Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Za a rufe kasuwar da karfe 11 na dare a Ingila da Italiya da Faransa
  2. Za a ci gaba da hada-hada a Spaniya har sai ran Juma'a da daddare
  3. Liverpool sign Oxlade-Chamberlain daga Arsenal kan fam 35m
  4. Tottenham ta sayi Aurier kuma tana neman Llorente
  5. Mahrez na dab da barin Leicester

Rahoto kai-tsaye

Daga Naziru Mikailu

time_stated_uk

Mu kwana lafiya

To jama'a a nan muka kawo karshen shirin, sai a kasance da shafin bbchausa.com da kuma rediyo domin sanin yadda za ta kaya daga nan zuwa lokacin da za a rufe kasuwar musayar 'yan kwallo da ma sauran labaran wasanni.

Sanchez zai ci gaba da zama a Arsenal

Rahotannin da ke fitowa daga London na nuna cewa Alexis Sanchez zai ci gaba da zama a Arsenal.

Kulob din ya sanya sharadin cewa ba zai sayar da dan kwallon ga Man City ba har sai ya samu wanda zai maye gurbinsa.

Kuma wanda Arsenal ta so ta saya wato dan wasan Monaco Thomas Lemar ya nuna cewa ba zai koma kulob din na London ba.

Wannan na nufin idan dai ba wani gagarumin sauyi aka samu ba, to babu shakka Sanchez zai ci gaba da zama a Arsenal.

Alexis Sanchez
PA

Denayer ya koma Galatasaray

Jason Denayer ya koma Galatasaray daga Manchester City a matsayin aro na shekara daya.

A baya ya taba taka-leda a Celtic, Galatasaray da kuma Sunderland amma bai taba buga wa babbar tawagar City ba.

View more on twitter

Tab din jam! PSG ta dauki Mbappe

PSG ta dauki matashin dan kwallon Monaco Kylian Mbappe a matsayin aro na shekara daya tare da zabin sayensa din-din-din a kaka mai zuwa.

View more on twitter

Torino ta dauki Niang

Za ku iya tuna lokacin da Watford ta dauko Mbaye Niang a matsayin aro bara? Dan wasan na gaba ya sake sauya kulob, inda ya koma Torino na Italiya.

View more on twitter

Fatan alheri...

Abokin wasan Renato Sanches a Bayern Munich Franck Ribery ya yi wa matashin dan kwallon fatan alheri kan komawar da ya yi Swansea a matsayin aro.

Good luck in the Premier League @renatosanches35 ✊🏼💪🏼 #Swansea

Saura sa'o'i shida a rufe kasuwa

Yayin da ya rage saura sa'o'i biyar a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafar Turai, ga wasu daga cikin manyan cinikin da aka kammala a gasar Premier kawo yanzu:

Alex Oxlade-Chamberlain wanda ya koma Liverpool daga Arsenal a kan fam miliyan 35.

Serge Aurier ya koma Tottenham daga PSG a kan fam miliyan 23.

Nahki Wells wanda ya koma Burnley daga Huddersfield a kan fam miliyam biyar.

Renato Sanches wanda ya koma Swansea daga Bayern Munich a matsayin aro.

Orestis Karnezis ya koma Watford ne daga Udinese a matsayin aro.

Chamberlain
Getty Images

Sanches ya koma Swansea

Swansea ta dauki mutumin da ta ke nema.

Renato Sanches ya koma kulob din a matsayin aro na kaka daya daga Bayern Munich.

View more on twitter

Origi ya koma Wolfsburg

Divock Origi na Liverpool ya koma kungiyar Wolfsburg a matsayin aro tsawon kaka daya.

Dan kwallon ya ci kwallaye 21 a wasa 77 da ya buga wa Liverpool tun bayan da ya koma kulob din shekara biyu da suka wuce daga kungiyar Lille ta kasar Faransa.

