Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Babu tabbas kan makomar Conte a Chelsea
 2. Chamberlain zai bar Arsenal?
 3. Chelsea na neman Drinkwater da Canreva
 4. Rooney ya dena taka wa Ingila leda

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. Chelsea na tunanin sayan Vardy

  Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana tunanin sayan dan Leicester City, mai shekara 30, kuma dan wasan gaba na Ingila, Jamie Vardy, in ji jaridar Mirror.

  Vardy
 2. Aston Villa na neman aron dan West Ham

  Aston Villa na fatan cewar za ta iya samun aron dan asalin Scotland da ke taka leda West Ham, Robert Snodgrass, zuwa karshen kakar bana.

  Snodgrass ya buga wa kociyan Villa, Steve Bruce a Hull, inda ya taimaka mishi wajen shigar da kulob din gasar Firimiya a shekarar 2015. West Ham ta sayi Snodgrass kan kudi kimanin fam miliyan 10 a watan Janairun da ya wuce, amman har yanzu dan shekara 29 din bai saje ba a kulob din.

  Robert Snodgrass
 3. Dan wasan gaban Chlesea ba zai koma Lille ba

  Dan wasan gaban Chelsea, Michy Batshuayi, ba shi da sha'awar barin Stamford Bridge domin komawa Lille, wadda aka alakanta da tayin dan wasan dan asalin Belgium mai shekara 23 kan kudi fam miliyan 36, in ji jaridar London Evening Standard.

  Michy Batshuayi
 4. Liverpool da Arsenal na neman dan wasan Madrid

  Liverpool da Arsenal na sha'awar dan wasan gefen Real Madrid,Lucas Vazquez, mai shekara 26, wanda ya fara wasannin gasar La Liga 12 kawai karkashin Zinedine Zidane a kakar bara,kamar yadda Daily Express ta ruwaito daga Don Balon.

  Lucas Vazquez
 5. PSG za ta rubanya kudin da Madrid ke son bai wa Mbappe

  Paris St-Germain za ta biya dan wasan gaban Monaco, Kylian Mbappe kudin albashi na fam miliyan 13.8- abun da ya yi sama da albashin da Real Madrid ta yi wa dan shekara 18 din sau biyu, in ji Marca.

  Mbappe
 6. Rooney ya daina taka leda wa Ingila

  Dan wasan kwallon kafa da ya fi ci wa Ingila kwallo, Wayne Rooney, ya dena taka wa kasar leda daga yanzu.

  Dan wasan gaban na Everton, mai shekara 31, bayyana hakan ne a wata sanarwar da ya fitar.

  Rooney ya ci wa Ingila kwallaye 53 cikin wasanni 119 da ya buga mata.

  Wayne Rooney
 7. Neymar zai kalubalanci karar da Barca ta kai shi

  Dan wasan gaba na Paris St-Germain, Neymar, zai kalubalanci matakin shari'ar da tsohuwar kungiyarsa, Barcelona, ta dauka a kansa.

  Barcelona tana son Neymar ya mayar da kyautan fan miliyan 7.8 da ya karba domin ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara biyar- kafin ya bar kulob din.

  Dan wasan Brazil din ya kafa tarihi a watan Agusta bayan ya koma PSG kan kudi fan miliyan 200 bayan kungiyar ta saye kwantiraginsa.

  Wata sanarwa daga dan wasan mai shekara 25 da lauyoyinsa ta ce dan wasan zai kare kansa a hukumance sannu a hankali.

  Kuma da alamar Neymar yana nuna cewar shi yake bin Barcelona kudi bayan ya bar Nou Camp exit, maimakon ace kungiyar ce take binshi kudi.

  Neymar
 8. Man City na shirin yi wa Jonny Evans tayi na biyu

  Manchester City tana shirin yi wa dan wasan baya na tsakiya a West Brom, Jonny Evans, mai shekara 29, bayan an yi watsi da tayin fam miliyan 18 da aka yi wa dan wasan a makon jiya, in ji ESPN.

