Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Naziru Mikailu, Mohammed Abdu da Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. Barcelona ta cimma yarjejeniya da Dembele

  Barcelona ta cimma yarjejeniya da dan wasan Borussia Dortmund mai shekara 20, Ousmane Dembele, amman yanzue dole ta cimma matsaya da kungiyar kwallon kafa ta Jamus din wadda ke neman kusa da Fam miliyan 90.2 a kan dan wasan in ji jaridar L'Equipe

  Dembele
 2. 'Sanchez ya rungumi kaddara'

  Dan wasan gaban Chile, Alexis Sanchez, mai shekara 28, ya shirya domin ya rungumin kaddara kan kin sayar da shi da Gunners ta yi, ya kuma karasa shekara daya da ta saura a kwantiraginsa kafin ya bar kulob din a kasuwar 'yan wasa na badi, in ji jaridar Mirror.

  Sanchez
 3. 'Yan wasa sun yi min yawa -Wemger

  Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce karin 'yan wasa za su bar Gunners kafin a rufe kasuwar 'yan wasa saboda 'yan wasansa sun yi yawa, in ji jaridar Telegraph.

  Wenger
 4. Jurgen Klopp ya fasa sayan Dijk

  Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp, ya shirya domin janye zawarcin dan wasan Southampton, Virgil van Dijk, da yake yi, yana mai amincewa da taka ledan masu tsaron bayan da kulob dinsa ke da shi yanzu, in ji jaridar Mirror.

  Virgil van Dijk
 5. 'Barcelona na son sayan Julian Draxler da kudin Neymar'

  Barcelona za ta iya amfani da wasu daga cikin kudaden da ta samu daga cinikin Neymar domin zawarcin dan wasan PSG, Julian Draxler, dan wasan da aka ga wakilinsa a Barca,in ji jaridar Bild.

  Julian Draxler
  Image caption: Julian Draxler dan wasan Jamus ne
 6. 'Barcelona na da gwarin guiwar sayan Coutinho'

  Duk da cewar kociyan Liverpool, Jurgen Klopp, ya ce Coutinho ba na sayar wa ba ne, Barcelona tana samun kwarin guiwa na cimma yarjejeniyar sayan shi kan kudi Fam miliyan 90 (Kimanin naira biliyan 42) a wannan makon, in ji jaridar Sun.

  Barcelona
 7. Barcelona na za ta taya Countinho

  Barcelona za ta taya dan wasan Liverpool, Philippe Coutinho, mai shekara 25, kan fam miliyan 120 (kimanin naira biliyan 57) bayan ta sayar da Neymar ga Paris St-Germain, in ji jaridar Star

  Coutinho