Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Neymar zai fi kowa daukar albashi
 2. Shin wane ne zai maye gurbin Neymar a Barcelona
 3. Man United na neman Serge Aurier
 4. Kwantan wasa: Kano Pillars za ta kara da Rivers United
 5. Za a fara gasar tsere da guje-guje a Landan

Rahoto kai-tsaye

Daga Naziru Mikailu, Mohammed Abdu da Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. Nan muka kawo karshen shirin

  Tare da fatan za ku tara a ranar Litinin domin jin wasu labaran wasanni kai tsaye.

 2. Labarai da dumi-dumiNeymar ya fanshi kansa a Barcelona

  Barcelona ta sanar da cewar Neymar ya biya kudin kunshin yarjejeniyar barin kungiyar na fam miliyan 200 da aka sawa duk wata kungiya da take son daukarsa kafin yarjejeniyarsa ta kare.

  Ana sa ran Neymar zai saka hannu kan kwantiragi mafi tsada a duniya a Paris St-Germain, bayan da ya nemi bukatar barin Barcelona a ranar Laraba.

  Kai tsaye
 3. 'Roma ba za ta kara kudin da ta taya Mahrez ba'

  Daraktan wasannin Roma, Monchi ya ce ba zai kara kudi a kan tayin da ya yi wa dan kwallon Leicester Riyad Mahrez kan kudi fam miliyan 35 ba.

  Sai dai Shakespeare ya ce Mahrez ba ya son taka-leda a Italiya. A yanzu dai Roma na son zawarcin Munir da Emre Can.

  Kai tsaye
 4. Barcelona za ta maye gurbin Neymar

  A cewar Sun Sport Barcelona na shirin kashe Yuro miliyan 222 kudin sayar da Neymar ga PSG, domin ta sayo Coutinho da Hazard.

  Kai tsaye
 5. Kwantan wasa Pillars da Rivers

  Rivers United tana daga cikin kungiyoyi 9 da ba su ci wasa ba a fafatawar da suka yi a waje. ta yi canjars hudu an doke ta sau 11.

  Kai tsaye
 6. Kwantan wasan Pillars da Rivers

  Kano Pillars ta ci wasa shida a jere a gida, tun bayan rashin nasara da ta yi a hannun Akwa United da ci daya mai ban haushi a ranar 9 ga watan Afirilu

  Kai tsaye
 7. Dan Sama'ila ya buge Shagon Samsu

  Damben gargajiya tsakanin Dan Sama'ila da Shagon Shamsu Kanin Emi, wanda da farko wasan ya jo da takaddama.

  An yi wasan ne a gidan Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria

  Daga baya Dan Sama'ila ya yi nasara.

  Video content

  Video caption: Damben na su ya zo da takaddama
 8. Mbappe ya ce yana son ya koma Madrid

  Jaridun Faransa sun bayyana cewar Kylian Mbappe ya shaida wa Monaco cewar zai bar kulob din, domin yana so ya koma Real Madrid da murza-leda.

  Kai tsaye
 9. Post update

  Bayan da Bonucci ya bar kungiyar Juventus, tuni ta koma harin matashin dan wasan Real Madrid, Benjamin Kuscevic.

 10. Bolt ya ce da kyar a sami mai gadonsa

  Da zarar an kammala gasar tsale-tsalle da guje-guje da za a fara a Landan a ranar 4 ga watan Agusta zuwa 13 ga watan, dan wasan tseren Jamaica, Usain Bolt zai yi ritaya.

  Sai dai ya ce da wuya a samu wanda zai gaje shi.

  Video content

  Video caption: Shan kawayoyi zai kashe wasanni-Usain Bolt
 11. Takaitattun Labaran Wasanni

  Takaitattun Labaran wasanni da muka gabatar da safiyar Alhamis

  Video content

  Video caption: Takaitattun Labaran Wasanni
 12. Yadda Neymar ya bayyana aniyarsa ta barin Barca

  A ranar Laraba ne dan wasan Brazil Neymar ya shaida wa Barcelona cewa yana so ya bar kungiyar.

  Dan kwallon ya isa filin atisaye tare da mahaifinsa da kuma wakilinsa, inda suka yi dan gajeren taro da shugabannin kulob din.

  Daga nan ne kuma koci Ernesto Valverde ya bashi izinin ficewa daga filin atisaye domin ya mayar da hankali kan batun makomarsa.

  Daga bisani kuma sai Barce ta fitar da sanarwa inda ta ce duk da cewa har yanzu yana da kwantiragi da ita, ta bashi damar tattauna makomarsa.

