Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Croatia 2-0 Najeriya
  2. Croatia da Najeriya suna rukunin D tare da Iceland da Argentina
  3. Wasan Argentina da Iceland an tashi 1-1
  4. Wannan ne karon farko da Croatia da Najeriya suka hadu
  5. Croatia ta samu nasara wasanta na farko a kofin duniya
  6. Najeriya ta samu nasara daya a wasanni 12 a gasar kofin duniya, ta doke Bosnia-Herzegovina a 2014

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

Sai wani lokacin

Croatia 2-0 Najeriya

A nan muka kawo karshen sharhin kai-tsaye da muka kawo ma ku a gasar cin kofin duniya

Sai wani lokacin.

Najeriya tana kasan teburin rukuni

Croatia 2-0 Najeriya

Croatia ke jagorantar rukunin D bayan ta doke Najeriya. Argentina da Iceland sun tashi 1-1

Rukunin D
BBC

Croatia ta doke Najeriya

Croatia 2-0 Najeriya

An hure wasa

Croatia 2-0 Najeriya

Kovacic ya yi gaba da gaba da golan Najeriya

Croatia 2-0 Najeriya

Amma golan ya kame

Yadda Modric ya ci Najeriya a Fanareti

Croatia 2-0 Najeriya

Modric
Reuters

An kara minti hudu

Croatia 2-0 Najeriya

An fitar da Mikel

Croatia 2-0 Najeriya

Nwankwo ya karbe shi

Najeriya ta nemi rama kwallo daya

Croatia 2-0 Najeriya

Pjaca ya karbi Mandzukic

Croatia 2-0 Najeriya

Croatia ta sake canji

Saura minti biyar a hure wasa

Croatia 2-0 Najeriya

An bayar da Fanareti biyar a rana daya

Croatia 2-0 Najeriya

Messi ya barar da Fanareti a wasan Argentina da Iceland. Fanareti biyar aka bayar a wasannin da aka buga a yau Asabar

Messi
Getty Images

Iheanacho ya kai kora

Croatia 2-0 Najeriya

Ya nemi ya ba musa ya ci amma Strinic ya kabe wa Croatia kwallon

Kovacic ya karbi Rebic

Croatia 2-0 Najeriya

Croatia ta yi canji

Saura kiris Croatia ta kara

Croatia 2-0 Najeriya

Iheanacho ya karbi Ighalo

Croatia 2-0 Najeriya

Najeriya ta sake yin canji

Croatia ta dawo tana matsawa Najeriya

Croatia 2-0 Najeriya

Modric ya ci fanareti

Croatia 2-0 Najeriya

Modric

Croatia 2-0 Najeriya

Croatia ta samu fanareti

Croatia 1-0 Najeriya

Ekong ya yi wa Mandzukic keta bayan an bugo kwana

Yanzu kalubale ya fi yawa kan Najeriya

Croatia 1-0 Najeriya

Idan Najeriya ta bari aka tashi a haka, za ta kasance ta karshe a rukunin D, bayan Iceland ta rike Argentina 1-1

Moses ya nemi fanareti

Croatia 1-0 Najeriya

Moses ya fadi a gidan Croatia bayan ya samu kwallo a kafar Mikel amma alkali ya hana fanareti

Najeriya ta yi canji

Croatia 1-0 Najeriya

Musa ya karbi Iwobi

Croatia ta yi canji

Croatia 1-0 Najeriya

Brozovic ya karbi Kramaric

Ighalo ya yi yunkuri

Croatia 1-0 Najeriya

Ya sa kai amma golan Croatia ya kama

Najeriya ta fi kai hari bayan hutun rabin lokaci

Croatia 1-0 Najeriya

Najeriya na shirin canji

Croatia 1-0 Najeriya

An tayar da Kelechi Iheanacho da Ahmed Musa suna motsa jiki

Saura kiris Croatia ta kara

Croatia 1-0 Najeriya

Rakitic ya nemi raga daga nesa

Croatia 1-0 Najeriya

Amma kwallon ta bi saman ragar Najeriya

Super Eagles sai sun yi da gaske

Croatia 1-0 Najeriya

Sai Najeriya ta yi da gaske kafin haduwarta da Iceland da ta yi kunnen doki da Argentina.

Moses ya kai kora

Croatia 1-0 Najeriya

Amma ya buga kwallon ta fita

Najeriya sun samu kwana

Croatia 1-0 Najeriya

Najeriya ta samu kwana uku

An dawo

Croatia 1-0 Najeriya

Croatia ta fi Najeriya taba kwallo

View more on twitter

Ko kun san cewa?

Croatia 1-0 Najeriya

Nasarori biyar da Najeriya ta samu a wasanni 18 da ta buga a gasar cin kofin duniya, kasashen Turai ne ta doke. Najeriya ta doke Bulgaria 3-0, Girka 2-0 a 1994, Spain 3-2 da Bulgaria 1-0 a 1998, Sai Bosnia Herzegovina 1-0 a 2014. Ko a bana Super Eagles za su gagari Croatia?

Najeriya
Getty Images

Yadda aka fafata a kafin rabin lokaci

Croatia 1-0 Najeriya

Najeriya da Croatia
Getty Images
Najeriya da Croatia
Getty Images
Najeriya da Croatia
Getty Images
Najeriya da Croatia
Getty Images
Najeriya da Croatia
Getty Images

An tafi hutun rabin lokaci

Croatia 1-0 Najeriya

Mandzukic ya kai wa Najeriya hari

Croatia 1-0 Najeriya

Kwallo ta taba Etebo ne ta shiga raga.

Najeriya
FIFA

Saura kiris Croatia ta kara

Croatia 1-0 Najeriya

Kramaric ya nemi karawa Najeriya amma kwallon ta bi saman raga

Yadda Najeriya ta ci kanta

Croatia 1-0 Najeriya

Oghenekaro Etebo ya ci wa Croatia kwallo a ragar Najeriya.

Croatia
Getty Images

Etebo ya ci kansu

Croatia 1-0 Najeriya

Dan wasan Najeriya Etebo ne ya ci kansu