
Barca 3-0 Juventus, Chelsea ta ci 6-0
Labaran wasanni kai tsaye kan gasar cin kofin Zakarun Turai fafatawar cikin rukuni a ranar 12 ga watan Satumba 2017.
Labaran wasanni kai tsaye kan gasar cin kofin Zakarun Turai fafatawar cikin rukuni a ranar 12 ga watan Satumba 2017.
Rahoto kai-tsaye
Daga Mohammed Abdu
time_stated_uk
Post update
Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku tara a shirin mu na ranar Laraba.
Wasannin da za a yi a ranar Laraba
Post update
Manchester United 3-0 Basel
Marcus Rashford
Chelsea 6-0 Qarabag
Michy Batshuayi
Celtic 0-3 Paris St-Germain
Chelsea 5-0 Qarabag
Michy Batshuayi
Chelsea 4-0 Qarabag
Tiemoue Bakayoko
Barcelona 3-0 Juventus
Lionel Messi
Manchester United 2-0 Basel
Romelu Lukaku
Klopp ya ce sai a ranar Laraba ko Coutinho zai yi wasa
Barcelona 2-0 Juventus
Barcelona 1-0 Juventus
Lionel Messi
Celtic 0-3 PSG
Edinson Cavani a bugun fenariti
Rafa Benitez ya samu sauki
Kocin Newcastle United, Rafa Benitez ya koma kan aikinsa bayan jinya da ya yi.
Benitez sai a kan gadonsa ya kalli wasan Premier da Newsactle ta ci Swansea daya mai ban haushi sakamakon aiki da likitoci suka yi masa.
Sai dai bai halarci atisayen kungiyar ba, amma dai an sanar da shi dukkan abubuwan da suke wakana.
Manchester United 1-0 Basel
Marouane Fellaini
Fifa za ta fara sayar da tikitin kallon kofin duniya
Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta tsayar da ranar Alhamis domin fara sayar da tikitin kallon wasannin gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.
Tuni hukumar ta ce masu sha'awar kallon gasar za su iya neman tikitin a shafinta na Intanet wanda ta shirya sayar wa mataki biyu.
Celtic 0-2 PSG
Kylian Mbappe
Crystal Palace ta nada Hodgson kocinta
Crystal Palace ta nada tsohon kocin tawagar kwallon kafar Ingila, Roy Hodgson a matsayin wanda zai ja ragamar kungiyar kan yarjejeniyar shekara biyu.
Hodgson ya maye gurbin Frank de Boer wadda ta sallama a ranar Litinin bayan da ya kasa cin wasa a gasar Premier hudu da ya jaragamar kungiyar.
Hodgson mai shekara 70 zai horas da Palace a wasan Premier da za ta yi da Southampton a ranar Asabar.
Chelsea 2-0 Qarabag
Davide Zappacosta