Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

 1. An ba Chelsea fanariti

  Chelsea 2-0 Arsenal

 2. Chelsea ta fi taba kwallo

  Chelsea 2-0 Arsenal

  Tun da aka dawo hutun rabin lokaci Chelsea ke taba Arsenal, inda ta ci kwallaye biyu.

 3. Pedro ya kara wa Arsenal

  Chelsea 2-0 Arsenal

  Kwallo biyar kenan da Pedro ya ci a gasar Europa a bana

 4. Sarri na 'bankwana' da Chelsea

  Chelsea 0-0 Arsenal

  Wannan zai iya kasancewa wasa na karshe da Sarri ke jagorantar Chelsea bayan rahotanni sun ce zai koma Italiya domin horar da Juventus

  Sarri
 5. Yadda Giroud ya ci ragar Arsenal

  Chelsea 1-0 Arsenal

  Emerson ne ya kawo wa Giroud kwallon shi kuma ya ci da kai

  Chelsea
  Chelsea
 6. Giroud ya ci wa Chelsea

  Chelsea 1-0 Arsenal

  Giroud yanzu ya ci kwallaye 11 a gasar Europa a bana, kuma shi ne ya fi yawan cin kwallaye a gasar ta bana

  Giroud
 7. Yadda Petr Cech ya kabe kwallon Giroud

  Chelsea 0-0 Arsenal

  Arsenal
 8. An tafi hutun rabin lokaci

  Chelsea 0-0 Arsenal

 9. Ra'ayi

  Chelsea 0-0 Arsenal

  SMS Message: Arsenal za ta yi Kokarin ganin ta lashe wannan kofi ganin yadda ba ta cikin top 4 wanda za su buga gasar zakarun Turai na shekara Mai zuwa. A bangaren Chelsea kuwa Sarri zai yi kokarin lashe kofin domin samun kwarin gwiwar cigaba da horarwa a kungiyarsa. from Ibrahim Muhammad Bin Malam Alkaitaw
  Ibrahim Muhammad Bin Malam Alkaitaw
 10. Giroud ya kai hari

  Chelsea 0-0 Arsenal

  Amma Petr Cech ya kabe kwallon.

 11. Karancin 'yan kallo

  Chelsea 0-0 Arsenal

  Chelsea
  Chelsea
 12. Karo na biyu da kungiyoyi Ingila ke buga wasan karshe

  Chelsea 0-0 Arsenal

  Karo na biyu da kungiyoyi Ingila ke buga wasan karshe

  Karo na uku kenan da kungiyoyi daga kasa daya ke buga wasan karshe a gasar Turai.

  Karo na biyu kuma ke nan da kunguyoyin Ingila ke buga wasan karshe bayan Tottenham da Wolves da suka buga wasan karshe a UEFA Cup a 1972.

  Chelsea da Arsenal
 13. Chelsea ta fara matsawa Arsenal

  Chelsea 0-0 Arsenal

 14. Karancin magoya baya?

  Chelsea 0-0 Arsenal

  Ana buga wasan ne ba tare da dimbin magoya bayan Chelsea da Arsenal ba wadanda nisa ya hana su zuwa Baku domin kallon wasan.

  Rahotanni sun ce magoya bayan kungiyoyin 5,000 ne kawai suka samu zuwa kallon wasan a filin Baku mai daukar ‘yan kallo 70,000 a Azerbaijan.

  Arsenal da Chelsea
 15. Aubameyang ya barar da dama

  Chelsea 0-0 Arsenal

 16. Arsenal ta kai hari

  Chelsea 0-0 Arsenal

  Alexandre Lacazette ya yi kokarin kai wa Pierre-Emerick Aubameyang kwallo daga tsakiya amma bai same shi ba. Olivier Giroud ya samu bugun tazara.

 17. Wasan ban kwana ga Hazard

  Chelsea 0-0 Arsenal

  Wannan zai iya zama wasa na karshe da Hazard yake buga wa Chelsea inda ake jita-jitar cewa zai koma Real Madrid.

  Hazard