Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Ajax ta ci wasan farko da ci 1-0 a Landan
 2. Harry Kane ba zai buga karawar ba
 3. Tottenham tana ta uku a teburin Premier
 4. Duk wanda ya lashe wasan zai hadu da Liverpool a wasan karshe a Madrid
 5. Son Heung-min zai taka leda

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Rayyan da Umar Mikail

time_stated_uk

Bayyana ra'ayinka

 1. Karshe!

  Ajax 2-3 Tottenham

  Kafin 1 ga watan Yunin, a nan muke maku ban kwana.

  Umar Mikail ne da Umar Rayyan ke ce muku sai da safe.

 2. Ajax 2-3 Tottenham

  Yanzu za mu jira zuwa ranar Asabar 1 ga watan Yuni mai zuwa domin buga wasan karshe a birnin Madrid na kasar Spaniya a filin wasa na Wander Metropolitano.

  Za a buga wasan ne tsakanin Liverpool da kuma Tottenham, wadanda dukansu kungiyoyin Ingila ne kuma rabon da a yi hakan tun shekarar 2008, inda Man United ta cinye kofin a bugun finareti.

  Liverpool da Tottenham
 3. Ajax

  Ajax 2-3 Tottenham

  Wannan matashiyatr kungiyar ta Ajax ta ga samu ta ga rashia lokaci guda.

  Abin da ya faru ya yi kama da wanda ya tsakanin Tottenham din da Man City a wannan gasa ta Champions League ta bana.

  Wadannan matasan 'yan wasa suna da damar ci gaba da neman cin kofuna a gaba domin kuwa matasa ne wadanda za su debi shekaru nan gaba sun amurza leda.

  Ajax
 4. Mauricio Pochettino

  Ajax 2-3 Tottenham

  Mauricio Pochettino kocin Tottenham ya barke da hawayen murna. Ba mu ga laifinsa ba domin bai taba jagorantar wata kungiya ba da ta kai kusa da wannan mataki a babbar gasa kamar wannan.

  Mauricio Pochettino
 5. Tottenham

  Ajax 2-3 Tottenham

  Lucas Moura ya kai Tottenham wasan karshe a Champions League a karon farko.

  Moura
 6. Yadda wasan ya kasance

  Ajax 2-3 Tottenham

  A
 7. GOooooooooooooooooooo

  Ajax 2-3 Tottenham

  Lucas Moura ya ci kwallo ta 3 a daren yau

 8. Post update

  Ajax 2-2 Tottenham

  Muna cikin mintuna 5 na karshe da aka kara.

  Waye ne zai fito wasan karshe?

 9. AAA! OOohhh

  Ajax 2-2 Tottenham

  Saura kiris Ajax su kara kwallo. Ba don Vertonghen ba da ya yi siulu ya jefa ta waje da tuni wasa ya zama 3-2

 10. Post update

  Ajax 2-2 Tottenham

  Magalan ya shigo, inda ya canji Van de veek a minti na 88

 11. Lalalalala

  Ajax 2-2 Tottenham

  Ajax na ganin tashin hankali fa a mintunan karshen nan.

  Hare-hare biyu munana aka kai masu a minti daya. Lucas Moura ya kusa karawa bayan da ya buga ta da kansa, inda Onana ya ciro ta da kyar.

  Son ya kuma jan kwallon cikin yadi na 18 sai dai ya buga ta saman raga.

 12. Post update

  Ajax 2-2 Tottenham

  Wasa ya kacame. Davies ya buge Ziyech a tsakiyar fili. 'Yan Tottenham suna korafin babu abin da aka yi masa ya fadi

  Ziyech
 13. Ziyech

  Ajax 2-2 Tottenham

  Ziyech ya narka kwallo gada-gadan zuwa ragar Lloris amma ta bugi turke.

  Da tuni 3-2 fa😲

 14. Katin gargadi

  Ajax 2-2 Tottenham

  An bai wa Ziyech katin gargadi a minti na 76

 15. Katin gargadi

  Ajax 2-2 Tottenham

  Danny Rose ya karbi katin gargadi a minti na 76

 16. Lucas Moura

  Ajax 2-2 Tottenham

  Kwallaye 3 da Lucas Moura ya ci gaba dayansu a waje ya ci ba a gida ba.

  To ko zai kara a wannan wasa? za mu gani dai.

  Minti 16 ne ya rage kawai

 17. Post update

  Ajax 2-2 Tottenham

  'Yan wasan Ajax har biyu a bakin ragar Lloris amma 'yan bayan Tottenham sun fitar da kwallon waje.

 18. Ajax 2-2 Tottenham

  Ajax 2-2 Tottenham

  Tottenham sun bude wuta a wannan wasa kuma da alama za su fita da wani abu daga filin wasa nan Johan Cruijff ArenA

  Kwallo daya kawai suke bukata yanzu don shiga wasan karshe

  false

 19. Ziyech

  Ajax 2-2 Tottenham

  Ziyech ya kai mummunan ga Lloris sai dai kwallo ta yi fadi kuma ta fita waje