Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Barcelona da Chelsea (4-1)
  2. Besiktas 1-3 Bayern Munich (1-8)
  3. Wadanda suka kai wasan daf da na kusa da na karshe Real Madrid da Sevilla da Manchester City da Liverpool da Juventus da Roma.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

Bayyana ra'ayinka

Nan Muka kawo karshen shirin

Ana sa ran raba jadawalin gasar cin kofin zakarun Turai wasannin daf da na kusa da na karshe da ta gasar Europa a ranar Juma'a.

Tare da fatan za ku kasance da BBC domin sanin kungiyoyin da za su kara a tsakaninsu.

Sai mun sake haduwa a shirin mu na gaba.

Barcelona 3-0 Chelsea

An tashi daga wasa, kuma Barcelona ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe.

Wadanda suka kai matakin sun hada da Real Madrid da Juventus da Manchester City da Liverpool da Roma da Bayern Munich da kuma Sevilla.

Barcelona 3-0 Chelsea

Yadda wasan ke garuwa tsakanin tsakanin Barcelona da Chelsea.

Kai tsaye
BBC Sport

Barcelona 3-0 Chelsea

Chelsea ta saka Pedo ya sauyi Eden Hazard.

Barcelona 3-0 Chelsea

An bai wa dan wasan Chelsea, Marcos Alonso katin gargadi bayan da ya yi wa Paulinho keta.

Barcelona 3-0 Chelsea

Alvaro Morata ya canji Olivier Girou, shi kuwa Victor Moses ya maye gurbin Davide Zappacosta.

Ita ma Barcelona ta cire Ousmane Dembele.

Barcelona 2-0 Chelsea

Watakila Chelsea ta yi ban kwana da gasar bana kenan, kamar yadda Tottenham da Manchester United suka yi.

Kai tsaye
Getty Images

Barcelona 3-0 Chelsea

Lionel Messi ya kara na uku ta tsakankanin kafar mai tsaron ragar Chelsea.

Kwallon farko ma da ya ci ta tsakankanin kafar golan ya ci.

Kai tsaye
Reuters

Barcelona 2-0 Chelsea

Alonso na Chelsea ya kai hari mai kyau, amma Pique ya sa kafa ya tare kwallon.

Barcelona 2-0 Chelsea

Willian ya yi fushi da abokin wasansa Olivier Giroud, bayan da ya yi kokarin bashi kwallo sai ta tafi kai tsaye wajen Marc Andre Ter-Stegen.

William ya so Giroud ya zagaya ta baya ne.

Barcelona 2-0 Chelsea

Kocin Barcelona, Ernesto Valverde ya gamsu da rawar da kungiyarsa ke takawa, amma ya hangi Chelsea ta mamaye wasan tun dawowa daga hutu.

Hakn ne ya sa ya saka Paulinho ya canji Andres Iniesta.

Barcelona 2-0 Chelsea

Tun dai bayan da aka dawo hutu Chelsea sai saka kaimi take yi ta kuma samu kwana.

Ko Chelsea za ta ci kwallo kuwa Camp Nou?

Barcelona 2-0 Chelsea

Tun bayan da aka dawo daga hutu Chelsea sai kai hare-hare take ta yi.

Kai tsaye
Getty Images

An tafi hutu Barcelona 2-0 Chelsea

Barcelona 2-0 Chelsea

Chelsea ta samu bugun tazara kuma Marcus Alonso ya buga amma kwallon ya bugi turke ya fita waje.

Hari ne mai kyau.

Barcelona 2-0 Chelsea

Barcelona ba ta taba yin rashin nasara a gida ba idan har Lionel Messi ya ci kwallo a gasar cin kofin zakarun Turai a wasa 30 da ta buga.

Kai tsaye
Getty Images

Barcelona 2-0 Chelsea

Willian ya yi kokarin shiga da'irar Barcelona, amma 'yan kwallon Barcelona biyar suka yi kansa daga baya suka kwace kwallon.

