Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mohammed Abdu

time_stated_uk

Bayyana ra'ayinka

 1. Post update

  To Jama'a nan na kawo karshen gabatar muku da shirin na labarin wasanni kai tsaye da fatan za ku tara a shirimnmu na gaba.

  Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW ke muku fatan alheri mu sake haduwa a shirin gaba.

 2. Karashen wasan mako na 28 a La Liga ranar Lahadi

  • Athletic Bilbao da Atletico Madrid
  • Real Madrid da SD Eibar
  • Real Sociedad da Osasuna
 3. Karashen wasan mako na 31 a Bundesliga ranar Lahadi

  • FSV Mainz 05 da FC Augsburg
  • Schalke 04 da Bayer 04 Leverkusen
 4. An tashi wasa Mallorca 0-4 Barcelona

  Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Liga bayan da ta samu maki uku a kan Real Mallorca.

  Koda Real ta ci Eibar ranar Lahadi, Barcelona za ta ci gaba da zama ta daya da tazarar maki biyu amma yanzu dai tazarar maki biyar kenan kan Real ta buga wasanta.

  Kuma na 200 da Zinedine Zidane zai ja ragamar Real Madrid a matsayin koci.

 5. Mallorca 0-4 Barcelona

  Lionel Messi

  Lionel Messi ya ci kwallo na 20 a gasar La Liga kuma karo na 12 a jere.

  A manyan gasar kwallon kafar nahiyar Turai babu wanda ya yi wannan bajintar tun daga kakar tamaula ta (2008-09-2019-20).

  Cristiano Ronaldo ya yi wannan bajintar da kaka 11 da ya dunga cin kwallo 18 a gasar Premier League tare da Man United itun daga 2008-09.

  Kai tsaye
 6. Mallorca 0-3 Barcelona

  Jordi Alba ya ci kwallo na uku mai kyau kuma ya yi murnar cin kallon mai kayatarwa.

 7. Mallorca 0-3 Barcelona

  Luis Suarez na saka kaimi ko zai ci kwallo na hudu imnda ya samu damai zai fita a guje sai mataimakin alakalin wasa ya daga tuta cewar ya yi satar gida.

 8. Kwallo na uku - Mallorca 0-3 Barcelona

  Jordi Alba

  Tun farko sai da aka yi tantamar kwallon da Jordi Alba ya ci yana ganin kamar ya yi satar gida daga bangaren hagun fili sai da aka je aka duba VAR ta tabbatar da satar gida.

  Da alama Barcelona ta hada maki uku a wasan nan za ta ci gaba da zama ta biyu ko da Real ta doke Eibar a ranar Lahadi

 9. Napoli 1-1 Inter Milan

  Napoli ta kai wasan karshe a Copa Italiya za ta fafata da Juventus ranar Laraba.

 10. Post update

  Video content

  Video caption: Yaya Muhammad - Mai goyon bayan Real Madrid
 11. Canji - Mallorca 0-2 Barcelona

  'Yan kwallon Barcelona, Arthur da Nelson Semedo za su shiga filin saura minti 20 a tashi wasa.

 12. Mallorca 0-2 Barcelona

  Kwallo mai kyau da aka yi ta bani in baka tsakanin Suarez da ya bai Messi tun farko shi ya sawa Suarez kwallo ya kuma mayar masa da ita sai Messi ya nemi raga amma kwallon ta bude ta yi waje.

 13. Mallorca 0-2 Barcelona

  Luis Suarez ya dawo wasa kenan. Y canji Antoine Griezmann.

  An sa ran Suarez ba zai sake buga kwallo ba a kakar bana kan raunin da ya yi.

  Sai dai cutar korona ta tsayar da komai tun cikin watan Maris hakan ya ba shi damar murmurewa har zai ci gaba da buga gasar bana.

 14. Post update

  Video content

  Video caption: Abdurrazak Hasan - Mai goyon bayan Real Madrid
 15. Mallorca 0-2 Barcelona

  Ivan Rakitic ya shiga fili dan kwallon Barcelona inda ya maye gurbin Arturo Vidal wanda ya ci kwallon farko..

  Mallorca ta saka 'yan wasa biyu.

 16. Yadda Barcelona ta ja ragamar zangon farko

  Kai tsaye
 17. Mallorca 0-2 Barcelona

  Mallorca ta kusan zare kwallo daya bayan da Dani Rodriguez ya bai wa Ante Budimir shi kuma ya buga kwallo ta je wajen gola.

 18. Ko Real Madrid za ta ci La Liga kuwa?

  Video content

  Video caption: Ma'aruf Bilyaminu - Mai goyon bayan Real Madrid
 19. Mallorca 0-2 Barcelona

  Kai tsaye