Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Manchester utd za ta fafata da Real Madrid
 2. Van Dijk ya nemi Southampton ta sayar shi
 3. Klopp ba zai sayar da Philippe Coutinho ba
 4. Shirye-shiryen fara gasar Firimiya sun kankama

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. Sai gobe

  Toh, jama'a abun da ya samu kenan a yau. Ku tara gobe in mai duka ya kaimu inda za mu kawo muku labaran cinikin 'yan wasa kai tsaye daga bbhausa.com

 2. Yaya Karon Manchester United da Real Madrid zai kasance?

  A ranar Talatar nan ne za a fafata wasan cin kofin zakaran zakaru na Turai, Super Cup, tsakanin Manchester United da ta dauki kofin Europa, da Real Madrid wadda ta dauki Champions League, a babban birnin Macedonia, Skopje.

  Idan United ta yi nasara, zai kasance na biyu kenan da ta dauka, bayan na 1991, lokacin da a gidanta Old Trafford ta doke Red Star Belgrade 1-0.

  Kungiyar za kuma ta kasance ta biyu a kungiyoyin Ingila bayan Liverpool mai guda uku, da ta dauki kofin na Super Cup fiye da daya.

  Jose Mourinho ya yi rashin nasara a karawa biyu ta baya a gasar, a matsayin kociya, farko a 2013 yana tare da Chelsea da kuma 2003 lokacin yana horad da FC Porto. Babu wani kociya da ya taba rashin nasarar daukar kofin sau uku.

  Kuma kociyan ya kasance na farko da ya jagoranci kungiyoyi uku a gasar ta Super Cup.

  Kungiyoyin Spaniya ne suka dauki bakwai daga cikin kofin guda takwas da aka fafata a kansu.

  Kungiyar karshe da ta dauki kofin Europa, kuma ta yi nasarar cin kofin na Super Cup, ita ce Atletico Madrid a 2012, lokacin da ta doke, Chelsea wadda ta dauki Champions League 4-1.

  Barcelona ce kawai da AC Milan kofi biyar, suka fi Real Madrid cin kofin, inda take da uku.

  Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin a gasar Turai da cin kwallo 108, da suka hada da biyu a gasar cin kofin na Super Cup.

  Cristiano Ronaldo
 3. Cutar amai da gudawa ta kama 'yan wasa a Landan

  Wata cuta ta amai da gudawa ta kama 'yan gasar duniya ta tsalle-tsalle da guje-guje da ke zaune a wani otal a birnin Landan inda ake yin gasar.

  Hukumomin lafiya na Ingila sun ce kawo yanzu 'yan wasa 30 da wasu jami'ai sun kamu da alamun cutar, kuma an tabbatar da hakan a kan guda biyu.

  Duk da ficewa da ya yi daga gasar tseren mita 200 ta karshe, ranar Litinin bayan da ya kamu har ya yi amai, gwarzon dan tseren Botswana na mita 400 Isaac Makwala ya ce zai yi tseren karshe na mita 400, a Talatar nan.

  A makon da ya gabata ne 'yan wasan Jamus da Canada da ke da masauki a otal din Tower Hotel suka kamu da rashin lafiya.

  Saboda haka ne wata tawagar 'yan wasan Jamus mai mutane 30 za ta sauka a wasu otal otal din daban da wancan, yayin da aka dukufa domin shawo kan matsalar.

  Hukumomin otal din da aka samu cutar, Tower Hotel sun ce binciken da aka yi da jami'an lafiyar muhalli tare da na hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ya nuna cewa ba a otal din ba ne cutar ta samo asali.

  'Yan tsere
 4. Abubuwan da suka faru a Premier bayan shekara 25

  Yayin da ake shirin fara gasar Premier ta bana a karshen makon nan, gasar ta cika shekara 25 da aka bullo da ita, kuma idan aka duba tsawon wannan lokaci an samu sauye-sauye kan yadda take a da, ga kuma tarin abubuwan da suka faru a ciki zuwa yanzu.

  Gasar Premier yadda take a yau ta bambanta da yadda take a da, lokacin da ta faro da kungiyoyin kwallon kafa irin su Oldham da Athletic da Wimbledon.

  A tsawon wannan wannan tafiya ta shekara 25, an yi wasa 9,746, yayin da aka zura kwallo 25,769 a raga, a tsakanin kungiyoyi 47.

  Haka kuma an ba wa 'yan wasa jan kati, wato na kora daga fili har guda 1,477 a tarihin gasar ta Premier.

  Gasar Premier na cike da matsaloli da sallamar masu koci-koci na kungiyoyi a wannan lokacin, ba kamar yadda take ba a 1992.

