
Yadda kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon Turai ke ci
Labaran wasanni kan wainar da ake toyawa a kasuwar musayar 'yan kwallo ta nahiyar Turai, da ma sauran abubuwan da ke gudana a duniyar wasanni ranar Talata, 29 ga watan Agustan 2017.
Labaran wasanni kan wainar da ake toyawa a kasuwar musayar 'yan kwallo ta nahiyar Turai, da ma sauran abubuwan da ke gudana a duniyar wasanni ranar Talata, 29 ga watan Agustan 2017.
Rahoto kai-tsaye
Daga Abdulwasiu Hassan
time_stated_uk
Krychowiak a Leicester City?
Leicester City na tunanin sayan dan wasan tsakiyar Paris Saint-Germain, Grzegorz Krychowiak yayin da makomar Danny Drinkwater a kungiyar ke cike da tababa.
Rahonatnni sun ce zakarun gasar Firimiya, Chelsea, sun taya Drinkwater sau biyu, amman an yi watsi da tayin, inda tayi na biyun ya kai kimanin fam miliyan 32.
Kazalika, Leicester ta yi tambaya game da dan wasan Poland Krychowiak, mai shekara 28, in ji Leicester Mercury.
West Brom na son Pantilimon
An alakanta West Brom da son mai tsaron gidan Watford, Costel Pantilimon.
Dan asalin Romaniyar mai shekara 30zai maye gurbin lamba dayan West Brom, Ben Foster, in ji Birmingham Mail.
Newcastle na fatan kara 'yan wasa
Newcastle United tana fatan kara 'yan wasa biyu kafin a rufe kasuwar 'yan wasa, amman sai ta sayar da wasu 'yan wasa tukunna.
Jaridar Telegraph ta ba da rahton cewar duk da cewar kungiyar ta kashe fam miliyan 40 kan sabbin 'yan wasa a lokacin bazararnan, akwai wasu kudade da suka saura.
Man Utd za ta sabunta kwantiragin Shaw
Manchester United za ta kara wa dan wasan baya Luke Shaw kwantiragi domin hana dan wasan mai shekara 22 barin kulob din, in ji jaridar Sun.
Liverpool za ta kara wa Lemar kudi
Liverpool za ta kara wa dan wasan Monaco, Thomas Lemar, kudi zuwa fam miliyan 75, yayin da take neman sayan dan wasan da ya fi tsada a tarihinta.
An yi watsi da tayin kimanin fam miliyan 65 da Reds ta yi domin Monaco ba ta son sayar da dan wasan, in ji Liverpool Echo.
Mbappe ya gama gwaje-gwaje a PSG
Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Monaco, Kylian Mbappe, ya kammala gwaje-gwajen lafiya gabannin komawarsa kungiyar PSG da ke fafatawa a gasar Ligue 1.
An yi wa dan wasan mai shekara 18 gwaje-gwaje ne a Clairefontaine, inda yake atisaye da 'yan kwallon kasar Faransa, in ji TF1.
PSG za ta sayi Mbappe kan kudi fam miliyan 166 a alokacin bazara mai zuwa.
Lazio ta sallamar wa Monaco Keita Balde
Lazio ta sallama tayin da Monaco ta yi kan Keita Balde na kudi fam miliyan 28.
Ana tsammanin dan shekara 22 din a Monte Carlo a yau domin gwaje-gwaje, in ji Sky Italia.
Mene ne wanna ke nufi ga makomar Thomas Lemar da ake alakanta da komawa Liverpool?
West Brom ta kusa sayan Gibbs
Kungiyar kwallon kafa ta West Brom ta kusa sayan dan wasan baya Kieran Gibbs daga Arsenal.
Kungiyoyin sun cimma matsaya akan farashin cinikin da ya kai kimanin fam miliyan 5 domin sayan dan wasan mai shekara 27.
Dan wasan da ya tattauna da Watford da Galatasaray na bukatar yin gwaje-gwaje sannan ya rattaba hannu kan kwantiraginsa.
Watford ta fasa sayan dan Arsenal
Watford ta fasa sayan dan wasan bayan Arsenal, Kieran Gibbs, bayan ta kasa cima yarjejeniya da dan wasan.
Gibbs, mai shekara 27,yana shekara ta karshe a kwantiraginsa a Emirates, kuma an riga an sanar da shi cewar zai iya barin kulob din, in ji Sky Sports.
