Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Karo na takwas kenan da Chelsea ta ci FA a tarihi
  2. Wannan shi ne karo na takwas da kungiyoyin biyu ke karawa a Wembley
  3. Karo na 20 da United ke buga wasan karshe
  4. Fafatawa ta 13 da Chelsea ke kai wa wasan karshe
  5. United ta lashe kofin FA sau 12, ita kuwa Chelsea sau 7

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

Bayyana ra'ayinka

Nan muka kawo karshen shirin tare da fatan za ku tara a shirin mu na gaba.

Mohammed Abdu Mamman Skeeper ke yi muku barka da shan ruwa.

An bai wa Chelsea kofin FA na shekarar nan

Kungiyar Chelsea ta karbi kofin FA na bana da ta ci a ranar Asabar bayan da ta doke Manchester United da ci 1-0 a Wembley.

Tuni kuma 'yan wasa da koci suka shiga cikin fili inda suka yi hotuna da murnar lashe kofin da suka yi,sannan suka je majen magoya baya suka kuma jinjina musu.

Kai tsaye
Getty Images

Yadda kungiyoyin biyu suka murza leda

Kai tsaye
BBC Sport

Mourinho ya rungumi Conte

Bayan da aka tashi daga wasa Jose Mourinho ya rungumi Antonio Conte inda ya yi masa murna kan nasarar cin kofin Kalubale da ya yi.

Labarai da dumi-dumiChelsea ta lashe kofin FA na bana

An tashi wasa kuma Chelsea ta lashe kofin kalubalen Ingila na bana kuma na takwas jumulla.

Kai tsaye
BBC Sport

William ya canji Hazard

Chelsea ta sake yin sauyi, inda Wiliam ya shiga fili shi kuwa Hazard ya je ya huta.

Chelsea ta fitar da Giroud

Chelsea ta saka Motara inda ya sauya Giroud.

Kai tsaye
Reuters

United ta sake yin sauyi

Mai tsaron baya Phil Jones ya fita, inda Mata ya maye gurbinsa.

Kai tsaye
Reuters

Chelasea 1-0 Man United

An yi cnin kasuwar sama da mai tsaron ragar Chelsea, bayan da United take ta kai kora, kwallo ta fita kwana.

United ta sauya 'yan wasa

Romelu Lukaku da kuma Anthony Martial sun shiga fili, inda suka maye gurbin Jesse Lingard da kuma Marcus Rashford.

Kai tsaye
Getty Images

Chelsea ta ci gaba da tsare gidanta

Rashford ya samu dama mai kyau amma ya barar, bayan da ya buga kwallo ta bugi golan Chelsea sannan ta koma ta doki jikinsa sannan ta yi wajen fili.

Ko United za ta sa Lukaku kuwa?

Manchester United ta saka kaimi ko za ta farke kwallon da aka zura mata a raga, abin tambaya ko za ta saka Lukaku a karawar domin ya cece ta?

Kai tsaye
Reuters

Chelsea 1-0 Man United

Chelsea ta koma tsare baya tun lokacin da aka koma zagaye na biyu, inda ya bai wa United kara matsa mata da kai hare-hare.

Kai tsaye
BBC Sport

Chelsea 1-0 Man United

Sanchez ya ci kwallo amma mataimakin alkalin wasa ya ce ya yi satar gida.

Chelsea 1-0 Man United

Hazard ya kai kora ta gefe ya kuma buga kwallo amma mai tsaron ragar United, De Gea ya rike ta garam.

Kai tsaye
Getty Images

Chelsea 1-0 Man United

An bai wa Valencia katin gargadi bayan da ya yi wa Hazard keta.

Chelsea 1-0 Man United

Tun da aka koma zagaye na biyu, United sai kai hare-hare take ta yi domin farke kwallon da aka zura mata.

Rasford ya buga kwallo amma golan Chelsea ya hana ta shiga raga.

Chelsea 1-0 Man United

Victor Moses ya yi wa Ashley Young keta, an kuma bashi katin gargadi

Chelsea 1-0 Man United

An yi wa Hazard keta, United kokari suke su nakasa Chelsea idan har aka fitar da Hazard domin shi ne yake takura wa a karawar.

Chelsea 1-0 Man United

An kamo kashi na biyu a wasan karshe na cin kofin FA da ake fafatawa a Wembley.

Chelsea 1-0 Man United

Fenaritin da Eden Hazard ya ci shi ne na farko tun bayan wadda Ruud van Nistroy ya zura a ragar Millwall a shekarar 2004 a wasan karshe a kofin FA, idan ka cire bugun fenaritin da ake yi idan kungiyoyi sun tashi babu ci ko kuma canjaras.

Kai tsaye
Getty Images

Chelsea 1-0 Man United

Chelsea ce da ci daya mai ban haushi, ita kuwa Manchester United da murza kwallo.