  A kakar farko ta gasar kociya daya kawai aka kora Ian Porterfield na Chelsea bayan wasa 29 daga cikin 42, ranar 15 ga watan Fabrairu na 1993. Daga nan kuma abin sai karuwa yake a kai a kai ba kakkautawa.

  A tsakanin watan Agusta na 1994 da Agustan 1995, kungiyoyi 15 sun sauya kociyansu, inda guda takwas suka kori nasu daga aiki.

  Bayan kaka uku ana wasa 42 a tsakanin kungiyoyi 22, gasar ta Ingila wadda tuni ta samu makudan kudade daga nuna wasanninta ta talabijin, an rage ta zuwa tsarin wasa 38 tsakanin kungiyoyi 20.

  Yawan Cin Kwallo

  Babu kungiyar da ta fi Manchester United cin kwallo a gasar Premier, inda ta zura 1,856, ta zarta Arsenal mai bi mata a matsayi na biyu da kwallo 158.

  A kakar farko ta gasar ta 92-93 an zura jumullar kwallo 1,222 - Brian Deane na Sheffield United ne ya fara daga raga, lokacin da ya ci Manchester United da ka, bayan minti biyar da shiga fili a Bramall Lane.

  Alex Ferguson da Ronaldo
 5. 'Coutinho na neman tilasta wa Liverpool ta sayar da shi'

  Yahoo Sports ta ruwato cewar Philippe Coutinho na neman komawa Barcelona ta hanyar 'yin aiki kadan a atisaye.'

  Dan wasan Brazil din ya shaida wa Jurgen Klopp cewar yana son ya bar Anfield zuwa Barca kuma an ce ba ya ji dadin cewar Liverpool ba ta son ta saya da shi ba.

  Philippe Coutinho
 6. Ya kamata Sanchez ya tsaya a Arsenal -Keown

  Tsohon dan wasan baya na Arsenal, Martin Keown , ya yi imanin cewar ya kama Sanchez ya mutunta kwantiraginsa da Gunners.

  Sanchez, mai shekara 28,zai kammala kwantiraginsa a karshen kaka kuma ya wallafa wani sako a shafinsa na sada zumunta inda ya ce ba shi da lafiya.

  Duk da cewar dan wasan ya kama aiki a sansanin Arsenal da ke Colney a birnin Landan, bai buga wasan cin kofin Community Shield inda Arsenal ta tyi nasara kan Chelsea ranar Lahadi ba.

  Sanchez
 7. Riyad Mahrez: Roma ta rungumi kaddara

  Daraktan wasanni na Roma, Monchi, ya ce kungiyar kwallon kafar ta rungumi kaddara bayan ta kasa sayan dan wasan Leicester City, Riyad Mahrez.

  City ta ki tayi biyun da Roma ta yi mata kan dan wasan mai shekara 26, inda aka yi imanin cewar tayi na biyun da ta yi ya kai kimanin fam miliyan 32.

  City tana ganin tayin bai kai kudin da take nema ba, kuma Roma ba za ta sake taya dan wasan ba.

  Tuni dai Roma da fara neman wasu 'yan wasan.

  Riyad Mahrez
 8. Tottenham na da zabin sake sayan Gareth Bale

  Jaridar Mirror ta ruwaito cewar, Tottenham tana da zabin sake sayan tsohon dan wasanta na gefe, Gareth Bale daga Real Madrid.

  Amman yiwuwar komawar dan wasan arewacin Landan na da sarkakiya.

  A yarjejeniyar fam miliyan 85 da ta dauke Bale daga White Hart Lane zuwa Bernabeu a shekarar 2013, Daniel Levy ya samu zabi kan makomar dan wasan.

  Duk da cewar zabin ba na iya sake sayan dan wasan ba ne kai tsaye, Spurs za ta iya ba da daidai kudin tayin da wata kungiyar gasar Firimiya ta yi wa dan wasan, Real ta sallama shi.

  Wannan na nufin cewar idan Real Madrid ta yarda da tayin da Manchester United za ta yi kan dan wasan, Spurs za ta iya biyan kudin da Man Utd ta bayar cikin sa'o'i 72 domin sayan dan kwallon.

  Tottenham
 9. Arsenal na tuni game da wasanta na farko a Firimiya

  Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta fitar da wani sakon tuni ga magoya bayanta game da wasanta na farko a gasar Firimiyar bana.

  A wani sakon GIF din da ta wallafa a shafinta na Twitter, wadda kungiyar bata taba irinsa ba, ta nuna yadda take ganin magoya bayanta za su yi sauri domin su samu su kalli karawarta da Leicester City a ranar Juma'a.