  Amma kuma ta ce wajibi ne PSG ta biya fan miliyan 198 lakadan domin sayensa.

  Neymar
 13. Negredo ya koma Besiktas

  Bayan da Besiktas ta sanar da daukar Negredo a ranar Laraba, Valencia ta shaida a safiyar Alhamis cewar dan wasan ya koma buga gasar ta Turkiya.

 14. Pillars da Rivers United

  Za a buga kwantan wasan mako na 27 tsakanin Kano Pillars da Rivers United a gasar Firimiyar Nigeria a ranar Alhamis a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano, Nigeria.

  Kai tsaye
 15. An ki tayin Arsenal kan Dembele

  Borussia Dortmund ta ki tayin Dembele daga Arsenal, in ji Mundo Deportivo

  Ousmane Dembele
 16. Neymar: La Liga ta ki karbar kudin PSG

  Wakilan PSG da Neymar sun isa ofisoshin La Liga ranar Alhamis domin biyan Fam miliyan 198 da zai sa Barcelona ta sake shi.

  Wata sanarwar da aka aika wa BBC ta ce:

  "Za mu iya tabbatar da cewar lauyoyin dan wasan (Neymar) sun zo La Liga domin ba da kudin fansarsa kuma an ki karbar kudin. Wannan ne iya bayanin da za mu iya bayarwa a yanzu."

  Hukumar tana ganin ba zai yiwu ba PSG ta biya kudin Neymar ba tare da take dokokin adalcin ciniki da hukumar Uefa ta kakaba ba.

  Neymar
 17. Mbappe zai bar Monaco

  Dan wasan gaban Monaco mai shekara 18, Kylian Mbabppe ya yanke shawarar barin kungiyar, yayin da Real Madrid, da Manchester City da kuma Paris Saint-Germain suka fara rige-rigen sayansa, in ji jaridar L'Equipe.

  Barcelona ta riga ta tuntunbi Monaco kan sayan dan wasan gaban Faransan mai daraja, in ji Le10Sport

  Kylian Mbappe
 18. Neymar bai yi tsada ba - Mourinho

  Cinikin Neymar na Fam miliyan 198 da zai sa ya koma Paris-St Germain bai yi tsada ba, amman zai janyo matsala, in ji Jose Mourinho.

  Dan wasan gaba na Brazil din, mai shekara 25, ya shaida wa Barcelona cewar yana son ya bar ta ranar Laraba.

  Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp, ya soki cinikin bisa da'ar adalcin hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA, kan ciniki.

  Cinikin Neymar zai dara na Paul Pogba da ya kafa tarihi a matsayin ciniki mafi tsada da kudi fiye da Fam miliyan 100 a lokacin da ya koma Manchester United daga Juventus.

  Mourinho ya ce: "Masu tsada su ne wadanda suka kai ga wani mataki ba tare da wasu ire-iren kwarewa ba. A kan kudi fam miliyan 200, ba na tunanin Neymar yana da tsada.

  "Ina ganin yana da tsada kan cewar a yanzu za a iya samun karin 'yan wasa kan kudi fam miliyan 100, za a samu karin 'yan wasa kan Fam miliyan 80 da kuma karin 'yan wasa kan Fam miliyan 60. Kuma ina ganin wanna ita ce matsalar."

  Mourinho
 19. Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp, bai ji dadin cinikin Neymar ba

  Sabanin kalaman Mourinho, Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp, bai ji dadin cinikin Neymar mai cike da tarihi ba.

  Ya ce: "Akwai kulob-kulob da ka iya biyan irin wannan kudaden, Manchester City da PSG. Kowa ya san wannan.

  "Ina tunanin an kafa da'ar adalci ne saoda a hana aukuwar irin wannan lamarin. Amman wannan ta fi kama da shawara fiye da doka.

  "Ban gane hakan ba. Ban san yadda ya faru ba."

  Jurgen Klopp
 20. Wa zai maye gurbin Neymar?

  Philippe Coutinho

  Tun bayan da dan wasan Brazil Neymar ya ce zai bar Barcelona, ake ta rade-radi da hasashen wanda zai mare gurbinsa.

  Wasu dai na ganin Barca za ta yi kokarin sayen takwaransa na Brazil kuma dan Liverpool Philippe Coutinho.

  Tuni dai dama aka ce suna nemansa tun kafin Neymar ya ce zai bar kungiyar.

  Sai dai ganin makudan kudin da za su karba kan Neymar, babu shakka duk dan wasan da za su nema, to sai aljihunsu ya yi kuka.