Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Kocin Man Utd Mourinho "ba shi da kwarin gwiwa" game da sayen 'yan wasa
  2. Chelsea ta dauki aron Kovacic daga Real Madrid, za a bayyana Courtois a Real
  3. Wane dan wasan kulob dinka zai saya a kurarren lokaci?

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

Sai an jima

Jama'a, abin da ya samu ke nan a labaran kasuwar saye da musayar 'yan wasa ta Ingila a wannan lokaci.

Leicester ta sayi wani dan wasa

Leicester ta tabbtar da cewar ta cimma yarjejeniya da SC Freiburg game da sayen dan wasan baya Caglar Soyuncu.

Caglar Soyuncu.
Getty Images
Caglar Soyuncu

Fulham za ta sayi dan wasan Kamaru

Yaushe
Getty Images
Andre-Frank Anguissa

Fulham ta shirya domin sayen dan wasan tsakiyar Marseille, Andre-Frank Anguissa akan wata yarjejeniyar fan miliyan 22.3 bayan ta sayi dan wasan bayan Bristol City Joe Bryan kan kudi fan miliyan 6 da kuma golan Sevilla Sergio Rico wanda ta dauki bashinsa.

Dan wasan Kamaru Anguissa, mai shekara 22, ya buga wasan karshe na gasar Europa a watan Mayu inda Marseille ta sha kaye a hannun Atletico Madrid.

Fulham ta sayi Bryan

Rahotanni na cewa Joe Bryan ya so ya koma Aston Villa jiya har zuwa lokacin da Fulham ta shigo cikin cinikin.

View more on twitter

Stoke ta sayi Lucas

A daya daga cikin yarjejeniyoyin da aka yi ta kokarin kullawa tun da safe Stoke ta sayi Sam Clucas.

Sam Clucas
Getty Images
Sam Clucas

Swansea ta sayi dan wasa

Swansea ta sayi tsohon dan wasan bayan Cardiff Declan John.

View more on twitter

Everton ta kara wani dan wasa

Andre Gomes, wanda ya koma Barcelona daga Valencia shekara biyu da suka wuce - ya koma Everton buga wasan aro.

Sun sami 'yan wasa uku kenan cikin minti 10.

Andre Gomes
Getty Images

Brighton ta sayi dan wasa Wigan

Brighton ta sayi dan wasan bayan Wigan Dan Burn.

Dan wasan mai shekara 26 ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara hudu da Albion, amma zai cigaba da kasancewa da Wigan zuwa lokacin da za a bude kasuwar musayar 'yan wasa a watan Janairu.

Dan Burn
Getty Images
Dan Burn

West Ham ta sayi ..

West Ham ta sayi Carlos Sanchez.

View more on twitter

Huddersfield ta kulla yarjejeniya

Dan kasar Beligium, Isaac Mbenza, zai koma buga wasan aro a Huddersfield daga gasar Ligue 1 ta Faransa.

View more on twitter

An rufe kasuwar!

An rufe kasuwar musayar 'yan wasa na yarjejeniyar din-din-din. 'Yan wasa za su iya zuwa kungiyoyin EFL buga wasan aro..

rufewa
Getty Images

Labari daga Huddersfield

Muna saurar labari daga Huddersfiled duk da cewa lokaci ya yi

View more on twitter

Everton ta kara sayen wani dan wasa

Barcelona confirm ta tabbatar cewar Everton ta sayi dan wasan bayan Colombiya, Yerry Mina kan kudi yuro miliyan 30.

Yerry Mina
Getty Images
Yerry Mina

Saura minti 10

Saura minti 10 . Ina kake, Jordan Ayew? Ina Sam Clucas? Ina Carlos Sanchez?

Everton ta sayi Bernard

An kammala yarjejeniyar komawar dan wasan Brazil Bernard Everton. An taba alakanta dan wasan da manyan kungiyoyi kuma ya buga wa Brazil gasar kofin duniya ta 2014.

