Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Chelsea na son karin 'yan wasa
  2. Ba tabbas kan makomar Coutinho
  3. Man Utd ba ta fidda rai sayan Perisic ba
  4. Wa zai lashe gasar Premier bana?
  5. Real Madrid ta doke Man United

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

Sai mu tara gobe

Jama'a a nan muka kawo karshen shirin na yau, da fatan za ku sake kasancewa tare da mu a gobe idan Allah ya kaimu da misalin karfe 10.30 na safe agogon Najeriya da Nijar.

Real Madrid na murna bayan doke United

Bari na barku da wannan hoton na 'yan wasan Real Madrid lokacin da suke murna bayan doke Manchester United a gasar cin kofin zakarun zakarun nahiyar Turai.

Real Madrid
Getty Images
Real Madrid
Getty Images
Real Madrid
get

Isaac Makwala ya yi tsere shi kadai

Isaac Makwala ya kai wasan kusa da na karshe bayan da aka amince ya shiga gasar tseren mita 200, a gasar tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya da ake yi a Landan.

Tun da farko an hana shi shiga wasan mita 400 bayan da ya yi amai kafin fara wasan.

Ya dai yi gudun ne shi kadai.

Isaac Makwala
Getty Images

Allyson Felix na fatan yin bajinta

Ba'amurkiya Allyson Felix na harin cin lambar bajintarta ta duniya ta goma a shirin da take yi na shiga tseren mita 400 na karshe a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da ake yi a Landan, a yau Laraba.

'Yar kasar Bahama Shaunae Miller-Uibo da 'yar Bahrain Salwa Eid Naser su ne babbar barazanarta a gasar.

Shi kuwa dan Birtaniya Mo Farah, wanda zai koma gasar gudu a titi, ya bar ta filin wasa a kaka ta gaba.

Ya dai fara gasarsa ta bankwana da lamabra zinare da ya ci a gudun mita 10,000, kuma zai fara shirin fafatawa a gasar mita 5,000.

Gwarzo dan Jamaica Usain Bolt, wanda ya ci lambar tagulla bayan da ya zo na uku a gasar tseren mita 100, na shirin kawo karshen wasansa da ya cimma gagarumar nasara a duniya.

Yana fatan cin lambar zinare a tseren karba-karba na mutum hudu na mita 100, wanda za a yi ranar Asabar.

Mo Farah
Getty Images

Ba za mu kashe sama da fam 200m ba - Bayern Munich

Neymar
Getty Images

Kociyan Bayern Munich, Karl-Heinz Rummenigge ya ce kulob din ba zai taba kashe sama da fam miliyan 200 kamar yadda Paris St Germain ta biya wajen sayen Neymar ba.

"A matsayinmu na kulob din Bayren Munich dole ne mu samu bambamcin tunani", in ji Rummenigge.

Kudin da aka sayi Neymar ya fi kudin filin Allianz Arena.

A lokacin da Neymar zai koma PSG na tambayi kaina game da wanne abu ne ya fi muhimmanci?, Neymar ko filin wasa na Allianz Arena?

Ya ce, "ya kamata na bayyana gaskiyar cewa, gara ka mallaki Allianz Arena tunda yake ya fi muhimmanci".

McIlroy ya ce ba ya bukatar wata bajinta

Rory McIlroy ya ce ba shi da sauran wata bajinta da yake bukatar ya nuna yayin da yake kokarin cin babban kofinsa na farko a shekara uku a gasar kwallon golf ta Amurka.

Gwanin kwallon lambun na hudu a duniya, yana daga cikin mutum hudu da ake ganin za su yi nasara a gasar, wadda ake yi a filin Quail Hollow, inda ya yi nasara sau biyu da kuma tarihin bajintar da aka taba yi a filin.

McIlroy ya ce : "ba zan matsa wa kaina ba ta cewa sai na yi wata bajinta. Na riga na nuna wa duniya kokarina a cikin shekara tara da ta wuce,'' In ji shi.