  Jonny Evans
 9. Rose zai koma Man Utd ne ko Chelsea?

  Dan wasan Ingila, Danny Rose, mai shekara 27, zai tattauna da Tottenham a wannan makon, yayin da Chelsea da Manchester United ke nuna sha'awar sayan dan wasan,in ji Independent.

  Danny Rose
 10. Perez zai bar Arsenal?

  London Evening Standard ta ruwaito cewar ana tsammanin Arsenal za ta yarda da wata yarjejeniya kan sayar da dan wasan gaban Spaniya, Lucas Perez, mai shekara 28, ga Deportivo kan kudi fan miliyan 14.

  Lucas Perez
 11. Barca ta yi wa Dembele tayi na biyu

  Barcelona ta yi wa dan wasan Faransa, Ousmane Dembele, mai shekara 20, tayi na biyu kan kudi fan miliyan 119, amman Borussia Dortmund tana neman akalla fan miliyan 138, kamar yadda Sky Deutschland ta ruwaito daga AS.

  Dembele
 12. Chamberlain zai bar Arsenal?

  Da alamar dan wasan tsakiyar Ingila, Alex Oxlade-Chamberlain, ba zai sabunta kwantiraginsa a Arsenal ba, yayin da Chelsea da Liverpool ke nuna sha'awar dan shekara 24 din, in ji Telegraph.

  Chamberlain
 13. Chelsea na neman Drinkwater da Canreva

  Chelsea ta kusa cimma yarjejeniyar fam miliyan 30 kan sayan dan wasan Ingila da Leicester City, Danny Drinkwater, mai shekara 27. Zakarun gasar Firimiyar suna kuma hakon dan wasan Inter Milan, Antonio Candreva, mai shekara 30, wanda aka sanar da shi cewar zai iya barin kungiyar kan kudi fan miliyan 25, in ji Mirror.

  Danny Drinkwater
 14. Barca za ta yi wa Coutinho tayin karshe

  Barcelona za ta yi wa dan wasan Liverpool, Philippe Coutinho, tayin karshe kan kudi fam miliyan136 yayin da Barca ke neman Liverpool ta sauya shawara kan kin sayar da dan wasan, in ji Sun.

  Coutinho
 15. Chelsea ta bayyana mai iya maye gurbin Konte

  Chelsea ta ayyana tsohon kociyan Borussia Dortmund,Thomas Tuchel, a matsayin mutumin da take son ya maye gurbin Antonio Conte a daidai lokacin da rahotanni ke cewar ana takun saka tsakanin kociyan da shugabannin Chelsea, in ji Bild.

  Conte
  Image caption: Rahotanni na cewa ana takun saka tsakanin Conte da jagororin Chelsea
 16. Liverpool na son dan wasan Jamus

  Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp, yana shaukin sayan dan wasan Schalke da na Jamus Benedikt Howedes, mai shekara 29, kan kudi fam miliyan 18, in ji DW Sports, via Express.

  Benedikt Howedes
 17. Andre Gomes na spon barin Barca?

  Dan wasan tsakiyar Barcelona Andre Gomes, mai shekara 24, ya shaida wa Barcelona cewar yana soin barain Nou Camp,yayin da ake rade-radin cewar Manchester United na son ta mayar da shi dan wasa na hudu da za ta saya a lokacion bazarannan, in ji Manchester Evening News.

  Andre Gomes
 18. Huddersfield dan wasa daga Bundesliga

  Kungiyar da ge tarayya da Manchester United a saman teburin Firimiya, Huddersfield, ta lashe wasanninta na gasar firimiya kawo yanzu, kuma yanzu ta sayo dan wasan tsakiya daga gasar Bundesliga na Jamus. Ta sayo Abdelhamid Sabiri ne daga kungiyar Nurnburg kan kudin da ba a bayyana ba.

  View more on twitter
 19. Spurs na son dan wasan PSG Aurier

  Spurs na matsowa kusa da cimma yarjejeniyar sayan dan kasar Ivory Coast mai shekara 24 Serge Aurier daga PSG, in ji L'Equipe.

  .