Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. Sai gobe!

  Hjama'a abin da ya samu kenan a shafinmu na labarai da sharhi kan kasuwar musayar 'yan wasa ta Tuari

 2. Spurs na neman dan wasan da Gunners ke so

  Wata kafar wasanni a Brazil UOL Esporte report ta bayar da rahoton cewar kocin Tottenham, Mauricio Pochettino, yana son ya kawo dan wasan gaban da Arsenal take so, Malcolm, zuwa Spurs a lokacin bazara.

  Malcolm
  Image caption: Malcolm
 3. Za a ladabtar da Chelsea

  Chelsea ka iya fuskantar ladabtarwa kan karya dokar sayen 'yan wasan ketare da ke da kasa da shekaru 18, in ji Guardian.

  Chelsea
  Image caption: Chelsea
 4. An kai Pele Asibiti

  Pele
  Image caption: Pele

  Gwarzon danwasan Brazil Pele yana asibiti bayan ya fadi cikin gajiya ranar Alhamis.

  Daman dai tsohon dan wasan mai shekara 77 zai tafi Landan ne a karshen wannan makon domin ya halarci wata liyafar cin abinci da kungiyar 'yan jarida masu aiki kan labaran kwallon kafa (FWA) za su shirya.

  An yi wa Pele - wanda shi ne dan wasan daya tilo ya taba lashe gasar cin kofin duniya sau uku- wasu gwaje-gwaje da ke nuna cewa ya galabaita in ji kungiyar FWA

 5. United na kan gaba wajen neman Jean-Michael Seri

  Jean-Michael Seri
  Image caption: Jean-Michael Seri

  United tana gaba da Liverpool da Chelsea wajen neman dan wasan tsakiyar Nice, Jean-Michael Seri, mai shekara 26,yayin da Manchester City take sha'awar sayen dan kasar Ivory Coast din, in ji Mirror.

 6. Benteke a Chelsea?

  Benteke
  Image caption: Benteke

  Ana ta rade radin kan 'yan wasan da Chelsea za ta iya saya, amma da alama kungiyar ta shiga kasuwar 'yan wasa ne tana neman mai cin kwallo.

  Jaridar Daily Mail ta bayar da rahoton cewa dan wasan gaban Crystal Palace, Christian Benteke, yana daya daga cikin 'yan wasan da kungiyar take son ta saya.

  Magoya bayan Chelsea, kun fi son Benteke ne akan Crouch?

 7. Bordeaux ta ki sayar wa Arsenal dan wasa

  Malcolm
  Image caption: Malcolm

  Bordeaux ba za ta sayar da dan wasanta mai shekara 20 dan asalin kasar Brazil, Malcom a wannan watan ba. Wannan labarin dai zai sa kocin Arsenal, wadda take neman dan wasan, Arsene Wenger, ya sauya inda zai sami karin dan wasan gaba, in ji, The Sun.

 8. Chelsea na son 'yan wasa biyu daga Roma

  Edin Dzeko
  Image caption: Edin Dzeko

  Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana son sayen dan wasan gaban Bosnia, Edin Dzeko, mai shekara 31, da dan Italiya Emerson Palmieri, mai shekara 23, daga Roma. 'Yan wasan biyu za su iya kai kudi fam miliyan 77, in ji Daily Star.

 9. Fernandinho ya tsawaita kwantiraginsa da Man City

  Dan wasan tsakiyar Manchester City, Fernandinho, ya tsawaita kwantiraginsa a kungiyar zuwar shekarar 2020.

  Man City dai ta sayo dan wasan mai shekara 32 ne daga Shaktar Donesk a watan Yunin shekarar 2013, kuma ya ci gasar Firimiya da ta League Cup a kakarsa ta farko.

  Fernandinho
  Image caption: Fernandinho da Guardiola
 10. Dan wasan Barcelona ya tsawaita kwantiraginsa

  Sergi Roberto
  Image caption: Sergi Roberto

  Dan wasan tsakiyar Barcelona, Sergi Roberto, ya tswaita yarjejeniyarsa da kungiyar ta Kataloniya, lamarin da zai sa ya kai shekarar 2022 a kungiyar.

  Amma duk wata kungiyar da za ta saye shi za ta biya Yuro miliyan 500.

 11. Spurs da Man United na takaran sayen dan PSG

  Lucas Moura
  Image caption: Lucas Moura

  Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham da takwararta Manchester United suna takarar sayen dan wasan Paris St-Germain, Lucas Moura, mai shekara 25, in ji L'Equipe.

 12. Man City tana neman Emre Can

  Emre Can
  Image caption: Emre Can

  Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta ce tana neman dan wasan tsakiyar Liverpool, Emre Can,mai shekara 24, amma makomarsa ka iya dogara akan tayin Liverpool ga dan wasan tsakiyar Schalke mai shekara 22, Leon Goretzka, in ji Mirror.

 13. Mene ne jaridu ke cewa?

  Daily Star

  Jaridar Daily Star ta yi ikirarin cewa Borussia Dortmund ba ta ji dadin cewa Arsene Wenger ya yi magana a bayyane game da dan wasanta , Pierre Emerick Aubameyang, ba.

  Ya kuke ganin wannan?

 14. Chelsea na neman Crouch

  Peter Crouch
  Image caption: Peter Crouch

  Chelsea tana neman tsohon dan wasan gaban Ingila, Peter Crouch, mai shekara 36, bayan ciwo ya hana Andy Carroll, mai shekara 29,komawa kungiyar ta Chelsea daga West Ham, in ji Telegraph.