Dan Ireland ta Arewar ya kara da cewa, ''ban taba karaya ba. A ko da yaushe na yarda da kaina. Kuma har yanzu haka nake.''

Rory McIlroy
Getty Images

McGregor zai doke Mayweather - Froch

Floyd Mayweather da Conor McGregor
Getty Images
Mayweather na ganin zai samu dala miliyan 300 a damben na ranar 26 ga watan Agusta

Ritayar shekara biyu da Floyd Mayweather ya yi daga damben boksin, za ta ba wa abokin karawarsa Conor McGregor damar kafa wani tarihi a damben da za su yi mai takaddama in ji tsohon zakaran duniya Carl Froch.

McGregor wanda dan damben hannu da kafa ne zai kara da Ba'amurke Mayweather, mai shekara 40, a Las Vegas ranar 26 ga watan Agusta,a damben da kowannensu zai iya samun dala miliyan 100.

Froch wanda tsohon zakaraun duniya ne na boksin na ajin matsakaita nauyi sau hudu ya gaya wa BBC Sport cewa: "kowa yana ganin Mayweather ne zai yi nasara a damben, to amma za a sha mamaki.

Ya ce jama'a za su ga sabanin haka saboda shekarar McGregor 29, matashi ne da ke cike da buri da kuma kwarin guiwa.

Pape Souare ya koma atisaye wata 11 bayan hatsarin mota

Mai tsaron baya na Crystal Palace, kuma dan wasan Senegal, Pape Souare ya koma atisaye wata 11 bayan ya ji mummunan ciwo a hatsarin mota.

Souare, dan shekara 27, ya karye a cinya da haba a hatsarin kusa da Landan a watan Satumbar shekarar 2016.

Soure
Getty Images

Muna bukatar karin 'yan wasa - Chelsea

Duk da cewar Chelsea ta kashe sama da Fam miliyan 100 a kan 'yan wasa a lokacin bazararnan, Kociyan Chelsea, Antonio Conte ya kungiyar kwallon kafar tana bukatar karin 'yan wasa in har tana son ta kare kanbunta a gasar Firimiyar bana.

Conte
Getty Images

Kociyan Leicester City ya yarda da Mahrez

Riyad Mahrez zai ci gaba da taka wa Leicester City leda duk da cewar ya ce yana son barin kulob din, in ji kociya Craig Shakespeare.

Mahrez ya nemi ya bar Foxes, amman Shakespeare ya yarda da halayyar dan wasan tun da ya koma kulob din domin atisayen gabannin kaka.

"Zan iya magana ne kawai game da yadda na gan shi, kuma bai bani wata matsala ba," in ji Shakespeare, wanda kulob dinsa zai ziyarci Arsenal on ranar juma'a.

Mahrez
Getty Images

Leicester tana da hadari - Wenger

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce kungiyar kwallon kafa ta Leicester City, wadda za su kara da ita a wasansu na farko na Firimiyar bana, tana da hadari.

Kociyan ya ce:"Leicester tana da hanyar dakile mutane, suna da tsaron baya da kyau, kuma suna da hadari a wurin zari-zuga."

"Ina ganin mun yi shiri mai kyau ta hanyar wasan cin kofin Community Shield kuma dukkanin 'yan wasanmu sun samu buga wasa na mintuna masu amfani."

Arsenal
Getty Images

Ana kiki-kaka kan tafiyar Coutinho Barcelona

'Yan sa'o'i kadan suka rage kafin Barcelona ta dauke gwanin dan wasan Liverpool na Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 25, bayan da wakilan kungiyar ta Spaniya suka tashi takanas ta Kano suka tafi Liverpool a ranar Talata domin a yi ta ta kare a cinikin.

Jaridar Sport ta ruwaito wannan labari ne daga Metro, yayin da kuma ake samun wasu rahotannin da ke nuna cewa abu ne mai wuya tafiyar dan wasan ta tabbata saboda kociyansa yana sonsa.

