Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. An nada sabon shugaban DSS

  Matthew B. Seiyefa, mutumin da ya fi mukami a hukumar tsaro ta farin kaya bayan ya kori Lawal Daura, ya zama shugaban hukumar.

  Gwamnatin Najeriya ce ta bayar da wannan labarin a shafinta na Twitter.

  Hakazalika rahotanni a Najeriyar na cewa mukaddashin Shugaban Najeriyar, Yemi Osinbajo, yana ganawa da sabon shugaban hukumar.

  View more on twitter
 2. Karanta rudanin da aka shiga ranar Talata a majalisar dokokin Najeriya

  An shiga rudani a majalisar dokokin Najeriya ranar Talata bayan wasu jami'an tsaro na farin kaya (DSS) suka hana wasu sanatoci shiga majalisar, lamarin da ya sa mukaddashin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya kori shugaban hukumar DSS, Lawal Daura, daga aiki.

  Karanta yadda aka yi rudanin a nan:

 3. 'Saraki zai gabatar da jawabi ga 'yan jarida'

  Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki zai gabatar da jawabi ga wani taron manema labarai ranar Laraba, in ji mai taimaka masa kan harkokin kasa-da-kasa, Banks Omisore.

  A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ne Omisore ya fitar da sanarwar.

  Saraki
 4. 'Za mu hukunta jami'an tsaron da ke da hannu a wannan aiki'

  Mukaddashin shugaban Najeriya,Yemi Osinbajo, ya bayyana hana shiga majalisar da aka yi ranar Talata a matsayin yin karar tsaye ga dokar kasa.

  A cikin wata sanarwar da mai taimaka masa kan harkar watsa labarai, Laolu Akande, ya fitar shugaban ya ce aikin, wanda aka yi ba bisa sanin fadar shugaba ba, abin Allah-wadai ne wanda ba za a lamunta ba.

  Osinbajo ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewar za a gane tare da hukunta dukkan wadanda ke da hannu a wannan aiki na "take doka".

  Osinbajo
 5. Osinbajo ya gana da Lawal Daura kafin ya kore shi

  Daura

  Bayanai sun nuna cewar mukaddashin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya gana da shugaban rundunar tsaro ta farin kaya (DSS), Lawal Daura, kafin ya kore shi.

  Kamfanin dillacin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewar Osinbajo ya gana da sufeto janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, da shugaban DSS, Malam Lawal Daura ranar Talata, bayan jami'an DSS sun hana wasu sanatoci shiga zauren majalisar dattawan kasar.

  Duk da cewar daga bayan jami'an sun kyale sanatocin sun shiga majalisar, NAN ta ce Idris ya isa ofishin Osinbajo da misalin karfe 12.35 na rana, yayin da Daura ya isa da misalin karfe 1.15 na rana.

 6. An kori shugaban DSS Lawan Daura

  Mukaddashin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya kori shugaban hukumar jami'an tsaro ta farin kaya, Lawal Daura.

  Osinbajo, wanda ya zama mukaddashin shugaban kasa tun lokacin da shugaban Buhari ya tafi hutun kwana goma a Landan, ne ya bayar da wannan umarnin ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkar yada labarai, Laolu Akande.

  Wata sanarwar da Laolu Akande, ya fitar ranar Talata, ta ce an umarnin Lawal Daura ya mika ragamar shugabancin hukumar ga jami'i mafi girma a hukumar ta DSS.

  View more on twitter
 7. "Akpabio ya yi murabus daga mukaminsa a majalisa"

  Rahotanni sun ce shugaban marasa rinyaje a majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ya sauka daga kujerarsa.

  Shugaban dai ya sauka ne daga kujerar shugaban marasa rinjaye gabannin bayyana ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki.

  Hakazalika sanatan ya wallafa wasikar barin mukamin nasa a shafinsa na Twitter.

  View more on twitter
 8. Abin da ya faru a majalisa maganar majalisa ce —APC

  Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ce jam'iyyar ba ta da hannu kan abin da ya faru a majalisar dokokin kasar ranar Talata.

