Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Za a rufe kasuwar a Ingila da misalin karfe 12 na dare, a Scotland za arufe ta karfe daya na dare
 2. Barcelona ta dauki 'yar wasan Najeriya Asisat Oshoala da kuma 'sabon Dani Alves'
 3. Peter Crouch ya dawo gasar Firimiya

Rahoto kai-tsaye

time_stated_uk

 1. Karshe!

  Mun kawo karshen labarai da bayanai kai-tsaye game da kasuwar saye da musayar 'yan wasa ta nahiyar Turai. Mun gode.

 2. Babbar haja a yau

  Miguel Amiron

  Cinikin da Newcastle ta yi na sayan Miguel Almiron shi ne mafi girma a yau Alhamis.

  An saye shi ne a kan fam miliyan 20.

  'Yan wasa 9 ne kawai aka yi ciniki a yau a gasar Firimiya.

 3. Everton ta bayar da Evans aro

  Anthony Evans

  Dan wasan tsakiya na Everton Antony Evans ya koma kulob din Blackpool a matsayin aro.

  Dan kwallon, mai shkara 20, zai ci gaba da wasa ne a matsayin aron har zuwa karshen kakar bana.

 4. Kagawa na shirin koma wa Turkiyya

  Rahotanni sun ce tsohon dan wasan Manchester United Shinji Kagawa na yunkurin barin gasar Bundesliga.

  Dan wasan zai koma kungiyar Beşiktaş ta kasar Turkiyya da taka leda a matsayin aro har zuwa karshen kakar bana.

  View more on twitter
 5. Chelsea ta ba da aron Lucas Piazon

  Dan wasan gaban Chelsea Lucas Piazon, mai shekara 25, ya koma gasar Serie A a matsayin aro, inda zai rika taka leda a kungiyar Chievo har zuwa karshen kakar bana.

  A
 6. Tielemans ya koma Leicester daga Monaco

  A

  Kungiyar Leicester City ta tabbatar karbar dan wasan Monaco Youri Tielemans a matsayin aro.

  Dan Belgium din mai shekara 21 ya koma Monaco daga Anderlecht a shekarar 2017.

  Sai dai ita ma Monaco ta dauki dan wasan Leicester Adrien Silva a matsayin aro, a wani bangare na yarjejeniyar musayar Tielemans.

 7. Crouch ya dawo gasar Firimiya

  Peter Crouch
  Image caption: Crouch yana cikin 'yan wasa kalilan da suka zura kwallaye 100 a gasar Firimiyar Ingila

  Peter Crouch ya koma gasar Firimiya daga Stoke City mai buga gasar Championship, dan wasan mai shekara 38, yanzu zai rika taka leda a kungiyar Burnley.

  View more on twitter
 8. Barcelona ta dauki sabon 'Dani Alves'

  Emerson

  Barcelona ta dauki dan wasan baya mai suna Emerson daga Atletico Mineiro.

  A yarjejeniyar da aka cimma dan wasan ba zai koma Barcelona ba har sai karshen kakar bana.

  Barcelona ta ce "dan baya ne mai buga bangaren dama, kuma yana da karfin dada kwallo kamar gaya-wa-jini-na-wuce irin na Dani Alves."

 9. Asisat Oshoala ta koma Barcelona

  'Yar wasan Najeriya Asisat Oshoala ta koma kungiyar Barcelona ta mata daga kungiyar Dalian ta kasar China.

  Asisat Oshoala
  Asisat Oshoala
 10. Arsenal ta bayar da aron dan wasa

  Arsenal ta bayar da aron dan wasanta Emile Smith-Rowe ga kunhgiyar RB Leipzig zuwa karshen kakar bana.

  Dan wasan da ke buga wa karamar kungiyar Arsenal wasa ya zura kwallaye a gasar Europa ta bana.

