Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Buhari Muhammad Fagge

time_stated_uk

 1. Karshen sharhi

  Nan ne muka kawo karshen sharhin wasannin gasar Premier da suka gudana a yau Lahadi. Mu na godiya gare ku da kuka kasance tare da mu Umar Mikail da Buhari Muhammad Fagge ne ke cewa mu kwana lafiya.

 2. Jadawalin Premier

  Jadawalin Premier

  Jadawali
  Image caption: Jadawali
 3. Mun ci kwallo masu ban mamaki.

  Liverpool 3-1 Man City

  Kocin Liverpool Jurgen Klopp,ya tattauna da BBC Sport:"Suna da matukar kyau, dole mu kare bangarenmu ta yadda za mu iya, amma mun ci kwallo masu ban mamaki.

  "Akwai matukar wahala wasa da su, a zahiri yake yadda wasan ya yi zafi, kuma ya cancanci hakan, ba karamin abu bane, suna taba kwallon daga waje, Sterling. ta yaya muka rike shi? saboda kunga abin da ya faru lokacin da muka kasa rike shi.

  "Yaran sun nutsu sun kuma mai da hankali. abin farin ciki ne, wannan ce kawai hanyar da za mu iya cin ye City, wtakila a samu wasu kungiyoyin da za su iya hakan ta wata hanyar daban, amma mu daita wannan hanyar ce kawai za mu iya doke su.

  Yaya kake ganin kwallon farko? matsalar VAR ce, na ga yadda tattauanwar kafin kwallon farko, kuma na dan jira inga mai zai faru, aka ga ba matsala ba ce. Dole in yi murna a daren yau.

  "Duk wasan da muke da City wasa ne na kallo kamar wannan, amma banda wasanmu na gida na bara, saboda an fimu kokari, amma wannan ba shi ne wasan da ya fi kyau ba, amma ya yi kyau na ji dadin wasan."

  Jurgen Klopp
  Image caption: Jurgen Klopp
 4. Anfield shi ne filin wasan kwallon kafa mafi wahala a duniya.

  Liverpool 3-1 Man City

  A tattaunawarsa da BBC Sport kocin Manchester City ya ce" ina taya Liverpool murna, sun ci kwallo uku, mun ci daya amma ina alfahari da 'yan wasana, kalilan ne za su iya zuwa nan su yi abin da muka yi."

  "Mun fara wasan yadda ya kamata, mun kuma nuna kwarewa, sune zakarun Turai kuma filin wasansu shi ne mafi wahala a duniya, sun buga shot biyu sun kuma ci kwallo biyu.

  "Ba karamin abu bane bayan an ci ka kwallo biyu ka yi abin da muka yi, wannan na daya daga cikin wasan da yafi birge ni da yan wasana suka buga, wannan kuma shi ne muke bukata, kuma za mu ci gaba da hakan.

  Da aka tambaye shi kwallon farko da aka ci City sai ya ce, "kuje ku tambayi Mike Riley da mutanensa."

  Guardiola
  Image caption: Guardiola
 5. Liverpool ta lallasa City, ta yi dare-dare a teburi

  Liverpool 3-1 Man City

  Liverpool ta gwada wa Man City kwanji tare da tura ta matsayi na hudu a teburin Premier daga matsayi na biyu da take a baya.

  Maki 8 ne tsakanin Liverpool da kuma kungiyoyin Leicester City da Chelsea wadanda da ke a matsayi na biyu.

  Dan wasan tsakiya Fabinho ne ya fara jefa kwallo a minti na 6 da fara wasan, kafin daga baya Mohammed Salah ya ci tasa a minti na 13.

  Sadio Mane ne ya kara kwallo ta uku a minti na 51, wadda kuma ita ce kwallo ta 18 da ya ci a wasa 17 da ya buga a filin wasa na Anfield.

  Bernardo Silva ne ya farke kwallo daya da City ta iya jefawa a makare a watro minti na 78.

  Liverpool ce kungiya daya tilo da har yanzu ba a yi nasara a kanta ba a gasar Premier ta bana.

  Manchester City ce kawai ta ci Liverpool din a baya a gasar Premier kwana 311 da suka gabata.

  Fabinho
  Sadio Mane
  Tawagar Liverpool
  Tawagar Liverpool
 6. An tashi

  Liverpool 3-1 Man City

  Liverpool ta tabbata a saman teburi da maki 8 tsakanin ta Leicester da ke matsayi na biyu.

 7. Sadio Mane

  Liverpool 3-1 Man City

  Sadio Mane ya ci kwallo 18 a wasa 17 da ya buga a filin wasa na Anfield.

  Sadio Mane
  Image caption: Sadio Mane
 8. An kara minti 4

  Liverpool 3-1 Man City

  Ba karamar asara ba ce ga City idon aka tashi a haka.. kuma da alamar hakan ne zai faru

 9. Post update

  Liverpool 3-1 Man City

  Jurgen Klopp na neman tsira da kwallon da ya ci...

 10. Liverpool ta yi canji

  Liverpool 3-1 Man City

  Salah ya fita Gomez ya shiga.

 11. Liverpool 3-1 Man City

  Liverpool 3-1 Man City

  City ta mamaye kwallon tana neman kara farkewa cikin kasa da minti 5 kafin a tashi.

 12. Sterling da Guardiola

  Liverpool 3-1 Man City

  Sterling da Guardiola na korafin sun samu finareti biyu ba a basu ko daya ba.

 13. Ra'ayoinku daga Facebook

  Liverpool 3-1 Man City

  SMS Message: Hhhh, Musulmin Allah saura viyu ma from Haxxan Bin Yaqub
  Haxxan Bin Yaqub
  SMS Message: Kowa Liverpool takama sai yagane kurensa from Moh'd Kabir Gotel
  Moh'd Kabir Gotel
 14. Liverpool 3-1 Man City

  Liverpool 3-1 Man City

  City ta buda filin tana neman kara farke kwallo. Sterling ya kama da wuta.

 15. Liverpool ta yi canji

  Liverpool 3-1 Man City

  Roberto Firmino ya fita Alex Oxlade-Chamberlain ya shigo

 16. GOAL '77 Bernardo Silva

  Liverpool 3-1 Man City

  Bernardo Silva ya zare wa City kwallo daya cikin ukun da aka ci ta

 17. Liverpool 3-0 Man City

  Liverpool 3-0 Man City

  Kiris ya hana Mane ya ci gida.

 18. Man City ta yi canji

  Liverpool 3-0 Man City

  Agüero ya fita Gabriel Jesus ya shigo