Kai tsaye
AFP/Getty image

Barcelona 2-0 Chelsea

Chelsea ta kai mummunan hari, amma kwallon ya fita waje, idan har Chelsea ta ci gaba da wannan kokarin komai zai iya faruwa.

Barcelona 2-0 Chelsea

Ousmane Dembele ya taimawa Barcelona ta ci kwallo tara a wasa 12 a gasar cin kofin Zakarun Turai da ya buga, inda ya ci uku daga ciki.

Kai tsaye
Getty Images

Barcelona 2-0 Chelsea

Akwai aiki a gaban Chelsea , sun taba tashi 2-2 da Barcelona a 2012, inda suka fitar da Barca daga gasar sannan suka kai wasan karshe.

Wannan karon ma abinda suke bukata kenan.

Barcelona 2-0 Chelsea

An bai wa dan wasan Barcelona Sergio Roberto katin gargadi bayan da ya ja Eden Hazard.

Barcelona 2-0 Chelsea Ousmane Dembele

Kai tsaye
Rex Features

Barcelona 1-0 Chelsea

Chelsea na taka rawar gani

Willian,ya buga kwallo daga yadi na 25, yayin da mai tsar matsaron ragar Barcelona, Marc Andre Ter-Stegen iya hana ta shiga raga..

Barcelona 1-0 Chelsea

Chelsea na kai hare-hare tun bayan da Barcelona ta ci ta.

Barcelona 1-0 Chelsea

Kwallon da Messi ya ci Chelsea a minti biyu da dakika takwas ita ce mafi sauri da ya ci a gasar cin kofin zakarun Turai.

Kai tsaye
Getty Images

Barcelona 1-0 Chelsea

Yadda ake gara kwallo tsakanin kungiyoyin biyu

Kai tsaye
BBC Sport

Barcelona 1-0 Chelea Lionel Messi

A Ingila ma shi ne ya farke wa Barcelona kwallo

Kai tsaye
Getty Images

An take kwallo Barcelona 0-0 Chelsea

Barcelona da Chelsea

'Yan wasa sun fito fili suna gaisawa a tsakaninsu, yan kallo kowa ya kama wurin zama da sauran jami'ai.

Barcelona da Chelsea

Luis Suarez ya dade bai ci kwallo a gasar cin kofin zakarun Turai ba, rabon da ya ci tun a watan Maris din 2017, bayan da ya ci Paris St-Germain.

Kai tsaye
BBC Sport

Muhawarar da kuke yi a BBC Hausa Facebook

Sunusi Ahmad Kano: Barcelona kam suna da cikakkiyar damar yin nasanar to amma sun san Chelsea ba kanwar lasa ba ce ganin yadda suke takawa Barcelona birki a lokatan baya. Inawa Chelsea fatan kai wa zagaye na gaba.

Hassan Sani Idris: Gaskiya bana jin club din Ingila akwai wanda zai iya cinye Barcelona.

Barcelona da Chelsea

Kocin Chelsea, Antonio Conte ya ce za su sha wahala a karawar da za su yi da Barcelona a Camp Nou, amma za su yi iya kokarinsu suga sun samu nasara.

Kai tsaye
Getty Images

Chelsea

Kai tsaye
BBC Sport

Barcelona

Kai tsaye
BBC Sport

Barcelona da Chelsea

Kai tsaye
BBC Sport
Kai tsaye
Getty Images

Ra'ayin Suraj Bello Suraj kan Barca da Chelsea

Ra'ayin Suraj Bello Suraj kan Barca da Chelsea

Barcelona da Chelsea

Wannan ne wasa na 14 da kungiyoyin biyu za su kara a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Kai tsaye
Getty Images

An tashi wasa Besiktas 1-3 Bayern Munich (1-8)

Bayern Munich ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe, inda jumulla ta ci kwallo 8-1.

A karawar farko a Jamus kwallo 5-0 ta ci.

Kai tsaye
Reuters

Ra'ayin Jibrin Soja kan Barca da Chelsea

Ra'ayin Jibrin Soja, Minna kan Barca da Chelsea