Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. Sai gobe!

  Abin da ya samu kenan a labaran kasuwar musayar 'yan wasa. Sai gobe!

 2. Rooney ya saka motarsa a kasuwa

  Motar da Rooney ya saka a kasuwa
  Image caption: Motar da Rooney ya saka a kasuwa

  Wayne Rooney ya saka motarsa samfurin BMW i8 a kasuwa, in ji Liverpool Echo.

  Motar dai wadda ya saya cikin shekarar 2015 kan kudi kimanin fam 112,000 an saka ta a kasuwa kan kudi fam 64,995.

  Cikin motar ce dai Rooney ya isa Goodison Park a taron manema labaransa na farko a watan Agusta.

  A yanzu dai an hana shi tuki bayan ya amsa laifin tuki a lokacin da ya sha barasa a watan Satumba.

  Wayen Rooney
  Image caption: Wayen Rooney
 3. Javier zai bar West Ham

  Javier Hernandez
  Image caption: Javier Hernandez

  Dan wasan gaban West Ham, Javier Hernandez, zai iya barin kulob din a kasuwar musayar 'yan wasa ta watan Janairu kamar yadda ESPN ta ambato ejen dinsa yana cewa.

 4. 'Danny Welbeck ba zai bar Arsenal ba'

  Wenger
  Image caption: Wenger

  Kocin Arsenal, Arsene Wenger, ya ce dan wasan gaba Danny Welbeck ba zai bar kulob din ba a watan Janairu, duk da cewa Crystal Palace da Besiktas na son dan wasan, in ji Talksport.

 5. Juventus na shakkar sayen dan Liverpool

  Emre Can
  Image caption: Emre Can

  Juventus ta amince tana tantama game da sayen dan wasan tsakiyar Liverpool, Emre Can, wanda kwantiraginsa zai kare a lokavcin bazara, in ji Mirror.

 6. Palmieri ya yarda ya koma Chelsea

  Emerson Palmieri
  Image caption: Emerson Palmieri

  Dan wasan bayan Roma, Emerson Palmieri, ya yarda ya koma Chelsea kan wata yarjejeniyar shekara hudu yayin da ake ci gaba da tatatuanawa game da cinikin dan wasan da ya kai kudi fam miliyan 20. Komawar dan wasan mai shekara 23 Chelsea zai sa Kenedy ya koma Newcastle buga wasan aro, in ji Evening Standard.

 7. Madrid na son Salah

  Real Madrid na shirin sayen dan wasan Liverpool, Mohamed Salah, mai shekara 25, a lokacin bazara kamar yadda Liverpool Echo ta ambaci shugaban hukumar kwallon kafa ta Masar yana cewa.

  Salah
 8. Arsenal za ta sake wata musaya?

  Aubameyang
  Image caption: Aubameyang

  Kungiya kwallon kafa ta Borussia Dortmund tana neman Arsenal ta ba ta dan wasanta Olivier Giroud, mai shekara 31, in har tana son ta ba ta dan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 28, ko kuma a dakatar da cinikin zuwa lokacin bazara, in ji Mirror.

  Magoya bayan Arsenal, kun yarda a yi musayar Giroud da Aubameyang?

 9. Kocin Liverpool ya nemi gafara

  Kocin Liverpool, Jurgen Klopp, ya nemi gafara game da ce-ce-ku-cen da ya kaur tsakaninsa da wani magoya baya a lokacin da kulob dinsa ya sha kaye a hannun Swansea ranar Litinin.

  Jurgen Klopp
  Image caption: Jurgen Klopp
 10. Wenger ya tabbatar Arsenal na son Aubameyang

  Wannan ya nuna cewa Wenger ya tabbatar a hukumance cewar kulob dinsa na neman Aubameyang.

  Mutane zao su so su yadda za ta kaya.

  Aubamenyang
  Image caption: Aubamenyang
 11. Shin Mkhitaryan da Ozil za su iya taka leda a kulob daya?

  Wenger ya hakikance akan wannan.

  ya ce: "Za su iya wasa tare mana."

  Mkhitaryan
  Image caption: Mkhitaryan
 12. Ku kalli bayan jaridu...

  The i

  Ku kalli labaran wasannin da jaridu suka wallafa tukunna....

  Daily Mirror
  Daily Telegraph
 13. Manchester United ta fi samun kudi

  Man United
  Image caption: Man United

  kafar Deloitte ta wallafa wani rahoton da ke bayani game da irin kudaden da kulob-kulob na duniya ke samu inda ta ce kungiyar Man United ce ta fi samun kudi cikin shekara biyu a jere.

  Rahoton ya ce kudin da Old Trafford ta samu na baya-bayan nan shi ne fam miliyan 581.

 14. Sanchez ya rattaba hannu...

  Sanchez na rattaba hannu
  Image caption: Sanchez na rattaba hannu

  Baya ga musayar Alexis Sanchez da Henrikh Mkhitaryan tsakanin Man United da Arsenal, za mu tattauna kan abubuwa da dama ciki har da kayen da Liverpool ta sha a Swansea

 15. Man City na son Aymeric Laporte

  Aymeric Laporte
  Image caption: Aymeric Laporte

  Manchester City tana son Aymeric Laporte kuma tana tunanin biyan fam miliyan 60 na sayen dan wasan daga Athletic Bilbao, in ji Sun.