Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Shamsiyya Haruna

time_stated_uk

 1. Karshe!

  Crytsal Palace 0-2 Leicester City

  Everton 1-1 Tottenham

  Ba iya Premier Ingila kawai aka yi yau ba, Kano Plllars ta tashi 0-0 da Rivers United FC a gasar Firimiyar najeriya mako na farko.

  Kano Pillars 0-0 Rivers United

  Plateau United 3 - 1 Lobi Stars

  Abia Warriors 2 - 0 Katsina Utd

  Warri 1-1 Akwa United

  Heartland 0-1 MFM

  Wiki 2-1 Jigawa Golden Stars

  Nan muka kawo karshen rahotannin game da wasannin yau. Umar Mikail da Shamsiyya Haruna ke fatan mu kwana lafiya.

 2. Jan katin da aka bai wa Son

  Everton 1-1 Tottenham

  Hukumar Premier League ta ce:

  "An bai wa Son jan kati ne saboda ya jefa rayuwar dan wasa a hadari domin abin ya faru ne ta hanyar abin da ya aikata."

  An dai kori Son daga wasan ne a minti na 79 bayan ya yi wa Andre Gomes keta kuma da farko katin gargadi lafarin ya yi niyyar ba shi, amma sai aka sauya hukuncin zuwa katin kora.

  Gomes bai iya ci gaba da wasan ba saboda tsananin buguwa da ya yi bayan ya yi karo da Aurier. Shi kansa Aurier bai ji dadin abin da ya faru ba.

  Son
 3. Wasa ya kare

  Everton 1-1 Tottenham

  Tottenham ta ci gaba da fuskantar kalubale a kakar Premier ta bana bayan canjaras da ta yi da Everton 1-1 a wasan mako na 11.

  Everton ta nuna cewa a gidanta ake wasan domin kuwa ba ta bari an fi ta taka wata rawa ba kuma har zuwa karshensa tana kai kora.

  Ta farke kwallon da Dele Alli ya saka mata a raga ne ana saura minti biyar a tashi daga wasan bayan minti 12 da aka kara bayan shafe minti 90 - Cunk Tuson ne ya ci kwallon.

  Shi kuwa Dele Alli ya ci tasa kwallon ne tun a minti na 63. Kwallo ce mai kyan gaske inda sai da ya yanke mutum daya sannan ya ratsa bayan Everton kuma ya buga ta gefen hagu na ragar Jordan Pickford.

  An kori Son Heung-Min daga wasan bayan ya yi wa Andre Gomes keta, abin da yasa aka fitar da dan wasan a makara, kuma haka Spurs ta kare wasan da mutum 10 a cikin fili tun daga minti na 79.

  Sakamakon ya bar tottenham a mataki na 11 da maki 13, yayin da ita kuma Everton ta ci gaba a mataki na 17 kamar yadda ta fara wasan.

  Ericksen
  Image caption: Christian Ericksen
 4. GOAL Everton '97

  Everton 1-1 Tottenham

  Cenk Tosun ne ya ci kwallon da ka

 5. Ran Serge Aurier ya baci

  Everton 0-1 Tottenham

  Serge Aurier bai ji dadin abin da ya faru ba game da Andre Gomes kuma tuni Juan Foyth ya karbe shi.

 6. An kara minti 12

  Everton 0-1 Tottenham

  Minti 12 aka kara kan 90 da aka shafe. Minti 12? Eh saboda lokacin da aka bata wurin kula da Andre Gomes.

 7. Everton 0-1 Tottenham '85

  Ganin cewa yanzu Spurs za ta kammala waan da 'yan wasa 10, ko Everton za ta yi amfani da damar? Ma ji ma gani dai. Saura kasa da minti 5 a tashi

 8. An fitar da Gomes a makara

  Everton 0-1 Tottenham

  Andre Gomes ba zai iya ci gaba da wasan ba domin kuwa a makara aka fitar da shi daga filin wasan.

  Hatsari ne ya faru, inda Gomes din ya yi karo da kafafuwan Aurier bayan Son ya kayar da shi.

 9. Jan kati (RED CARD)

  Everton 0-1 Tottenham

  Alkalin wasa ya kori Son Heung-min na Tottenham bayan ya yi wa Andre Gomes keta.

 10. Canji

  Everton 0-1 Tottenham

  Tottenham ta sako Giovani Lo Celso a madadin Tanguy Ndombele.

  Everton kuwa sauya Theo Walcott ta yi da Cenk Tosun.

 11. Dele Alli ya kusa jawo finareti

  Everton 0-1 Tottenham

  Mintuna kadan bayan ya ci wa Tottenham, Dele Alli ya kusa jawo finareti.

  Ya taba kwallo da hannunsa a cikin gidansu amma dai VAR ta cece shi ta ce babu finareti - amma kuwa da ya sha suka jim kadan bayan yabo.

  Dele Alli
 12. Richarlison

  Everton 0-0 Tottenham

  Richarlison ya dada wa Gazzaniga wata kwallo mai hadarin gaske, amma golan Tottenham din bai bari ta shiga ba - tsalle ya yi da kyau ya ture tarew da kama ta.

 13. Babu finareti

  Everton 0-0 Tottenham

  An duba abin da ya faru a cikin yadi na 18 din Everton bayan Yerri Mina ya kayar da Son.

  Amma na'urar VAR ta ce babu finareti kuma wasa ya ci gaba.

 14. Everton 0-0 Tottenham

  Lucas Digne ya buga bugun tazara zuwa ragar Spurs amma 'yan baya sun yi aikinsu.

  Everton ta fara wannan zagayen da karfinta sama da Tottenham.

 15. Everton 0-0 Tottenham

  Everton 0-0 Tottenham

  An shiga falle na biyu na wasa amma har yanzu babu ci.

  Tottenham dai bana abubuwa ba sa yi mata kyau kuma yau ma idan ba ta yi da gaske ba za ta sha mamaki musamman ganin cewa ita ma Everton tana neman maki ko ta halin-kaka.

 16. Hutun rabin lokaci

  Everton 0-0 Tottenham

  An tafi hutun rabin lokaci ba tare da kowannensu ya zura kwallo a raga ba.

 17. Richarlison

  Everton 0-0 Tottenham

  Richarlison ya yi kokari sosai da ya yanka Davinson Sanchez a cikin yadi na 18, sai dai shot din da ya buga ya haura saman raga. Da alama dan kasar Brazil din zai iya kai Everton ga nasara.

 18. Firimiyar Najeriya

  Abia Warriors 2 - 0 Katsina Utd

  Abia Warriors ta casa Katsina United da ci 2-0

 19. Firimiyar Najeriya

  Plateau United 3 - 1 Lobi Stars

  Lobi Stars ta sha kashi a hannun Plateau United da 3-1