View more on twitter

Saura kasa minti 15

Saura kasa da minti 15 a rufe kasuwar musayar 'yan wasa. A halin yanzu muna tsammanin wasu labarai daga Everton da Fulham....

Dan wasan bayan Chelsea ya tafi

Bristol City ta sayi dan wasan bayan Chelsea, Jay DaSilva. Wane irin tasiri tafiyarsa za ta yi?

View more on twitter

Man City za ta ba da aron sabon dan wasa?

Kocin Celtic Brendan Rodgers na ganin dan wasan Australiya Daniel Arzani zai koma kulob din buga wasan aro. Dan wasan mai shekara 19 ya kammala yarjejeniyar komawarsa Manchester City daga Melbourne City da safiyar yau.

Amma ana ganin za a bayar da shi aro ga zakarun Skotland.

Daniel Arzani
Reuters

An kulla yarjejeniyar!

Bari mu fara sa'ar karshe ta kasuwar musayar 'yan wasa - Michael Hefele ya koma Forest.

View more on twitter

Yarjejeniyar da aka kulla..

An dai kammala wannan yarjejeniyar a yau.

View more on twitter

Leicester na son dan wasan Chlesea

Danny Drinkwater
Getty Images
Danny Drinkwater

Leicester tana tunanin sake sayen dan wasan tsakiyar Ingila Danny Drinkwater daga Chelsea, shekara daya bayan ta sayar wa Chlesea dan wasa mai shekara 28 kan kudi fan miliyan 35, in ji Independent.

Kasa da sa'a biyu!

A halin yanzu dai saura kasa da sa'o'i biyu a rufe kasuwar musayar 'yan wasa.

agogo
Getty Images

'Ba na tunanin farashi'

Sabon gola Chelsea Kepa yana jawabi ga wani tarob manema labarai a yanzu haka.

Ya ce: "Ina matukar murna da kasancewana a nan.Wani babban kalubale ne gare ni kuma wani babba abu ne gare ni. Wani babban cigaba ne a wasan kwallon kafana

"Game da farashi (yarjejeniya) na, abu ne wanda ba na tunani akai. Kawai zan yi kokarin ci gaba da kasancewa yadda nake kuma in yi iya kokarina."

Kepa
EPA
Kepa

Shin dan wasan Liverpool zai koma Newcastle?

A kasar Estoniya ana rade-radin cewar Rafa Benitez da Newcastle suna neman dan wasan kasar da ya suna a kasar waje.

Shin da gaske Liverpool za ta sayar da Ragnar Klavan?

Ragnar Klavan
Getty Images
Ragnar Klavan

Courtois ya koma Madrid kan yarjejeniyar...

Courtois
EPA

Ya tabbata cewar Thibaut Courtois ya koma Real Madrid kan yarjejeniyar shekara shida, lamarin da ya kawo karshen zamansa na shekara bakwai a Chelsea.

Dan kasar Belgium din bayan Chelsea ta tabbatar da cewar dan wasan tsakiyar Real Madrid Mateo Kovacic ya koma buga wasan aro a kulob din.

Dan wasan da Man City ta rasa..

Jerome Boateng
Getty Images

Dan wasan da Manchester City ta Rasa Boateng ya yarda ya koma kungiyar kwallon kafar Paris St-Germain,yayin da Bayern Munich ta shirya sayar da shi kan kudi fan miliyan 40.5, in ji Le Parisien.

Courtois yayin da ake gabatar da shi ga manema labarai

Man City ta kasa sayen dan Bayern

Manchester United ta kasa sayen dan wasan Bayern Munich mai shekara 29 Jerome Boateng domin suna ya buga musu wasan aro ne kawai, in ji Sun.

Jerome Boateng
Getty Images

An rattaba hannu

Domin kada a yi shakka game da sayen sabon gola, Real ta wallafa bidiyo a shafin Twitter inda Courtois yake rattaba hannu kan yarjejeniyar komawarsa Madrid....

