Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

Bayyana ra'ayinka

 1. Post update

  Nan muka kawo karshen shirin da fatan kun ji dadin kasancewa da mu.

  Sunnana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW nake cewa mu hadu a wani shirin nan gaba, sai an jimanku.

 2. Yadda teburi yake kawo yanzu

  Premier
 3. Sauran wasannin da za a buga ranar Asabar

  Premier
 4. Man City 1-0 Tottenham

  Wasa na 10 a jere da Manchester City ta ci a Premier League bana, babu kungiyar da ta yi wannan bajintar a kakar da ake buga wa.

 5. An tashi wasa - Manchester City 1-0 Tottenham

 6. Man City 1-0 Tottenham

  Leroy Sane ya kai kora an kuma bata kwallo, shi kuwa Lucas Moura ya fadi kasa bayan da Manchester City suka tare shi, Raheem Sterling ya tsaya daf da kwallo bai bari an biga da wuri ba.

 7. Canji - Man City 1-0 Tottenham

  Phil Foden ya fita David Silva ya canje shi.

  Kuma tun kwallon da dan wasan mai shekara 18 da ya ci ba a kara zura wata ba.

  Premier
 8. Man City 1-0 Tottenham

  Raheem Sterling da kuma Paulo Gazzaniga suna mayar wa da juna magana, bayan da dan wasa City ya yi

 9. Man City 1-0 Tottenham

  Danny Rose ne ya kai wa Bernardo Silva matsi, amma bai kwace kwallo ba.

  pREMIER
 10. Canji - Man City 1-0 Tottenham

  Fernando Llorente ya shiga fili ya canji Toby Alderweireld.

  Magoya bayan Manchester City ba za su manta da dan kwallon ba a karawar da suka yi ranar Laraba a gasar Zakarun Turai.

 11. Man City 1-0 Tottenham

  Fernando Llorente - na motsa jiki zai shigar wa Tottenham wasa.

 12. Man City 1-0 Tottenham

  Manchester City ta dan yi barci.

  Lucas Moura ne ya samu kwallo ya wuce 'yan baya ya buga amma mai tsaron ragar City dan Brazil, Ederson ya hana ta shiga raga.

  Premier
 13. Man City 1-0 Tottenham

  Raheem Sterling ya samu dama mai kyau da zai kara kwallo na biyu amma hakan bai yi wu ba.

  Premier
 14. Canji - Man City 1-0 Tottenham

  Tottenam ta cire dan wasan tsakiya Dele Ali ta saka mai tsaron baya, Danny Rose.

 15. Man City 1-0 Tottenham

  Son Heung-min na korafin fenariti bayan da ya yi kokarin jan kwallo sai ya yi zargin ta taba hannun mai tsaron bayan Man City.

 16. Canji - Man City 1-0 Tottenham

  Manchester City ta sauya Sergio Aguero ta saka Leroy Sane.

  Aguero ya ci kwallo 19 a bana saura kwallo daya ya ci ta 20 jumulla, kuma karo biyar yana cin 20 a kaka a jere. Zai yi kankankan da Thiery Henry.

  Premier
 17. Canji - Man City 1-0 Tottenham

  Eric Dier, ya fita Tottenham ta saka Victor Wanyama.

 18. Neman fenariti - Man City 1-0 Tottenham

  Magoya bayan City sai kuwa suke yi kan yadda wasan ke tafiya da yake sun ci kwallo daya.

  Toby Alderweireld ne ya cillo kwallo sama zuwa wajen Dele Alli, shi kuwa mai tsaron baya Kyle Walker ya yi kokari ta bugio jikinsa.

  Dele Ali ya nuna cewar ta taba hannun Walker amma alkalin wasa ya ce ko kusa, saboda haka ba sai an je VAR ba.

 19. Man City 1-0 Tottenham

  'Yan wasan Tottenham Ben Davies da kuma Eric Dier sun rufarwa Bernardo Silva amma sun kasa tare shi.

 20. Man City 1-0 Tottenham

  Phil Foden ya shiga da'irar ragar Tottenham da kwallo, ammam Foyth ya sa masa matsi bai amfana da ita ba.