Amma kuma jaridar the Sun ta kara da cewa dan wasan tsakiya na Portugal Andre Gomes kila ya je Liverpool din a karkashin yarjejeniyar cinikin Coutinho din.

Sai dai yayin da duk ake wannan magana kociyan Liverpool Jurgen Klop jaridar Daily Mirror ta ruwaito cewa kociyan dan jamus zai yi tsayuwar daka kan hana dan wasan tafiya Barcelona.

Philippe Coutinho da Jurgen Klopp
Getty Images

'PSG za ta biya Fam miliyan 80 kan Sanchez'

PSG ta shirya domin ta biya fam miliyan 80, na sayan dan kwallon Chile, Alexis Sanchez, mai shekara 28, a kokarinta na doke Man City a yunkurin sayan dan wasan na Arsenal, In ji jaridar independent.

Sanchez
Getty Images

'Yan Leicester City biyu ba za su buga wasan Arsenal ba

Labarin da ke fitowa daga Leicester a yanzu na cewa 'yan wasan kulob din biyu ba za su buga karawarsu da Arsenal a wasan na farko a gasar Firmiya ta kakar bana ba, a ranar Juma'a.

Kociya Craig Shakespeare ya ce Danny Drinkwater "zai sake sati daya " (kafin ya yi wasa) domin matsalar da ya samu a kugu.

Shi ma Vicente Iborra (targade a kugu) "ba zai buga wasan Arsenal ba.

"Kelechi Iheanacho ya yi cikakken atisaye bayan an buge shi," kamar yadda kungiyar ta bayyana a shafinta na Twitter:

View more on twitter

'Har yanzu Roma na neman Mahrez'

Riyadh Mahrez
Getty Images

Har yanzu Roma na son sayan dan wasan gefe na Leicester City, Riyad Mahrez, amman tana neman wasu 'yan wasan kuma..

Daraktan wasan kungiyar, Monchi, ya ce kungiyar kwallon kafa ta gasar Serie A din ta kara kudi a tayin da take yi wa dan wasan na Aljeriya zuwa fam miliyan 27.

Mahrez, wanda ya taimaka wa Leicester City cin gasar Firimiya a kakar 2015-16, ya nemi a kyale shi ya tafi.

"A halin yanzu, kungiyar ta kusa kai makura kuma na yi imanin cewar tayinmu na da muhimmanci sosai," in ji Monchi.

Karanta karin bayani a nan.

Real Madrid ta sake daukar kofi

Real Madrid ta sake rike kofin zakaran zakaru na Turai, Super Cup, bayan da ta doke Manchester United da ci 2-1 a wasan da ta mamaye su a babban birnin Macedonia, Skopje, cikin tsananin zafi.

Casemiro ne ya fara daga raga a minti na 24 bayan da Dani Carvajal ya sako kwallo tsakanin 'yan bayan United din.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne a minti na 52 sai Isco, ya tura wa Gareth Bale kwallo, shi ma ya mayar masa, a wani ba-ni-in-ba-ka suka yi, dan Spaniyar ya sheka ta biyu a raga.

Romelu Lukaku, wanda ya barar da wata dama, bayan golan Madrid ya yi aman harin da Pogba ya kai da ka can a minti na 54, bayan minti bakwai tsakani ya natsu ya sheka daya a raga bayan wani aman da Keylor Navas din ya sake yi.

Isco
Getty Images
Isco ne ya zura wa Madrid kwallonta ta biyu

Larson ya koma Hull City

Tsohon dan wasan tsakiya na Sunderland, Sebastian Larson, mai shekara 32, ya koma Hull City kan yarjejeniyar shekara daya, kamar yadda kungiyar ta wallafa a shafinta na Twitter:

View more on twitter

Man Utd ba ta fidda rai sayan Perisic ba

Ana tsammanin Manchester United za ta sake kokarin sayan dan wasan gefen Inter Milan, Ivan Perisic a wannan makon, in ji jaridar Manchester Evening News.