View more on twitter

Sai dai kuma....

Sai dai kuma Leicester ta hakikance akan cewar ba za ta sayar da Maguire ga Manchester United ba, in ji Daily Mail.

Maguire
Getty Images

Maguire na da kwarin gwiwar komawa Man U

Har yanzu dan wasan bayan Leicester dan Ingila Harry Maguire, yana da kwarin gwiwar komawa Manchester United, duk da cewa an yi fatali da tyi biyun da kulob din ya yi wa dan wasanmai shekara 25, in ji Sky Sports

Harry Maguire
Getty Images

Courtois ya kusa zama dan Madrid

Gola Thibaut Courtois ya kusa zama dan wasan Real Madrid.

Real ta nuna hoton gwaje-gwajen da ake yi wa dan wasan...

View more on twitter

Saura sa'o'i biyar

A halin yanzu dai saura sa'o'i biyar a rufe kasuwar musayar 'yan wasa a gasar Firimiyar Ingila.

Me kake ganin kulob dinka za samu kafin a rufe kasuwar?

Man City ta sayi Daniel Arzani

Manchester City ta sayi dan wasan tsakiyar Australiya Daniel Arzani daga Melbourne City.

Dan wasan mai shekara 19 asalinsa Iran ne.

Arzani became the youngest player to make a World Cup appearance for Australia in Russia this summer
Getty Images
Arzani ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya fara buga wa Australiya wasa a gasar kofin duniya a Rasha

West Ham ta sayi dan wasan Arsenal

Perez scored seven goals during his two seasons at Arsenal
Getty Images
Perez ya ci kwallo bakwai a kaka biyun da ya yi da Arsenal

West Ham ta sayi dan kasar Sfaniya daga Arsenal kan kudi fan miliyan 4.

Dan wasan mai shekara 29 ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara uku da Hammers, bayan ya shafe shekara biyu da Gunners.

Chelsea ta sayi golan Atletic Bilbao

Chelsea tsa yi Kepa Arrizabalaga daga Athletic Bilbao kan kudi fan miliyan 71 - kudi mafi yawa da aka taba kashewa wajen sayen gola, kuma kudi mafi yawa da kulob din ya taba kashewa.

Kepa, mai shekara 23, zai isa Stamford Bridge bayan an cimma sharadin fansa cikin yarjejeniyarsa .

Kepa has made one appearance for Spain
Getty Images
Kepa ya buga wa Sfaniya wasa daya

Mounrinho ba shi da kwarin gwiwar sayen dan wasa

Mourinho
Getty Images
Mourinho

Kocin Manchester United, Jose Mourinho, ya ce shi ba shi da kwarin gwiwar sayen wani dan wasa kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa ranar Alhamis.

Mourinho ya dade yana jaddada cewar yana son ya kara 'yan wasa gabannin kakar bana inda ya fi mayar da hankali kan sayen dan wasan baya na tsakiya.

Chelsea ta dauki aron Kovacic

Mateo Kovacic ya buga wa Croatia wasanni  biyar a gasar kofin duniya a Russia
Getty Images
Mateo Kovacic ya buga wa Croatia wasanni biyar a gasar kofin duniya a Russia

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta dauki aron Mateo Kovacic na tsawon shekara daya daga Real Madrid, yayin da ake tsammanin komawar gola Thibaut Courtois Marid zai tabbata ranar Alhamis.

Dan wasan tsakiya, Kovacic, mai shekara 24, ya kasance a Real tsawon shekara uku tun da ya koma kulob din daga Inter Milan.

Leicester ta sayi Benković

.
Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Leicester ta sayi dan wasan baya Filip Benković daga Dinamo Zagreb.

Dan wasan mai shekara 21 wanda ya koma kungiyar kan wani kudin da a bayyana ba, ya kulla yarjejeniyar shekara biyar da kulob din.