  Wata sanarwar da mukaddashin kakakin jam'iyyar, Yekini Nabena, ya fitar, ta ce duk da cewa jam'iiyar tana sa ido kan abin da ke faruwa a majalisar kamar dukkan 'yan Najeriya, babu hujjar daura wa shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomhole, laifin abin da ya faru a majalisar.

  Saboda haka, jam'iyyar ta ce abin da ya faru a majalisar lamari ne kawai na majalisar dokoki.

  Majalisa
 9. "An dage zaman jami'an majalisa"

  An dage zaman jami'an majalisar dokokin Najeriya saboda irin yanayin da majalisar ta sami kanta ranar Talata, in ji mataimakin kakakin majalisar wakilai, Yusuf Lasun.

  Lasun ya shaida wa manema labarai hakan ne a wajen zauren majalisar.

  Wajen zauren majalisa
  Image caption: Manema labarai na zaman jiran abin da zai faru a wajen zauren majalisar ranar Talata
 10. "PDP ce ta janyo hatsaniyar da aka yi a majalisa"

  Sai dai kuma, wani dan majalisar wakilai na jam'iyyar APC daga jihar Edo, Johnson Agbonayinma ya ce 'yan jam'iyyar PDP ne suka janyo hatsaniyar da ta faru a majalisar dokoki domin tayar da zaune-tsaye.

  Johnson Agbonayinma
  Image caption: Johnson Agbonayinma
 11. Rashin daukar mataki ne ya kai DSS majalisa —Atiku

  Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, wanda yake neman takara shugaban kasa a zaben badi, ya ce rashin daukar mataki kan abin da jami'an tsaro suka yi a jihar Binuwe cikin mako biyun da suka gabata n ya sa jam'ain tsaron farin kaya suka je majalisar dokoki.

  Atiku ya fadi haka ne a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

  View more on twitter
 12. "Sanatoci na kokarin kare dimokradiyya"

  An wallafa wani bidiyo a shafin Twitter na majalisar dattawan Najeriya wanda aka ce na sanatoci ne wadanda ke kokarin "kare dimokradiyya daga juyin mulki kan majalisar dokoki."

  View more on twitter
 13. 'Buhari ba shi da hannu a cikin abin da ya faru a majalisa'

  Mai taimaka wa Shugaban Najeriya kan lamuran majalisar dokoki, Ita Enang, ya shaida wa BBC cewar, Shugaba Muhammadu Buhari ba shi da masaniya kan lamarin da ya auku a majalisar dokokin kasar ranar Talata.

  Ita Enang daga hagu
  Image caption: Ita Enang daga hagu ya ce Buhari ba shi da hannu kan abin da ya faru ranar Talata
 14. Abin kunya ne ya faru a majalisa —Sanata Misau

  Isah Hamma Misau
  Image caption: Sanata Isah Hamma Misau yana daya daga cikin 'yan majalisar da suka sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP cikin 'yan kwanakin nan.

  Sanata Isah Hamma Misau, mai wakiltar mazabar Bauchi ta tsakiya, ya yi zargin cewar jami'an tsaro sun yi kokarin bai wa 'yan hamayya a majalisar kariya wajen aikata ba daidai ba.

  Ya kuma bayyana takaicinsa kan lamarin da ya bayyana a matsayin abin kunya.

 15. Jami'an tsaron sun hana sanatoci shiga majalisa

  Jami'an tsaron Najeriya na farin kaya (DSS) sun hana wasu 'yan majalisar dattawan kasar shiga zauren majalisar da safiyar Talata.

  Jami'ian, da suka ce sun tare hanyar shiga zauren ne bisa umarnin da aka ba su 'daga sama', sun kyale 'yan majalisar sun shiga zauren majalisar daga baya.

  Rahotanni dai suna zargin cewar hana 'yan majalisar shiga na da alaka da yunkurin tsige shugaban majalisar, Bukola Saraki.

  Jami'an tsaro
 16. Barka da shigowa wannan shafin

  Jama'a, barkanku da shigoiwa wannan shafin inda za mu kawo muku labarai da sharhi game da rudanin da aka shiga a majasalisar dokokin Najeriya.