Divock Origi
Getty Images

Nani ya koma Lazio

Tsohon dan wasan Manchester United Nani ya koma kungiyar Lazio a matsayin aro.

Dan wasan ya koma Valencia ne a shekarar 2016 daga Fenerbahce.

NANI
Getty Images

Karnezis ya koma Watford

Watford ta dauki golan Greece Orestis Karnezis a matsayin aro na shekara daya daga Udinese na Italiya.

Dan kwallon mai shekara 32 ya buga wa Udinese wasa fiye da 100 tun lokacin da ya koma kungiyar daga Panathinaikos a 2013.

Orestis Karnezis
Getty Images

Declan John ya koma Rangers

Rangers ta dauki dan kwallon baya na Cardiff City Declan John a matsayin aro na shekara daya.

John, mai shekara 22, ya taso ne a tawagar matasa ta Cardiff sannan kuma ya buga wa Wales wasa sau biyu.

Declan John
PA

Vlasic zai koma Everton

Everton na fatan kammala cinikin matashin dan kwallon Hajduk Split Nikola Vlasic a kan fan miliyan 10 kafin a rufe kasuwar hada-hadar 'yan wasa cikin daren yau.

Nikola Vlasic
Getty Images

Serge Aurier ya koma Tottenham

Dan wasan baya na Ivory Coast Serge Aurier ya bar PSG inda ya koma Spurs har zuwa shekarar 2022.

Serge Aurier
Getty Images

Stryjek ya koma Accrington Stanley

Accrington Stanley ta dauki golan Poland Max Stryjek a matsayin aro har zuwa karshen kakar bana.

Max Stryjek
Getty Images

Chamberlain kwararren dan kwallo ne – Klopp

Kociyan Liverpool Jorgen Klopp ya ce ya yi matukar farin cikin daukar dan wasan Arsenal Alex Oxlade-Chamberlain.

Ya ce "mutane na magana a kan lambar da zai buga, amma ni na fi so a yi magana a kan dan wasan da kuma rawar da zai iya takawa."

Ya kara da cewa Alex yana da kwarewa duk da cewa shi matashi ne, domin ya dade yana buga Firimiya, gasar zakarun Turai, sannan kuma yana buga wa kasarsa wasa.

Medical ✅
Signed ✅

Go behind the scenes as @Alex_OxChambo completed his move to the Reds:
lfc.tv/AtMz

Medical ✅ Signed ✅ Go behind the scenes as @Alex_OxChambo completed his move to the Reds: lfc.tv/AtMz

City ta amince Bony ya koma Swansea

Manchester City ta amince da tayin fam miliyan 12 da Swansea City ta yi wa Wilfried Bony.

Wilfried Bony
Getty Images

Liverpool ta dauki Oxlade-Chamberlain

Liverpool ta sayi dan wasan Arsenal, Alex Oxlade-Chamberlain kan fam miliyan 40.

Dan wasan tawagar Ingila mai shekara 24, ya ki ya koma Chelsea da taka-leda a ranar Talata duk da cewar Arsenal ta amince da tayin da aka yi masa.

Oxlade-Chamberlain ya buga wa Arsenal wasa ukun da ta yi a gasar Premier bana, duk da sanar wa da Arsene Wenger cewar ba zai tsawaita zamansa a Gunners ba.

Dan wasan ya buga wa Arsenal tamaula sau 198 tun komawarsa Gunners daga Southampton a watan Agustan 2011.

Kudin da Liverpool ta sayi Chamberlain shi ne na biyu mafi tsada a kungiyar bayan dan kwallon RB Leipzig, Naby Keita da ta dauka kan fam miliyan 48, wanda sai a badi zai koma Anfield.

Alex Oxlade-Chamberlain
Getty Images

Barkanmu da rana

Ranar Karshe ta cinkin 'yan kwallo

Jama'a barkanmu da sake saduwa a filin namu na yau, in da za mu kawo muku bayanai kan wainar da ake tonawa a ranar karshe ta musayar 'yan kwallon Turai.