  'Yan Arsenal
 10. 'Tottenham ba za ta sayar wa Man Utd Danny Rose ba'

  Tottenham ta shaida wa Manchester United cewar dan wasanta na baya, Danny Rose ba na sayarwa ba ne, in ji jaridar Metro.

  Rahotanni sun ce Manchester United da Inter Milan sun shirya domin zawarcin dan shekara 27 din, amman kociyan Spurs, Mauricio Pochettino, ya ce ba za a tilisata masa sayar da ko wane dan wasa ba.

  Danny Rose
 11. 'Ba za a sayar da Crystal Palace ga Tony Adams ba'

  ShugabanCrystal Palace, Steve Parish ya musanta cewar ana gab da sayar da kulob din ga wasu 'yan kwasuwa da tsohon mai tsaron bayan Arsenal, Tony Adams, ke jagoranta, in ji (Mirror).

  Tony Adams
 12. 'Liverpool ka iya musayar Gomes da Countinho'

  Dan wasan tsakiyar Portugal, Andre Gomes, ka iya koma wa Liverpool a wani bangare na yarjejeniyar cinikin Countinho.

  Wannan bayanin na fitowa ne a daidai lokacin da wakilan Barca suka isa Liverpool domin sayan Countinho kamar yadda jaridar The sun ta ruwaito daga Mundo Deportivo (Mundo Deportivo via Sun)

  Andre Gomes
 13. "Sauran 'yan sa'o'i Barca ta saye Countinho"

  Rahotanni daga Spaniya na cewa saura 'yan sa'o'i ne kawai Barcelona ta saye Philippe Coutinho daga Liverpool.

  Sport ta ce wakilan Barca sun niki gari zuwa Liverpool ranar Talata domin kammala wata yarjejeniya kuma suna son su bayyana dan shekara 25 din a matsayin dan wasansu a cikin wannan makon.

  Rahotannin sun kara da cewa masu Liverpool sun yarda cewar za su sayar da dan wasan duk da cewar Klopp ba ya son hakan.

  Coutinho
 14. 'Drinkwater na cikin 'yan wasa hudun da Chelsea ke so'

  Dan wasan Leicester City, Danny Drinkwater, na daya daga cikin manyan 'yan wasan da Chelsea ke hako, in ji Standard.

  Kociya Antonio Conte yana son ya kara sabbin 'yan wasa hudu kafin karshen wata ciki har da dan shekara 27 na Leicester City.

  Har wa yau kulob din zai ba da aron wani dan wasan da ake gani da daraja, Lewis Baker, wanda bai buga wasan cin kofin Community Shield da Chelsea ta fafata da Arsenal ba.

  Danny Drinkwater
 15. Bale ya mayar da hankalin kan wasan Super Cup

  A halin yanzu dai Gareth Bale ya mayar da hankali ne kan wasan zakaran zakarun Turai da za a buga tsakanin kungiyarsa ta Real Madrid da Manchester United a ranar Talata.

  Dan wasan ya bayyana hakan ne a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twittter da maudu'in #HalaMadrid.

  Gareth Bale
 16. Bayan Iheanacho, Leicester ta kara dan wasan gaba

  Bayan ta sayi dan wasan gaban Najeriya, Kelechi Iheanacho, Leicester City ta kara sayan wani dan wasan gaba daga kungiyar kwallon kafa ta Coventry.

  George Thomas mai shekara 20 ya koma Leicester City ne kan kwantiragin shekara uku, in ji Leicester City a shafinta na Twitter.

  George Thomas
 17. 'Barca na sha'awar Dembele'

  Barcelona na sha'awar sayan dan wasan Borussia Dortmund mai shekara 20, Ousmane Dembele, in ji Sport.

  Ousmane Dembele
 18. 'Dole Coutinho ya koma Barca'

  Dole dan wasan Brazil Coutinho ya koma Barca, in ji tsohon dan wasan Ingila Ian Wright a hirarsa da BBC.

  Coutinho
 19. 'Bale ba zai koma gasar Firimiya ba'

  Kociyan Real Madrid, Zinedine Zidane, ya musanta rade-radin da ake yi cewar Bale zai iya koma taka leda a gasar Firimiya, in ji Mirror.

  Zidane Bale
 20. 'Man Utd za ta taya Bale in... '

  Manchester United za ta taya dan wasan gaban Real Madrid, Gareth Bale, idan Zinedine Zidane bai saka shi cikin 'yan wasansa 11 na farko ba a wasan karshe na gasar Super Cup da za a buga ranar Talata, in ji jaridar Times.

  Gareth Bale