Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Mece ce makomar Messi?
 2. Wane dan gasar Firimiya ne zai koma Isra'ila?
 3. Ina Chamberlain ya nufa?
 4. Mece ce makomar Ibrahimovic?

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. 'Manchester City ta fi karfi bana'

  Kociyan Everton, Ronald Koeman, ya ce shi yana cikin masu son salon wasan Pep Guardiola a Manchester City.

  Kungiyoyin biyu za su kara a daren Litinin, kuma Koeman ya ce: "Yadda shi (Guardiola) yake son wasa wani salo ne da ya fi wahala. Abun kayatarwa ne mutum ya kalli yadda kulob dinshi ke taka leda."

  Koeman ya kara da cewar kulob din yana da karfi fiye da yadda yake a bara.

  Everton vs City
 2. Dan wasan tsakiyar Hull City ya kusa komawa Swansea City

  Dan wasan tsakiyar Hull City, Sam Clucas, mai shekara 26, yana gab da komawa Swansea City, a lokacin da kociyan Tigers, Leonid Slutsky, yake cewa dan wasan na "shirin komawa wani kulob na daban," in ji Hull Daily Mail.

  Sam Clucas
 3. 'Barca za ta nemi sayan di Maria'

  Barcelona za ta nemi sayan dan wasan Paris St-Germain mai shekara 29 da ya taba taka wa Manchester United leda, Angel di Maria, in suka kasa sayan Philippe Coutinho, mai shekara 25, daga Liverpool, kamar yaddaDaily Mirror daga Mundo Deportivo.

  di Maria
 4. Masu tsaron bayan Arsenal biyu za su koma Birmingham

  Masu tsaron bayan Arsenal, Carl Jenkinson, mai shekara 25, da Cohen Bramall, mai shekara 22, sun shirya domin su koma Birmingham City akan aro, in ji Birmingham Mail.

  .
 5. Valencia na sha'awar dan wasan Man Utd

  Valencia na sha'awar aron dan wasan tsakiyar Manchester United Andreas Pereira, mai shekara 21, in ji Daily Mail.

  Andreas Pereira
 6. 'Dole Chelsea ta kara matsa kaimi'

  Mai tsaron gidan Chelsea, Thibaut Courtois, ya ce kulob din na bukatar kara matsa kaimi fiye da yadda ya yi a bara.

  Dan wasan mai shekara 25 ya ce tayiwu kayen da Chelsea ta sha a wasanta na farko a gasar Firimiya ya kasance zaburarwar da take bukata.

  Bayan shan kayen ne kungiyar doke Tottenham 2-1.

  Thibaut Courtois
 7. Mustafi ka iya barin Arsenal

  Dan wasan bayan Arsenal, Shkodran Mustafi, mai shekara 25, ka iya barin kulob din, yayin da Inter Milan ke sha'awar sayan dan wasan Jamus din wanda ake ganin kudinshi ya kai fam miliyan 35, in ji Daily Star

  Mustafi
 8. Burnley ta sayi dan wasan Chris Wood

  Burnley ta sayi dan wasan gaban Leeds United Chris Wood kan kudin da ake ganin ya kai kimanin fam miliyan 15.

  Chris
 9. Dan wasan Man City ya koma Antalyaspor

  Dan wasan tsakiyar Man City, Samir Nasri, ya koma kungiyar Antalyaspor ta Turkiyya kan yarjejeniyar shekara biyu bayan ya buga wa Man Citty wasannin Premier 129 cikin shekara 6.

  Nasri
 10. Darakatocin Barca ba su dace ba -Neymar

  Dan wasan da ya kafa tarihi da komawa PSG daga Barcelona kan kudi fam miliyan 200 ya ce daraktocin kulob din ba su dace da aikinsu ba.

  Da yake magana bayan wasan farko da ya buga wa PSG a gida inda ya ci kwallaye biyu, Neymar ya ce shi ya bar tsohon kulob din nasa cikin lumana, amman bai bar daraktocin kungiyar cikin ruwan sanyi ba.

  "A nawa tunanin, bai kamata su kasance daraktocin da za su jagoranci Barca ba. Barca ta cancanci abun da ya fi haka,"

  in ji Neymar.

  Neymar
 11. 'Mamadou Sakho ya yi tsada'

  Kociyan Crystal Palace, Frank de Boer, ya ce dan wasan Liverpool, Mamadou Sakho, mai shekara 27, ya yi masa tsada, in ji Guardian.

  Sakho
 12. Kungiyar Turkiyya ta taya dan Man City

  Kungiyar kwallon kafa ta Turkiyya, Antalyaspor ta taya dan wasan tsakiyar Manchester City, Samir Nasri, mai shekara 30, kan yarjejeniyar shekara biyu da ta kai fam 70,000 a ko wanne mako, in ji Times.

  Samir Nasri
 13. 'Dole Arsenal ta sayar kafin ta saya'

  Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce dole ya sayar kafin ya saya yayin da yake amsa cewar kulob dinsa na da 'yan wasa masu yawa, in ji Independent.

  Wenger
 14. Barca na son sayan Seri daga Nice

  Kungiyar Barca da ke taka leda a gasar La Liga ta shirya domin biyan kudin fansan dan wasan tsakiyar Nice, Jean Michael Seri, mai shekara 26 da fatan cewar za su saka shi a wasa tare da dan wasan Liverpool, Philippe Coutinho a kaka mai zuwa kamar yadda Daily Mail ta ruwaito daga Mundo Deportivo.

  Jean Michael Seri
 15. Babu tabbas kan zama na a Barca - Iniesta

  Kyaftin din Barcelona, Andres Iniesta, mai shekara 33, wanda yarjejeniyarsa za ta kare a lokacin bazara mai zuwa, ya nuna cewar babu tabbacin ci gaba da zamansa a kulob din, kamar yadda Daily Mail ya ruwaito daga El Pais.

  Iniesta
 16. Arsenal ta yi wa Chamberlain tayi

  Arsenal ta yi wa dan wasan gefe Alex Oxlade-Chamberlain, mai shekara 24, tayin yarjejeniyar shekara hudu da ya kai fam 125,000 a ko wanne mako domin dakile sha'awarsa da Chelsea ke yi, in ji Daily Star.

  Chamberlain
 17. Man City za ta kafa tarihi wajen sayan Messi

  Manchester City ta shirya domin kafa tarihi na biyan kudi mafi yawa wajen sayen dan wasa domin cimma kudin sayen dan wasan gaba Lionel Messi fam miliyan 275 daga Barcelona, in ji Yahoo Sport.

  Jami'an City sun gana da wakilan Messi domin tattauna yiwuwar komawar dan wasan mai shekara 30 zuwa Etihad, in ji Daily Record.

  Messi
 18. Ana tsammanin Ibrahimovic tsawaita zamansa a Man Utd

  Ana tsammanin dan wasan gaban Manchester United mai shekara 35, Zlatan Ibrahimovic, zai rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejejniya ta tsawaita zamansa a Old Trafford a wannan makon, in ji ESPN .

  Ibrahimovic