Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Liverpool 3-0 Manchester City
  2. Barcelona 4-1 AS Roma
  3. Liverpool da Man City sun kara sau 179 a wasannin gasar Ingila
  4. Wannan ne karon farko da Liverpool da City za su kara a kofin zakarun Turai
  5. Liverpool ta ci karawa 87, City ta yi nasara a wasa 45 da canjaras 46
  6. Har yanzu ba a ci Barcelona a La Liga ba, inda ta ci wasa 23 da canjaras 7

Rahoto kai-tsaye

Daga Naziru Mikailu

time_stated_uk

Bayyana ra'ayinka

Muna godiya...

Liverpool 3-0 Man City, Barca 4-1 Roma

Jama'a a nan muka kawo karshen wannan sharhi sai a ci gaba da kasance wa da BBCHAUSA.COM domin samun labaran wasanni da ma sauran labarai.

Muna taya magoyan Liverpool da na Barcelona murnar nasarar da suka samu.

Hotuna daga Anfield

Liverpool 3-0 Man City

Liverpool
Reuters
Guardiola
Reuters
Liverpool
AFP

Liverpool
Reuters

An kara minti uku

Liverpool 3-0 Man City

Man City na ta kai kora

Liverpool 3-0 Man City

Amma har yanzu babu labari. Klopp da Guardiola sun kasa zama

Liverpool da Man City
Reuters

An ba wa Henderson katin gargadi

Hakan na nufin ba zai buga kashi na biyu ba a mako mai zuwa

Kwana biyu a jere

Liverpool 3-0 Man City

City sun samu kwana biyu a jere amma duka babu labari.

An cire Mo Salah

Saboda ya ji rauni - Wijnaldum ne ya maye gurbinsa

Barcelona 2-0 Roma

Samuel Umtiti (minti 55)

Barca sun kai kora

Barcelona 1-0 Roma

Iniesta ya ba wa Lionel Messi kwallo amma kwallon da ya buga ta daki Alisson Becker.

Messi
Reuters

An dawo wasa kaor na biyu

Liverpool 3-0 Man City, Barca 1-0 Roma

An tafi hutun rabin lokaci

Liverpool 3-0 Man City

Man City ba su kai harin da ya fuskanci raga ba a minti 45 na farko.

Liverpool da Man City
BBC Sport

Nicolas Otamendi - Man City

Barcelona 1-0 Roma

Daniele de Rossi ya ci gida (minti 38)

Saura kiris Liverpool su kara da hudu

Liverpool 3-0 Man City

Har yanzu babu ci

Barcelona 0-0 AS Roma

Amma barcelona na ta kai kora - sun ma daki turken raga sannan sun ci kwallo an hana saboda satra gida.

View more on twitter

Liverpool 3-0 Man City - Sadio Mane

Mo Salah ne ya bugo kwallon daga gefen dama sannan Mane ya yi tsalle ya sa kai - sai raga.

Liverpool
Reuters

Ta yaya za ka bar Salah ba tare da maki ba

Robbie Savage

Tsohon dan wasan Leicester City da Wales a BBC Radio 5 live

City sun yi kuskure duk da cewa Salah ya yi satar gida, ba zai yi wu kabar mutumin da ya ci kwallaye da yawa a bana ba ba tare da wani yana binsa ba.

Liverpool 2 -0 Man City

Alex Oxlade-Chamberlain

saura kiris City ta rama

Liverpool 1-0 Man City

Man City sun kai mummunan hari ta hannun Sane amma ya buga kwallon ta yi gefe sosai.

Barca ta ci amma...

Suarez ya ci kwallo amma an hana saboda ya yi satar gida

Liverpool 1-0 man City - Mo Salah

Salah
AFP

An fara wasa

Liverpool da Man City, Barca da Roma

Messi ya buga wasa 100 a gasar Zakarun Turai

Barcelona da Roma

Daf da fara wasa

Liverpool da Man City, Barca da Roma

Filin wasa na Anfield da Nou Camp sun cika makil da 'yan kallo - Liverpool da Man City - Barcelona da AS Roma.

View more on twitter

Klopp ya nemi afuwar Guardiola kan jefan da aka yi musu

Liverpool da Man City

Kocin Liverpool Jurgen Klopp: "A gaskiya ban gane wannan ba.Mun yi kokari domin ganin mun kaucewa irin wannan yanayin... Ina neman afuwa a madadin Liverpool." Kocin Man

Kocin Manchester City Pep Guardiola: "Na gode wa Jurgen da afuwar da ya nema. Ba mu yi tsammanin haka ba,.. wannan ba dabi'ar 'yan Liverpool ba ce".

Man City
Getty Images

An fara motsa jiki

Liverpool da Man City

Duka kungiyoyin biyu sun fito domin motsa jiki.

Daga dukkan alamu filin wasa na Anfield ya yi shar bayan ruwan saman da aka yi.

Liverpool da City
BBC Sport

Guardiola ya fi kowanne koci

Liverpool da Man City

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce wannan wasa ne mai kyau kuma za mu yi kokarinmu. Ina girmama Pep Guardiola sosai.

Ina ganin shi ne kocin da ya fi kowanne kwarewa a duniya.

Mun kara a wasu wasanni kadan... Ina ganin koci ne mai kyau kuma yana da kyakkyawar mu'amala.

Liverpool da Man City
Reuters

Rabon da Suarez ya ci kwallo...

Barcelona da Roma

Suarez
Getty Images

Abin al'ajabi, wata 13 rabon da Luis Suarez ya ci kwallo a gasar zakarun Turai. Kamar kullum yau ma yana cikin tawagar Barcelona tare da Messi.

John Stones dan bayan City ya ci kwallo uku tun wancan lokacin...