Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Wannan karawa ce ta 53 a Premier, United ta ci 24, Arsenal 13 da canjaras 15
 2. Arsenal tana ta 4 a kan teburi da maki 30, United tana ta 7 da maki 22
 3. Arsenal ta yi wasa 19 a jere ba a doke ta ba har da 12 a Premier
 4. A bara United ce ta ci Arsenal 3-1 a Emirates da 2-1 a Old Trafford

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

Bayyana ra'ayinka

 1. Post update

  Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku tara nan gaba, Sunana Mohammed Abdu.

 2. Mourinho ya ce da kyar United ta yi ta hudu

  Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce burin da ya dauka na zama cikin kungiyoyin hudun farko a gasar Premier a karshen Disamba ya sauya.

  Mourinho ya yi fatan ne kafin karawar da United ta tashi babu ci da Crystal Palace a ranar 24 ga watan Nuwamba.

  Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin

  Kai tsaye
 3. Bayan da aka buga wasan mako na 15

  Manchester City tana nan a matakinta na daya, sai Liverpool ta biyu, Tottenham ta koma ta uku, Chelsea ta hudu sai Arsenal data koma ta biyar, United ta yi kasa zuwa mataki na takwas, bayan da take na bakwai a baya.

  Kai tsaye
 4. Sakamakon wasu wasannin mako na 15 da aka yi

  Kai tsaye
 5. Manchester United 2-2 Arsenal

  An tashi wasa Manchester United 2-2 Arsenal, kuma karawar ta kayatar sun raba maki a tsakaninsu.

 6. Manchester United 2-2 Arsenal

  An kusan tashi 'yan United sun koma tsare gida.

 7. Manchester United 2-2 Arsenal

  Arsenal ta ci kwallo amma alkalin wasa ya ce Mikhtariyan ya yi satar gida, kuma shi ne ya jefa a raga.

 8. Manchester United 2-2 Arsenal

  Arsenal ta samu damar cin kwallo ta hannun Aubemeyang ya buga sai dai golan United David De Gea ya hana ta shiga raga.

 9. Manchester United 2-2 Arsenal

  Arsenal ta kai kora mai zafi da ya kamata ta ci kwallo amma Mihktariyan ya barar.

 10. Manchester United 2-2 Arsenal

  Wasa ya dauki zafi inda Arsenal ta ci kwallo na biyu nan da nan United ta farke wasa ya koma 2-2.

  Kai tsaye
  Kai tsaye
 11. Manchester United 1-1 Arsenal

  Arsenal ta sauya dan kwallon Nigeria, Alex Iwobi ta saka Lacazette ya canje shi.

 12. Manchester United 1-1 Arsenal

  United ta sauya Anthony Martila wanda ya ci mata kwallo ta kuma sa Romelu Lukaku a madadin sa.

 13. Wolves 2-1 Chelsea

  Matashin dan kwallon Wolves, Morgan Gibbs-White ya fita ana ta yi masa tafi saboda kokarin da ya yi, in da dan wasan tawagar Portugal, Helder Costa ya canje shi..

 14. Burnley 1-2 Liverpool

  Roberto Firmino

  Liverpool ta kara kwallo na biyu ta hannun Roberto Firmino, tun farko Liverpool ba a doke ta ba a Premier bana, kuma tana ta biyu biye da Manchester City.

  Kai tsaye
 15. Spurs 3-0 Southampton

  Son Heung-min

  To ko sai an dawo da Mark Hughes ne daga barinsa an fara cin kungiyar kwallo uku rigis, koda yake da Tottenham ta hadu.

 16. Wolves 2-1 Chelsea

  Chelsea ta yi canji biyu a jere bayan da aka kara mata kwallo na biyu, inda Olivier Giroud da Pedro suka canji Willian da kuma Alvaro Morata.

 17. Spurs 2-0 Southampton

  Lucas Moura

  Tottenham ta kara kwallo na biyu ta hannun Lucas Moura, bayan da Harry Kane ya ci na farko tun kan a je hutu.

 18. Burnley 1-1 Liverpool

  James Milner

  Liverpool ta farke kwallo ta hannun James Milner bayan da Origi ya ba shi ita shi kuma ya saka a ragar Burnley.

 19. GOAL - Wolves 2-1 Chelsea

  Diogo Jota

  Diogo Jota ya samu dama ya yi amfani da ita inda ya buga kwallo ta tsakanin kafar golan Chelsea ta kuma fada raga.

 20. Wolves 1-1 Chelsea

  Raul Jimenez

  Arsenal ce ta fara cin kwallo ta hannun Mustafi minti 26 da fara wasa, inda United ta farke ta hannun Martial minti hudu tsakani. Wolves ta farke kwallon da Chelsea ta zura mata. Morgan Gibbs-White ne ya guga kwallon ta je wajen Raul Jimenez, shi kuma ya kara ta a raga.