Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. 'Yan wasan gaba Salah da Firminho ba za su buga wa Liverpool ba
 2. Barcelona ta ci Liverpoool kwallo 3-0 a Camp Nou
 3. Liverpool na bukatar ta ci Barcelona 4-0 don samun kai wa wasan karshe
 4. Sau biyar kowanne daga cikin kungiyoyin biyu suka taba lashe kofin gasar

Rahoto kai-tsaye

time_stated_uk

 1. Kocin Barcelona

  Liverpool 4 - 0 Barcelona

  Kocin Barcelona Ernesto Valverde ya ce "Ni ban san ta yadda wannan wasan zai shafi aikina ba, amma dole koci ya dauki alhalkin duk abin da ya faru.

  "Abin takaici ne a wurinmu, karo na biyu kenan da haka take faruwa da su".

 2. Sergio Busquets ya nemi afuwa

  Liverpool 4 - 0 Barcelona

  dan wasan tsakiyar Barcelona Sergio Busquets ya nemi afuwar magoya bayansu.

  Ya ce: "Bayan abin da ya faru a Rome shekarar da ta gabata ta kuma faruwa. Abu ne mawuyaci a cinye ka bayan kana da nasarar 3-0. Muna bayar da hakuri."

 3. Rio Ferdinand ya ce

  Liverpool 4 - 0 Barcelona

  Rio Ferdinand ya ce ba za ka taba samun irin wannan ba sai a kwallon kafa.

  Ya ce: "Ni dan wasan kungiyar adawa ne amma wajibi ne ka jinjina wa Liverpool da magoya bayansu a wannnan dare. Mun zo kallon Messi ne don ya yi nasara".

 4. Ta leko ta koma wa Barcelona

  Liverpool 4 - 0 Barcelona

  Liverpool ta kai wasan karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai na Champions League, bayan da ta yi nasara a kan Barcelona 4-0 ranar Talata a Anfield.

  Liverpool ta ci kwallaye biyu ta hannun Divock Origi, sannan shima Georginio Wijnaldum ya ci biyu a karawar.

  Barcelona ce ta ci 3-0 a makon jiya a Nou Camp, amma Liverpool ta zare su sannan ta kara daya a raga, inda ta kai wasan karshe da kwallo 4-3.

  Liverpool tana ta biyu a teburin Premier, za ta buga wasan karshe da Wolverhampton ranar Lahadi.

  Barcelona
 5. Liverpool kai wasan karshe

  Liverpool 4-0 Barcelona

  Wayyo Allahna!!!!

  Wannan wane irin dare ne. Duniyar kwallon kafa na cikin wani yanayi na karya tarihi.

  Stats
 6. Liverpool

  Liverpool 4-0 Barcelona

  Liverpool na kan hanyarsu ta zuwa wasan karshe a karo na biyu a jere

  Liverpool
 7. An kara minti biyar

  Liverpool 4-0 Barcelona

  Alkalin wasa ya kara minti biyar kafin a tashi wasan. Idan aka tashi wasan a haka Liverpool ta yi nasara ke nan.

 8. Canji

  Liverpool 4-0 Barcelona

  Daniel Sturidge ya shigo cikin fili, inda ya canji Shaqiri a minti na 90

 9. Barcelona sun matsa kora

  Liverpool 4-0 Barcelona

  Barcelona sun matsa kora, amma masu tsaron bayan Liverpool sun kare gidansu.

 10. Van Dijk

  Liverpool 4-0 Barcelona

  Van Dijk ya tare kwallo mai hadari a cikin yadi na 18 dinsu

 11. Saura minti hudu a tashi wasa

  Liverpool 4-0 Barcelona

 12. Canji

  Liverpool 4-0 Barcelona

  Gomez ya karbi Origi

  Wannan wani salo ne daga Klopp don tabbatar da nasarar da suke da ita a yanzu.

  Gomez dan wasan baya ne kuma ya canji na gaba, wanda shi ne ma ya ci kwallo 2 daga ciki

 13. Origi

  Liverpool 4-0 Barcelona

  Origi ya fadi a tsakiyar fili yana karbar kulkawa.

  Saura minti 6 a tashi daga wasa.

 14. Goooo! Origiiiiiiiiiiiii

  Origi ya cilla kwallo ta 4 a ragar Barcelona.

  Dama taken Liverpool shi ne "ba za mu bar ka kai kadai ba"

 15. Post update

  Liverpool 3-0 Barcelona

  An bai wa Samedo katin gargadi

 16. Post update

  Liverpool 3-0 Barcelona

  Arthur ya canji Vidal a minti na 74.

  Vidal ya yi kokari sosai ganin yadda ya rika kaiwa da komowa a tsakiyar fili.

 17. Post update

  Liverpool 3-0 Barcelona

  Minti 73, kuma komai na tafiya yadda Liverpool ke bukatarsa.

 18. Liverpool

  Liverpool 3-0 Barcelona

  Liverpool na kokarin zama kungiya ta 3 da ta ci wasa bayan an ci ta 3-0 a wasan farko a matakin kusa da karshe a gasar Zakarun Turai ta Chamapions Leahgue da kum Europa.

  Muna jiran ganin karshen wannan dare mai cike da tarihi