A daidai wannan lokacin kuma, ya kasance na biyar ajerin 'yan wasan da suka fi taimaka wa a ci kwallo inda ya ke da 38.

Yana bayan Messi (54), Koke (45) na Athletico Madrid, Suarez (43) da kuma Ronaldo (42).

Neymar da Messi
Getty Images

Rawar da Neymar ya taka...

Tun bayan zuwansa Barca a 2013, Neymar ya zura kwallo 68 a kaka hudu da ya buga.

Wannan na nufin yana bayan Ronaldo (139), Messi (134), Luis Suarez (85), Antoine Griezmann (76) da kuma Aritz Aduriz (70) na Athletic Bilbao.

"Bajinta ce haka" ko kuwa dai kawai "ba yabo ba fallasa"?

Neymar da Messi
Getty Images

Dole a rage shan miyagun kwayoyi a wasanni - Bolt

Zakaran tseren duniya Usain Bolt ya ce dole 'yan wasa su rage shan miyagun kwayoyi a daidai lokacin da yake shirin tunkarar gasarsa ta karshe.

Bolt, wanda ya lashe lambar zinare sau takwas a gasar Olympic, kuma wanda ake wa kallon gagara-badau a fagen wasanni, zai yi ritaya bayan gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da za a yi a wannan watan.

Dan wasan kasar Jamaica, mai shekara 30, zai yi gudu a tseren mita 100 da kuma 4x100m a gasar, wacce za a fara a birnin Landan ranar Juma'a.

Ya ce: "Ina fatan 'yan wasa za su yi la'akari da abin da yake faruwa da kuma abin da ya kamata su yi su ciyar da wasan gaba".

Bolt ya lashe tseren 100m, 200m da 4x100m a gasar Olympic uku da ta gabata a jere - Beijing 2008, London 2012 da kuma Rio 2016.

Usain Bolt
BBC

Me zai faru ga PSG idan ta sayi Neymar?

Sanarwar da aka bayar cewa Barcelona ta bai wa Neymar damar tattaunawa da PSG ta fara janwo ce-ce-ku-ce.

Wannan na zuwa ne kwana biyu bayan an ruwaito cewar Barca ta shirya domin ta kai karar PSG domin kaucewa ka'idar kashe kudi wurin sayen 'yan wasa idan har ta sayi Neymar.

Kuma wannan ya biyo bayan gargadin daukar matakin shari'a da shugaban hukumar gasar La Liga, Javier Tebas, ya yi idan hukumar kwallon kafa ta Turai ta kasa daukar mataki.

Ya kuma ce an sanar da shugaban PSG, Nasser Al-Khelaifi, abubuwan da kungiyar kwallon kafa ta Spaniyar ke da niyyar yi.

Neymar
Getty Images

Neymar ya koma Barcelona daga kungiyar Santos ta Brazil, a shekarar 2013 kan kudi fam miliyan 48.6, kuma ya sake rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ta shekara biyar da kungiyar bayan da ta ci kofinta na zakarun Turai a 2016.

Wasu rahotanni sun ce Neymar zai je Doha, babban birnin Qatar, domin ganawa da shugaban kulob din na PSG.

Chelsea 'na zawarcin Drinkwater'

Rahotannin da ke fito wa daga Ingila na bayyana cewa zakarun gasar Premier Chelsea na zawarcin dan kwallon Leicester City Dani Drinkwater.

Kawo yanzu dai Leicester ba ta ce uffan ba game da wadannan rahotanni, amma a baya ta nuna sha'awar rike dukkan 'yan wasanta.

Sannan tana yunkurin sayen wasu sabbi.

Dani Drinkwater
Getty Images

Liverpool ta doke Bayern Munich 3-0

Liverpool ta doke Bayern Munich da ci 3-0 a wasan kusa da na karshe na gasar Audi Cup.

Sai dan wasan gabanta Daniel Sturridge, wanda ya zira kwallo ta uku, ya samu rauni.

An maye gurbinsa a minti na 87, inda koci Jurgen Klopp ya ce yana fatan raunin "ba mai muni ba ne".

Sadio Mane da Mohamed Salah ne suka zura sauran kwallo biyun, wanda hakan ya bai wa Liverpool damar karawa da Atletico Madrid a wasan karshe ranar Laraba.

Mane ne ya fara zira kwallon farko a minti na shida bayan wata dabara da Roberto Firmino ya yi.

Sannan kuma dan wasan na Senegal ya taimaka wa Salah ya zira kwallo ta biyu.

Daniel Sturridge
Getty Images

Neymar zai koma Barca

Neymar
EPA

Barcelona ta bai wa Neymar damar barin kulob din a daidai lokacin da ake ganin dan kwallon zai koma Paris St-Germain a kan kudi fan miliyan 198.

Dan wasan na Brazil, mai shekara 25, ya shaida wa abokan wasansa cewa yana son barin kungiyar.

Koci Ernesto Valverde ya bashi damar kada ya yi atisayi domin ya mayar da hankali kan makomarsa.

Akwai yarjejeniya a kwantiraginsa cewa duk kulob din da ke son daukarsa sai ya biya fan miliyan 198.

An bai wa Neymar damar barin Barca

Barcelona ta bai wa Neymar damar barin kulob din a daidai lokacin da ake ganin dan kwallon zai koma Paris St-Germain a kan kudi fan miliyan 198.

Dan wasan na gaba bai yi atisayi da takwarorinsa ba.

A wani sakon Twitter da kulob din ya wallafa, ya ce dan wasan na Brazil mai shekara 25, bai yi atisayin ba ne da izinin kocin kungiyar.

Neymar Jr no se entrena con permiso del técnico #FCBlive

Barkanmu da Hantsi

Jama'a barkanmu da sake saduwa da ku a yau Litinin, inda kamar kullum muke kawo muku irin wainar da ake tonawa a fagen wasanni, musamman a fannin hada-hadar 'yan kwallon Turai.