  View more on twitter
 11. Leicester 'tana gab da samun' sabon koci

  Kungiyar Leicester City tana gab da sayo sabon koci Youri Tielemans daga Monaco, akwai wani labarin da ke cewa har ma ya fara yin atisaye da kungiyar da yammacin yau.

  View more on twitter
 12. Ina so na kara cin kwallaye – Martial

  Anthony Martial

  Dan wasan Manchester United Anthony Martial ya ce: "Ina fatan kara cin kwallaye da kofuna saboda abin da ya sa na zo nan ke nan."

  Ya bayyana hakan ne bayan da ya sabun ta yarjejeniyarsa da United a ranar Alhamis.

  "Da irin 'yan wasan da muke da su yanzu da nan gaba, ina ganin za mu cimma nasarori," in ji shi.

 13. Kamara ya koma Turkiyya

  Dan wasan Fulham Aboubakar Kamara ya koma kungiyar Yeni Malatyaspor wanda take kasar Turkiyya a matsayin aro har zuwa karshen kakar bana.

  Kamara
  Image caption: A
 14. Newcastle ta kafa tarihi

  Miguel Almiron
  Image caption: Miguel ne dan wasa mafi tsada da New Castle ta saya bayan Michael Owen

  Kungiyar Newcastle ta kafa tarihi, inda ta biya tsabar kudi fam miliyan 20 don daukar Miguel Almiron daga kungiyar Atlanta.

  Wannan ya shafe fam miliyan 16 da kulob din ya biya Real Madrid kan dan wasa Michael Owen a shekarar 2005.

  Dan wasan gaban mai zura kwallo a raga kuma dan shekara 24 ya ci kwallaye 13, inda ya taimaka wa Atlanta lashe kofin MLS a karon farko a kakar bara.

  Ya zura kwallaye 21 a gaba dayan wasanni 62 da ya buga.

  Dan wasan ya shaida wa manema labarai cewa ya ji dadin zuwansa kulob din kuma zai yi bakin kokarinsa don ganin ya taimaka masa."

 15. Georges-Kevin Nkoudou ya koma Monaco

  Dan wasan Tottenham Georges-Kevin Nkoudou ya koma Monaco a matsayin aro har zuwa karshen kaka.

  Nkoudou ya koma Tottenham daga Marseille a watan Agustan shekarar 2016 a kan fam miliyan tara.

  Kuma ya ci kwallo guda a wasanni 26,inda ya yi wasa uku kacal a kakar bana.

  Georges-Kevin Nkoudou
 16. 'A karshen lokaci aka fi yi sayen manyan 'yan wasa'

  Shugaban hukumar kwallon kafa ta jihar Kano, Sharu Rabi'u Inuwa (Ahlan), ya ce a karshen lokaci aka fi sayen manyan 'yan wasa a wannan rana ta rufe kasuwar saye da musayar 'yan wasan kwallon kafar Nahiyar Turai.

  Video content

  Video caption: Sharu Rabi'u Inuwa
 17. Martial ya sabunta kwantiraginsa a United

  Anthony Martial
  Image caption: Martial na cikin manyan 'yan wasa

  Dan wasan gaba na Manchester United Anthony Martial ya tsawaita yarjejeniyar zamansa a Old Trafford.

  Dan wasan zai ci gaba da zama har zuwa watan Yuni na shekarar 2024 tare da zabin kara tsawaita yarjejeniyar na tsawon shekara guda.

  Martial ya buga wasanni 162 ya kuma zura kwallaye 46 a raga tun sa'adda ya fara yi wa United wasa a 2015.

  "Muna farin ciki Anthony ya tsawaita zamansa domin kuwa nan ne kulob mafi dacewa da shi a matsayinsa na babban dan wasa mai zura kwallo a raga", in ji kocin United Ole Gunnar Solskjae.

 18. Da gaske ne Madrid na neman Rashford ?

  Jaridar The Sun ta ce Real Madrid tana neman Marcus Rashford a kan fam miliyan 100, kafin ya sabunta yarjejeniyarsa da Manchester United.

  Rashford