Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Barin Coutinho Liverpool ba zai shafi kulob din ba ?
  2. Waye zai sayi Daniel Sturridge a kan £30m?
  3. Kane ya sake kafa tarihi
  4. Ba a yanke hukunci kan Sanchez ba
  5. Everton na son sayen Walcott

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahya

time_stated_uk

A nan muka kawo karshen bayanai da labarai kan musayar 'yan kwallon kafa. Da fatan kun ji dadin kasacewa tare da mu. Mun gode

Mo Salah zai buga fafatawar da za a yi a City - Klopp

Jurgen Klopp ya tabbatar cewa Mo Salah zai shiga fafatawar da kulob din zai yi da Manchester City ranar Lahadi.

Wane ne ba ya son Coutinho ya buga wasa?

Mo Salah
Getty Images
Mo Salah

Guardiola ya sake kafa tarihi

Pep Guardiola ya sake kafa tarihi inda ya zama gwarzon koci na wata karo na hudu a jere.

Kocin na Manchester City shi ne mutum na farko da ya samu irin wannan nasara a Gasar Premier, inda ya yi nasara a watan Satumba da Oktoba da Nuwamba da kuma Disamba.

Kulob din da yake shugabanta ne na daya a saman tebirin gasar Premier da tazarar maki 14 bayan da ya yi nasara a wasa shida a jere da kuma yin canjaras a watan da ba ayi nasara ko sau daya a kansu ba.

Dan kasar ta Spain ne ya zo na farko inda Sam Allardyce na Everton, Antonio Conte na Chelsea, Roy Hodgson na Cystal Palace,Jurgen Klopp na Liverpool da kuma Mauricio Pochettino Tottenham ke biye masa.

Manazarta da masu sharhi a fagen kwallon kafa ne suka yi zaben.

Pep Guardiola
Getty Images
Pep Guardiola

Cardiff City sun karbi aron dan wasan Norwich

Cardiff City sun karbi aron Yanic Wildschut daga Norwich har zuwa karshen kakar 2017-18.

Dan wasan mai shekara 26 ya koma Norwich ne daga Wigan a watan Janirun 2017, amma sau daya kacal ya ci kwallo a kakar wasa ta bana.

Ya bar kasarsa Netherlands a 2014 inda ya soma zuwa Middlesbrough ko da yake daga baya ya koma Wigan a watan Janairun 2016.

Yanic Wildschut
Getty Images

Oxlade-Chamberlain ya yi ta-maza

Alex Oxlade-Chamberlain ya ce barin Philippe Coutinho Liverpool ba zai shafi kulob din ba.

Dan wasan na tsakiya ya ce: "Lokacin da Phil ba ya kulob din, muna yin wasa mai kyau kuma yanzu ma muna da ‘yan wasa zakakurai wadanda za su iya zura kwallo.

"Na yi imanin cewa ‘yan wasan da muke da su za su sanya kulob din ya ci gaba. Ba na tsammanin barinsa zai shafe mu."

Mene ne ra’ayikun kan wannan kalami? Kuna ganin ya yi ta-maza ne kuwa yana da kanshin gaskiya?

Za mu ci gaba da yin nasara, in ji Oxlade-Chamberlain
Getty Images

Kane ya sake zaman gwarzon dan kwallo

Dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane ya yi kankanan da Steven Gerrard a samun kyautuka a gasar Premier inda ya zama gwarzon dan kwallon kafa na wata karo na shida.

Kane ya ci kwallo takwas a wasa shida da ya buga a watan Disamba, ciki har da kwallo uku-uku da ya ci a wasanni biyu da suka yi da Burnley da Southampton, wato ya ci kwallo 39 a gasar Premier a kakar wasa daya.

"Watakila zan iya cewa kwallon da na zura wacce ta fi burge ni ita ce wacce na kafa tarihin wannan shekara inda na ci Southampton" in ji Kane.

Na ji dadin sake kafa tarihi, in ji Kane
Getty Images

Wane hali 'yan wasan Arsenal ke ciki?

