Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. 'Yan takarar gwarzon kwallon kafa na Afirka na BBC na 2017
  2. Tarihin kowanne dan takara
  3. Mashu sha'awar kwallon kafa ne za su yi zabe
  4. A watan Disamba za a bayyan gwarzon kwallon kafa na Afirka na BBC na 2017
  5. Riyad Mahrez ne ya lashe kyautar 2016

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

Bayyana ra'ayinka

Nan muka kawo karshin za a rufe zabe a ranar 27 ga watan Nuwamba za a sanar da gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na BBC na 2017 a watan Disamba.

Za ku iya fara kada kuri'a

Kai tsaye
BBC

Dan takara na biyar Naby keita

Kungiya: RB Leipzig

Kasa: Guinea

Shekara: 22

Rawar da ya taka a kungiya a 2017: Yana cikin 'yan wasan Bundesliga 11 da babu kamrsu a Jamus, kuma 'yan kallon kwallo ne suka zabe shi a matsayin babu kamarsa, bayan da ya taimakawa RB Leipzig ta yi ta biyu a gasar ta Bundesliga da aka kammala.

Rawar da ya taka a Guinea a 2017: Keita ya ci kwallo a karawar da Guine ta yi da Libya da Tunisia a wasannin shiga gasar cin kofin duniya, duk da kasar ba ta kai ga samun tikiti ba, amma ya taka rawar gani.

Kai tsaye
Getty Images

Yankin Afirka da ba sa cin kyautar gwarzon dan kwallon Afirka na BBC

Kai tsaye
Google

Dan takara na hudu Victor Moses

Kungiya: Chelsea

Kasa: Nigeria

Shekara: 26

Rawar da ya taka a kungiya a 2017: Dan wasan ya ci kofin Premier a Chelsea sannan ya buga wasan karshe a kofin FA, wanda Arsenal ta lashe.

Rawar da ya taka a Nigeria a 2017: Moses ya buga wa Super Eagles wasa uku, amma yana daga cikin wadanda suka zura raga a wasan da Nigeria ta ci Kamaru 4-0 a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya. inda tuni Nigeria ta kai gasar da za a yi a Rasha a 2018 karo na uku a jere.

Kai tsaye
Getty Images

'Yan takara uku da aka sanar Sadio ko Pierre ko Salah?

Kai tsaye
Getty Images

Dan takara na uku Mohamed Salah

Kungiya: Liverpool

Kasa: Egypt

Shekara: 25

Rawar da ya taka a kungiya a 2017: Salah ya ci kwallo bakwai a wasa 11 da ya buga a gasar Premier bana, ya kuma ci biyar a gasar cin kofin Zakarun Turai a wasa shida da ya buga.

Rawar da ya taka a Masar a 2017: Rabon da Masr mai kofin Afirka bakwai ta je gasar cin kofin duniya tun 1990, amma Salah ne ya ci fenaritin da ya kai Masar gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Kai tsaye
Getty Images

Wasu 'yan wasan da suka lashe kyautar a baya

Cikin su har da Didier Drogba da Jay-Jay Okocha da Yaya Toure da kuma George Weah.

Kai tsaye
BBC

Abedi Pele

Shi ne ya fara lashe kyautar da BBC ta kirkira ta gwarzon dan kwallon kafa na Afirka.

Kai tsaye
Getty Images

Dan takara na biyu Sadio Mane

Kungiya: Liverpool

Kasa: Senegal

Shekara: 25

Rawar da ya taka a kungiya a 2017: Ya ci kwallo 13 a kakar2016-17

Rawar da ya taka a Senegal a 2017: Mane ya taimaka wa Senegal ta kai gasar kofin duniya da za a yi Rasha, rabonda ta je tun 2002.

Kai tsaye
Getty Images

Pierre-Emerick Aubameyang

Bayan Pierre-Emerick Aubameyang da ya ci kwallo 31 a 2016-17, Tony Yeboah na Ghana shi ma ya taka rawar gani a Bundesliga

Kai tsaye
Getty Images

Dan takarar farko shi ne Pierre-Emerick Aubameyang

Kungiya: Borussia Dortmund

Kasa: Gabon

Shekara: 28

Rawar da ya taka a kungiyarsa a 2017: Ya ci kwallo 40 a kungiyarsa taDortmund da kofin Jamus.

Rawar da ya taka a Gabon a 2017: Ya ci kwallo biyu a wasa uku da ya buga wa Gabon a gasar kofin nahiyar Afirka da ta karbi bakunci a 2017, amma kasar ba ta kai zagaye na biyu ba a gasar.

Kai tsaye
Getty Images

Gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na BBC na 2016

Dan wasan tawagar Algeria da Leicester City, Riyad Mahrez ne ya lashe kyautar 2016.

Kai tsaye
BBC

Yadda za a bayyana 'yan takarar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na BBC

Aminu Abdulkadir da Bara'atu Ibrahin ke gabatar da shiri kai tsaye a BBC Hausa Facebook kan yadda za a bayyana 'yan takara biyar da a kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na BBC na 2017.

View more on facebook

Labarai da dumi-dumiWasannin shiga gasar cin kofin duniya

Yanzu ana karawa a wasu wasannin shiga gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakunci wasannin a shiryar Afirka.

  • Zambia 2 : 2 Kamaru
  • Gabon 0 : 0 Mali
  • Ivory Coast 0 : 2 Morocco
  • Tunisia 0 : 0 Libya
  • Jamhuriyar Congo 0 : 0 Guinea

Yadda za a gabatar da shirin

Peter Okwoche ne da Mimi Fawaz za su gabatar da shirin tare da bako daga Nigeria tsohon dan kwallon Super Eagles, Emmanuel Amuneke.

Kai tsaye
Peter Okoche

Kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na BBC na 2017

Kai tsaye
BBC

Gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2017

A kalla mutum biliyan daya da miliyan 200 ne ke Afirka, ita ce nahiya ta biyu mafi tarin jama a.

Wasan kwallon kafa shi ne mafi farinjini tsakanin mutane da yawa a nahiyar.

Kai tsaye
Getty Images

Barkanmu da saduwa a cikin shirin sanar da 'yan takarar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2017.