Tottenham ka iya rasa dan wasan PSG
Tottenham za ta iya rasa dan wasan bayan Paris St-Germain, Serge Aurier, saboda dan wasan mai shekara 24 ya fi son ya koma Manchester United,kamar yadda Sun ta ruiwato daga SFR Sport.
An alakanta Chelsea da coinikin Marrez
An alakanta Chelsea da cinikin dan wasan gefen Leicester, Riyad Mahrez.
Amman nawa zakarun gasar Firimiyar ke son biya kan dan kasar Aljeriyar?
Za ku iya tafka muhawara a shafin Twitter da maudu'in #bbcsportsday.
Sam Allardyce zai koma Palace?
Ana tunanin mayar da Sam Allardyce kociyan Crystal Palace, idan har Eagles ta kori kociya Frank de Boer, in ji jaridar Mirror.
Chelsea ta fara tattaunawar sayar da Costa
Chelsea ta fara tattaunwar sayar da dan wasan gaba Diego Costa ga Atletico Madrid kan kudi fam miliyan 41, in ji jaridar Evening Standard.
A karshen kakar bara dan wasan mai shekara 28 ya samu sakon tes daga kociya Antonio Conte cewar ba a bukatarshi a kungiyar.
Ya kasa komawa kulob din a wannan kakar.
Everton na son Vlasic
Everton na fatan cimma yarjejeniyar da ta kai fam miliyan 10 domin sayan dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Hajduk Split da bai kai shekara 20 ba, Nikola Vlasic.
Dan wasan mai shekara 19 dan asalin kasar Croatia ne kuma zai iya wasa a tsakiya da gaba.
Dan wasan ya buge kociyan Everton, Ronald Koeman da kuma darakatan tamaular Everton, Steve Walsh a fafatawar da suka yi wasan neman shiga gasar Europa.
Koeman na son sayan dan wasan kafin a rufe kasuwar 'yan wasa ranar Alhamis.
Chmaberlain na gab da komawa Chelsea
Dan wasan tsakiyar Arsenal, Alex Oxlade-Chamberlain, yana gab da komawa zakarun gasar Firimiya Chelsea kan kudi fam miliyan 40.
Dan wasan na Ingila, mai shekara 24, zai karasa kwantiraginsa a lokacin bazara mai zuwa, kuma ya ki ya sake rattaba hannu kan wata saubuwar yarjejejniya a filin wasan Emirates .
Har yanzu dai Oxlade-Chamberlain bai yanke shawara ba kan ko zai koma Chelsea ko kuma Liverpool ne da taka leda, kuma kawo yanzu tayi mai karfin da aka yi wa dan wasan ya zo ne daga Chelsea.
Palace na neman Sakho
Crystal Palace ta ci gaba da shaukin sayan dan wasan bayan Liverpool, Mamadou Sakho, kafin a rufe kasuwar 'yan wasa ranar Alhamis.
Sakho ya yi nasara a wasannin aron da ya buga wa kungiyar kwallon kafar da ke fafatawa a gasar Firimiya a kakar bara.
Swansea ta taya Renato Sanches
Swansea ta taya dan wasan tsakiyar Bayern Munich, Renato Sanches.
An sanar da dan wasan Portugal din mai shekara 20 cewar zai iya barin kungiyar zakarun Jamus din kan bashi, in ji Wales Online.
An alakanta Chelsea da AC Milan da Monaco da kuma Liverpool da taya dan wasan da ya ci kofin Euro na shekarar 2016 .
Man City ta bai wa Sterling mamaki
Bayan rahotanni sun fito cewar Manchester City za ta ba da kudi da Raheem Sterling domin sayo Sanchez daga Arsenal, Raheem Sterling din ya rude.
Jaridar Guardian ta ce dan wasan na Ingila ya yi mamakin matakin da City ta ke son daukawa bayan ya ci kwallo biyu a wasannin gasar Firimiya uku da ya buga mata a kakar bana.
Amman dan wasan gaban zai iya yarda da komawa Landan.
Yarjejeniyar za ta kai labarai kuwa?
Barca na son kara 'yan wasa
Darakatan Barcelona, Robert Fernandez, ya ce kungiyar tana son ta kara sayan dan wasa daya ko biyu kafin a rufe kasuwar 'yan wasa bayan ta kammala sayan Ousmane Dembele daga Borussia Dortmund kan kudi fam miliyan 135.5 in ji Mundo Deportivo.
Liverpool za ta sayi Virgil van Dijk
The sun na ba da rahoton cewar Liverpool za ta sayi dan wasan bayan Southampton, Virgil van Dijk, bayan ta kammala sayan Naby Keita.