Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Naziru Mikailu

time_stated_uk

Bayyana ra'ayinka

 1. Ruwan sama a Turin

  Juventus da Real Madrid

  Ana tafka ruan sama a birnin Turin amma duka da haka magoya baya na ci gaba da tururuwa domin zuwa kallon wasan.

  Za a fara murza-leda nan da minti 20. Sai a kasance da mu.

 2. Sau nawa Juventus ta taba doke Madrid?

  A bara dai Madrid ce ta doke kungiyar a wasan karshe na gasar, abin da ya ba ta damar daukar kofin gasar a birnin Cardiff na kasar Birtaniya.

  A koawace karawa da Madrid ta taba yi da Juventus, Ronaldo yana samun zura kwallo a raga.

  Sau 19 kungiyoyin suna haduwa a tarihin gasar Zakarun Turai -Madrid ta yi nasara a wasanni tara, yayin da Juventus ta samu nasara a wasanni takwas, sun kuma yi kunnen doki a wasanni biyu.

  Hakazalika, duka kungiyoyin biyu kowace ta zura wa abokiyar karawarta kwallaye 22 ne a raga a tarihin karawarsu.

  Ronaldo
  Image caption: Ronaldo ya ci Juventus kwallo bakwai a wasa biyar
 3. Tawagar Juventus

  Da za ta kara da Real Madrid

  Masu tsaron gida: Buffon, Szczesny da De Sciglio

  'Yan wasan baya: Barzagli, Marchisio, Chiellini, Asamoah, Rugani, Lichtsteiner da Alex Sandro 'Yan wasan tsakiya: Khedira, Bentancur, Matuidi, Pinsoglio, Cuadrado, Bentancur, Sturaro da Marchisio

  'Yan wasan gaba: Higuaín, Douglas Costa, Mandžukić da Dybala.

  Franck Ribery
  Image caption: Bayern na dab da lashe gasar Bundesliga ta bana
 4. Tawagar Real Madrid

  Da za ta fafata da Juventus

  Ronaldo yana atisaye

  Masu tsaron gida: Keylor Navas, Casilla da Luca

  'Yan wasan baya: Carvajal, Vallejo, Ramos, Varane, Nacho, Marcelo, Theo da Achraf. 'Yan wasan tsakiya: Kroos, Modric, Casemiro, Llorente, Asensio, Isco, Kovacic da Ceballos.

  'Yan wasan gaba: Cristiano Ronaldo, Benzema, Bale, Lucas Vázquez da kuma Mayoral.

 5. Labarai da dumi-dumiJuventus da Real Madrid

  Real Madrid ta bayyana sunayen 'yan kwallon da suka buga mata wasan karshe a Cardiff wanda ta yi a watan Mayu ta kuma lashe kofin karo na 12 jumulla.

  Hakan na nufin Gareth Bale yana kan benci kenan.

 6. Sau nawa kungiyoyin suka kara

  Sau 19 kungiyoyin suna haduwa a tarihin gasar Zakarun Turai - Madrid ta yi nasara a wasanni tara, yayin da Juventus ta samu nasara a wasanni takwas, sun kuma yi kunnen doki a wasanni biyu.

  Yayin da wannan ne karon farko da za a kara tsakanin Sevilla, wacce ba ta taba lashe gasar ba, da Bayern Munich wacce ta lashe sau biyar.

  'Yan wasan Juventus
 7. Barkanmu da yamma...

  Gasar cin kofin Zakarun Turai

  Jama'a barkanmu da saduwa a wannan shiri na musamman inda za mu kawo muku sharhi kai tsaye kan wasannin cin kofin zakarun Turai.

  A yau za a fafata ne tsakanin Juventus da kuma Real Madrid, sai Sevilla da Bayern Munich a wasan gab da na kusa da na karshe.

  Real Madrid da Juventus