Tun farkon lokacin bazara ne dai ake rade-radin cewar Manchester Unied za ta sayi dan wasan Croatia din mai shekara 28.

Rahotannin sun kara da cewar an yi imanin cewar Inter tana hakikance cewar a hada da Anthony Martial cikin duk wata yarjejeniyar Perisic.

Sai dai United ta yi watsi da maganar a matsayin kora da hali, tana mai cewar kungiyar ba ta da niyyar sayar da dan asalin Faransan.

Perisic
Getty Images

Watford ta sayi matashin Brazil Richarlison

Richarlison
Reuters

Watford ta tabbatar da sayen matashin dan wasan Brazil na tawagar 'yan kasa da shekara 20 Richarlison, bayan da ya samu takardar izinin aiki a Ingila.

Dan wasan na gaba mai shekara 20 ya kulla kwantiragin shekara biyar ne daga Fluminense a kan kudi fam miliyan 11.

Fluminense da ke rukuni na daya a Brazil ta dauko Richarlison ne daga kungiyar America Mineiro da ke rukuni na biyu a kasar,a shekarar da ta wuce ta 2016.

Ya yi wa Fluminense wasa 67, inda ya ci mata kwallo 19, yayin da ya ci wa tawagar Brazil ta 'yan kasa da shekara 20, kwallo biyu a wasa takwas.

Watford za ta fara wasanta na Premier ne a gida da Liverpool ranar Asabar da karfe12:30 na rana agogon Najeriya da Nijar.

Me ya sa Mourinho ya kyautar da lambar yabonsa?

Bayan kungiyarsa ta sha kaye a hannun Real Madrid da 2-1, kociyan Manchester United, Jose Mourinho, ya mika lambar yabon da ya samu ga wani matashi cikin masu sha'awar kungiyarsa a Skopje da ke Macedonia.

Mourhinho ya ce: "ka gani, wasu lokutan ko na yi nasara ma, ba na adana lambobin yabo balle in na sha kaye.

"A gare ni lambar yabon za ta shiga wani wuri ne a gida na. Amman ga wannan matashin lambar yabon tana nan tamkar Wata ne. Ga wannan matashin lambar yabon wata aba ce wadda zai adana kuma zai yi ta tunawa da ita."

Mourinho
Getty Images

Ba za mu iya sayan Bale ba - Mourinho

Blae
Getty Images

Jose Mourinho ya ce fatan Manchester United na sayan Gareth Bale daga Real Madrid 'ya kare.'

A da kociyan United din ya ce zai yi iya kokarinsa wajen sayan Bale in har Madrid za ta sayar da shi, amman ya yarda cewar sayan Bale zai mar wuya bayan dan wasan ya fara wasa a fafatawar da United ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Madrid.

"Ina ganin a halin yanzu kowa ya san (dan wasan) zai tsaya," in ji Mourinho.

Da aka tambaye shi cewar ko an sanar da shi cewar zai iya barin kungiyarsa, Bale ya ce:"Ban sanda irin wannan maganar ba."

Ba tabbas kan ran da Neymar zai fara wasa a PSG

Wasan Neymar na farko a Paris St-Germain ka iya sake samun jinkiri saboda har yanzu hukumomin kwallon kafa a Faransa ba su samu takardun dake amincewa da tafiyarsa ba bayan ya kafa tarihi da komawarsa PSG daga Barcelona kan kudi Fam miliyan 200.

Hukumar kwallon kafa ta Faransa ta ba wa takwararta ta Spaniya wa'adin daren Alhamis domin ta ba ta takardun amincewa da komwarsa PSG da ke buga gasar Ligue 1. Idan har wa'adin ya wuce, Neymar ba zai buga wa PSG ba a Guingamp ranar Lahadi.

Neymar
Getty Images

Bar ka da hansti

Barkanku da zuwa wannan shafin inda za mu yi ta kawo muku labaran irin wainar da ake toyawa a kasuwar 'yan kwallo ta nahiyar Turai da kuma shirin da ake yi na fara gasar Firimiya.