Aaron Ramsey- Ya koma kulob din

Mesut Ozil (ya yi rauni a gwiwa)- Gobe za a yi masa gwaji a ga abin da ke damun gwiwar tasa, wacce ta kumbura.

Jack Wilshere- “Labari mai kyau a kan sa shi ne, gwajin da aka yi masa bai nuna wata matsala ba. Zai buga wasa ranar Lahadi," in ji Wenger.

Laurent Koscielny and Kolasinac: Za su koma wasa makon gobe

Nacho Monreal: Zai koma wasa a farkon makon gobe

Olivier Giroud: Zai yi jinyar mako biyu

Gobe za a yi ma Mesut gwaji
Getty Images

Wane ne zai sayi Daniel Sturridge a kan £30m?

Babu shakka shi dan wasa ne mai hazaka.

Sai dai raunukan da ya rika ji sun rage masa tagomashi.

Liverpool Echo ta ba ta rahoton cewa yanzu Sturridge zai iya barin Liverpool amma kulob din na son sayar da shi a kan £30m.

An kusa soma gasar cin Kofin Duniya don haka yana bukatar ya soma murza leda.

Amma wanne kulob ne zai iya sayensa a kan £30m?

Sturridge  ya yi fama da rauni
Getty Images

Everton na son sayen Walcott

Kocin Everton Sam Allardyce ya ce kulob din na tattaunawa da Arsenal da zummar sayen Theo Walcott a ciniki na dindindin.

Allardyce ya ce Walcott - mai shekara 28- zakakurin dan wasa ne da zai karawa kulob din tasiri sannan ya yi ta zura kwallo.

Ya kara da cewa: "Zan yi farin ciki idan muka kammala cinikin. Har yanzu ba mu kai gaci ba amma dai muna tattaunawa."

Walcott - wanda sau biyu yana daukar kofin FA a Arsenal - ya buga wa kulob din wasa 395 sai dai wasan minti 47 kawai ya buga a kakar wasan Premier da muke ciki.

Allardyce ya ce zai yi murnar sayen Walcott
Getty Images
Everton na son sayen Walcott

Demi ta sanya hannu kan sabon kwantaragi a City

Kulob din Manchester City ya bayar da sanarwar cewa Demi Stokesta sanya hannu a kan sabon kwantaragin shekara uku.

'Yar wasan mai shekara 26 'yar South Shields ta taba buga wasa a Sunderland da Vancouver Whitecaps gabanin komawarta City a 2015.

Demi ta taba yin wasa a Sunderland
Getty Images

Wane kalubale Coutinho zai fuskanta?

Philippe Coutinho bai gaba murmushin da yake yi ba tun da ya koma Nou Camp sai abokan aikinsa suka gaya masa kalubalen da ke gabansa.

Watakila hakan zai sa tsohon dan wasan na Liverpool ya gane irin rawar da zai taka.

Barca ta doke Celta Vigo da ci 5-0 in da ta kai matakin kwata fainal a gasar cin kofin Copa del Rey.

Lione Messi ya zura kwallo biyu, yayin da Jordi Alba da Ivan Rakitic da kuma Luis Suarez suka taka rawar gani.

Messi ya  zura kwallo biyu
Getty Images
Messi ya zura kwallo biyu

Ba a cimma matsaya kan Sanchez ba - Wenger

Arsene Wenger ya ce ba zai " manema labarai hakikanin" gaskiya kan ko Alexis Sanchez zai bar Arsenal a lokacin musayar 'yan kwallo a Janairun nan.

"Babu wata tartibiyar magana a kansa. Ku ['yan jarida] kun riga kun yanke shawara cewa zai koma that Manchester United - sai dai ba na son gaya muku abin da ba haka yake ba. Ba a cimma matsaya a kansa ba".

"Bisa al'ada anan ya kamata ya tsaya har zuwa karshen kakar wasa, amma dai za mu ga abin da zai faru".

Arsene Wenger
Getty Images

Jama'a barkanmu da saduwa a cikin shirin yadda ake ciniki a kasuwar masayar 'yan kwallo a Turai kai-tsaye a ranar Juma'a tare da Nasidi Adamu Yahaya.