Kai tsaye
BBC Sport

Chelsea 1-0 Man United

An tafi hutun minti 15 sannan su dawo wasa karo na biyu da za su sake yin minti 45 nan gaba.

Chelsea 1-0 Man United

Bayan Chelsea a daure take 'yan wasan United sun kasa ratsa ta balle su yi abin azo a gani.

Kai tsaye
Reuters

Muhawar da kuke yi a BBC Hausa Facebook

Gazzali Abdullahi: Mohammad abdu ina yi muku fatan alkhairi daga Garzali Abdullahi Tsamiyar mai baba karamar hukumar Rogo jihar Kano, Nigeria.

Shu'aibu Idris Kofar-fada Bulangu: Gaskiya wannan wasa akwai alamun Manchester united ce ke da nasara, duba yadda al'amura suka tabarbarewa Chelsean a karshe-karshen kakar wasanni ta bana.

Abdulbasid Abdullahi: Man United za ku gane baku da wayo domin za ku sha samba da mazgada a hannun Willian da Hazard, up Chelsea daga A.A.G

Chelsea 1-0 Man United

Rana na haske idanun magoya bayan Chelsea, da sun sani sun je filin da hula hana salla.

Kai tsaye
PA

Chelsea 1-0 Man United

Hazard ya buga fenariti ya kuma cin kwallon inda De Gea ya yi bangare guda kwallo kuma ta shiga raga.

Kai tsaye
Getty Images

Chelsea 0-0

Phil Jones na Manchester United ya kayar da Hazard a cikin da'ira ta 18 din United, an bai wa Chelsea fenariti.

Kai tsaye
Getty Images

Chelsea 0-0 Man United

Chelsea ta nemi fenariti ta hannun Tiemoue Bakayoko bayan da ya fadi a da'irar ta 18 din United, sakamakon hannu da Nemanja Matic ya dora masa a bayansa.

Kai tsaye
Getty Images

Chelsea 0-0 Man United

United ta kai kora a karon farko inda Marcus Rashford ya rike kwallo ya buga ta cikin da'ira ta Chelsea amma sun fitar da ita.

Chelsea 0-0 Man United

Olivier Giroud na Chelsea ya yi satar gida.

Chelsea 0-0 Man United

Eden Hazrd ya kai hari mai kyau, sai dai golan United David De Gea ya sa kafa ya hana kwallo shiga riga.

Kai tsaye
Reuters

Chelsea 0-0 Man United

Ander Herrera yana tsaron baya domin ya tare Eden Hazard.

An take wasa Chelsea 0-0 Man United

Yarima William bai halarci Wembley ba

Kai tsaye
Getty Images

Chelsea 0-0 Man United

Mai goyon bayan Manchester United, Rachel Riley ta halarci Wembley, domin ayi komai a idon ta.

Kai tsaye
Reuters

Chelsea 0-0 Man United

A ranar Lahadi aka kammala gasar Premier ta bana, Manchester City ce ta lashe kofin kuma karo na uku.

Manchester United ce ta yi ta biyu, ita kuwa Chelsea ta biyar ta yi, za ta buga gasar Europa a badi.

Kai tsaye
BBC Sport

Chelsea 0-0 Man United

Wannan ne karo na uku da kungiyoyin ke karawa a tsakaninsu a wasan karshe kuma fafatawa ta takwas a Wembley.

Wadanda suka hadu a wasan karshe a FA sau uku sun hada da (Arsenal da Liverpool, Arsenal da Newcastle da kuma Aston Villa da West Brom).

A haduwa biyu baya da suka yi Manchester United ta ci 4-0 a shekarar 1994, ita kuwa Chelsea ta yi nasara da ci 1-0 a shekarar 2007, kwallon da Didier Drogba ya fara cin United kenan, kuma wasan farko a Wembley bayan da aka yi wa filin gyara.

Kai tsaye
Getty Images

Chelsea 0-0 Man United

Manchester United ta lashe kofin FA sau 12, kuma wannan ne karo na 20 da take buga wasan karshe.

Wannan ne karo na 13 Chelsea za ta yi kofin FA, wanda ta dauka karo bakwai a tarihi.

Kai tsaye
Getty Images

Muhawar da kuke yi a BBC Hausa Facebook

Chiroma Hadi Khan Jallo: Akwai alamun wasan zai kayatar, idan Mourinho bai yi wasan tsare gida ba.

Ammar Mai Arsenal Makera: Fadan da babu ruwanka dadin kallo gare shi, amma ina bayan kanne na Chelsea.

Haruna Yusuf Daura: Ai inda sabo Conte ya saba doke Mourinho, wannan wasa tarihi ne zai maimaita kanshi up Chelsea.