Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. Sai gobe

  Jama'a, abin da ya samu kenan a shafinmu na labaran wasanni kai tsaye. Sai kuma gobe in mai duka ya kai mu. A kasance da shafinmu na labaran wasanni kai tsaye daga karfe 10.30 agogon Najeriya da Nijar.

 2. Crystal palace na son sayan dan mai tsaron gidan Roma

  Crystal Palace tana son sayan mai tsaron gidan Roma, Lukasz Skorupski, mai shekara 26,

  in ji jaridar Daily Mail.

  Lukasz Skorupski
 3. Matic ya ce zai dade a Man Utd

  Dan wasan tsakiyar Manchester United, Namanja Matic, ya ce zai dade a kungiyra kwallon kafan da ke saman teburin gasar Firimiya.

  Dan wasan da ya ci kyautar gwarzon dan wasa bayan United ta yi gagarumar nasara a wasanta na farko a gasar Firimiya, ya ce ya ji dadin yadda takwarorinsa na United suka karbe shi hannu bibbiyu.

  Namanja Matic
 4. Buffon da Messi da Ronaldo ka iya cin kyutar Uefa

  An fitar da sunayen Gianluigi Buffon da Lionel Messi da kuma Cristiano Ronaldo a matsayin wadanda za su iya cin kyutar gwarzon dan wasan ta hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa.

  Kociyoyi 80 da 'yan jarida 55 suka zabi 'yan wasan.

  Messi da Ronaldo sun ci kyautar sau biyu -inda Ronaldo ya ci a kakar bara.

  Za a mika kyautar ce a ranar 24 ga watan Agusta lokacin da da za a fitar da jadawalin gasar zakarun Turai.

  Uefa
 5. Newcastle za ta dakuki aron dan wasan Chelsea

  Ana tsammanin Newcastle United, da aka sani da Magpies, za ta dauki aron dan wasan gefen Chelsea mai shekara 21 Kenedy ,amman kociyan Blues, Conte ya jinkirta yarjejeniyar saboda tsoron raguwar 'yan wasansa, in ji. Goal.

  Kenedy
 6. Rafael Benitez na ya kara 'yan wasa

  Kociyan Newcastle United, Rafael Benitez, yana hakon karin 'yan wasa biyar kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa nan da mako biyu, in ji jaridar Telegraph.

  Rafael Benitez
 7. Stoke City na gab da shelar sayan Jese Rodriguez

  Kungiyar kwallon kafa ta Stoke City na gab da shelar sayan dan wasan gaba na PSG mai shekara 24 Jese Rodriguez, in ji jaridar Telegraph.

  Jesse Rodriguez
 8. Dan wasan Leicester na dab da komawa Derby County

  Dan wasan gefen Leicester City, Tom Lawrence, mai shekara 23, yana dab da komawa Derby County a wata yarjejeniyar da ta kai fam miliyan 7, in ji jaridar Daily Mail.

  Tom
 9. Carlos Tevez ya yi alkawarin komawa Shangai Shenhua

  An bai wa Carlos Tevez izinin zuwa Argentina, amman sai da ya rattaba hannu kan wata takarda cewar shi zai koma kungiyar kwallon kafa ta Shangai Shenhua zuwa ranar 30 ga watan Agusta.

  Akwai rahotannin da ke cewa, Tevez mai shekara 33, wanda ya koma Shanghai daga Boca Juniors a watan Disamba, yana son barin kulob din.

  Tsohon dan wasan gaba na Manchester City din ya nemi Shanghai ta kyale shi ya koma gida jinyan ciwon da ya ji a kafa.

  Tevez, wanda ya rattaba hannu akan yarjejeniyar shekara biyu, ya sha kwallaye biyu a wasanni 11.

  Tevez
 10. Chelsea na son dan wasan Ajax

  Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana sha'awar dan wasan baya Davinson Scanhez, amman Ajax ta hakikance cewar Sanchez ba na sayarwa ba ne, in ji jaridar Daily Star.

  Davinson Sanchez
 11. 'Ina son in koma Tottenham'

  Dan wasan bayan Colombia, Davinson Sanchez, mai shekara 21, ya shaida wa kungiyar kwallon kafarsa ta Ajax cewar shi yana son komawa Tottenham kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa, in ji jaridar Independent.

  Davinson Sanchez
 12. Diego Costa ya yi 'abin kunya'

  Rashin komawar dan wasan gaban Chelsea, Diego Costa, atisaye 'abin kunya ne', in ji tsohon dan wasan gaban Arsenal, Ian Wright.

  Dan wasan mai shekara 28, wanda a yanzu haka yana kasarsa Brazil, ya ce an yi masa kamar shi babban mai laifi ne a Chelsea kuma yana son ya koma tsohuwar kulob dinsa, Atletico Madrid.

  Diego Costa
 13. Ajen din Mahrez na son Roma ta kara mar kudi

  Ajen din wasan gefe na Leicester City, Riyad Mahrez, yana kokarin shawo kan kungiyar kwallon kafa ta Roma domin ta kara kudin da ta taya dan wasan mai shekara 26 zuwa fam miliyan 40 ciki har da kudaden da za a kara, in ji Sky Sports.

  Mahrez
 14. Komawar Ross Barkley Chelsea na cike da shakku

  Komawar dan wasan tsakiyar Everton Ross Barkley zuwa Chelsea ko Tottenham ya kasance cike da shakku bayan dan shekara 23 din ya ji ciwo a lokacin ataisaye, in ji jaridar Sun.

  Ross Barkley
 15. Marco Asensio na son tattaunanwa kan Arsenal

  Dan wasan tsakiya Marco Asensio, mai shekara 21, ya nemi a gudanar da tattaunawar gaggawa da Real Madrid bayan Arsenal ta nuna sha'awar son sayansa,in ji jaridar Sun.

  Marco Asensio
 16. Chelsea ta gindaya wa Diego Costa sharruda

  Chelsea ta gindaya wa dan wasan gaba Diego Costa wasu sharruda da dole sai ya cika kafin ta yi tunanin sayar da dan wasan mai shekara 28, in ji jaridar Guardian.

  Costa
 17. 'Zan yi kokarin shawo kan Coutinho'

  Keftin din Liverpool, Jordan Henderson, ya ce shi zai yi kokarinsa wajen shawo kan takwaransa, Philippe Coutinho, ya tsaya a Anfield, yayin da dan Brazil din mai shekara 25 ke neman komawa Barcelona, in ji jaridar Daily Mirror.

  Coutinho
 18. An samu baraka tsakanin Conte da masu Blues

  An samu rashin jituwa tsakanin kociyan Blues , Antonio Conte, da masu Stamford Bridge kan adadin yan wasan da ya kamata kungiyar ta saya yayin da kociyan dan asalin Italiya yake son sayan 'yan wasa masu kwarewa wadanda sake sayar da su ba zai yi kudi ba, in ji Times.

  Conte
 19. Barcelo ta cimma matsaya da Borussia Dortmund kan Ousmane Dembele

  Barcelona ta cimma yarjejeniyar biyan Borussia Dortmund fam miliyan90 domin sayan dan wasan gaba mai shekara 20 Ousmane Dembele kamar yadda Daily Express ta ruwaito daga Sport.

  Ousmane Dembele