Ana 'tauye' hakkin wasu 'yan kwallon Afirka

yan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kashi kusan casa'in cikin dari na 'yan wasan kwallon kafa a Jamhuriyyar Dimokuradiiya ta Kwango ba su da rubutacciyar takardar kwantaragi

Wani bincike da aka gudanar kan harkar wasan kwallon kafa a sassan duniya ya nuna cewa yanayin rayuwar mafi yawan 'yan wasan kwallon kafa na Afirka yana nesa da irin hangen da ake yi wa rayuwa mai kayatawar ta wasu mashahuran manyan 'yan wasa wadan da suka yi dacen shiga manyan wasannin gasar kwallon kafa na duniya, Piers Edwards ya rubuta wannan rahoton.

Hadaddiyar kungiyar kwararrun 'yan wasan kwallon kafa ta duniya (Fifpro), ta gudanar da wani bincike a kan kusan 'yan wasa dubu goma sha hudu a kasashe hamsin da hudu, wanda shi ne irinsa mafi girma da aka taba yi.

Fiye da 'yan wasa dubu uku daga cikin wadanda aka gudanar da binciken a kansu, sun fito ne daga kasashe goma sha uku na Afirka, wadanda suka hada da Boswana da Kamaru da Jamhuriyyar Dimokuradiyya Congo da Masar da Ivory Coast da Morocco da Namibiya da Afirka ta Kudu, da Tunisya da kuma Zimbabwe.

Yayin da yawa daga 'yan wasan kwallon kafa masu tasowa na nahiyar Afirka suke burin zama Didier Drogba ko Samuel Eto'o, bayanan da aka tattaro a binciken da hadaddiyar kungiyar kwararrun 'yan wasan kwallon kafa ta duniya ta gudanar yana nuna mummunan yanayi game da ainihin yadda rayuwar dan wasan kwallon kafa take a nahiyar.

Bayanan bidiyo,

Ana tauye hakkin wasu 'yan kwallon Afirka

Cin Zarafi

Daya daga cikin abubuwa masu matukar girgiza zuciya da binciken ya gano, shi ne cin zarafin 'yan wasan Afirka ya fi na ko'ina muni a duk duniya. Wato al'amarin da ya hada da shure da duka da ingijewa da mari da dai saurasu.

'Yan wasan kasar Ghana sun dara sauran 'yan wasan duniya har sau nunki goma, wajen fuskantar wannan matsala daga manyan 'yan wasa na kungiyarsu.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Suna fuskantar cin zarafi iri daban-daban:

· Wariyar launin fata galibi daga 'yan kallo ko wasu 'yan wasan,

· Hari a kwaryar filin wasa ko a waje,

· Tsoratarwa wajen sa hannu a kwangilar wasa,

· Ware dan wasa gefe guda a matsayin wani horo.

'Yan wasa kuma sun koka da nuna masu matsanancin bambanci, al'amarin da hadaddiyar kungiyar kwararrun 'yan wasan kwallon kafa ta duniya ta rarraba zuwa ko dai na wariyar launin fata ko batun lalata ko kuma addini, walau daga 'yan kallo ko wasu 'yan wasan, ko masu horar da 'yan wasa ko kuma wasu mutanen daban.

Wani bakon abu kuma shi ne, al'amarin da za a iya kwatantawa da nuna bambanci wanda mafi yawan lokuta rarrabuwa ta fuskar addini iri wadda ake gani a Scotland tsakanin mabiya darikar cocin Katolika da na Furotesta.

Can ma a kasar Afirka ta Kudu da Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo, ana samun aukuwar kai wa 'yan wasa hari sau nunki uku fiye da yadda abin ya ke akasari a kasashen duniya.

Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kwango ta fi adadin 'yan wasa da 'yan kallo ke kai wa hari a rana wasa, sai Kenya na biye da ita a mataki na biyu.

Akwai kuma shaidar abin da hadaddiyar kungiyar kwararrun 'yan wasan kwallon kafa ta duniya ta kira '' kebe dan wasa shi kadai daga sauran jama'a'', al'amarin da kan kai ga shafar kwakwalwa.

Binciken ya kuma gano cewa 'yan wasan da mai yi wu wa za a ware su a yi masu nasu horon su kadai a Afirka suke, inda wannan ya shafi kashi kusan takwas cikin dari na 'yan wasa, fiye da nunkin na 'yan wasan Turai da Amurka.

'Yan was da dama a Afirka fiye da ko'ina sun ce ana yi masu hakan ne don a matsa masu lamba su sa hannu a kwantaragi.

Rashin biya mai kyau

Ta fuskar biyan hakki, kashi dari cikin dari na 'yan wasan kwallon kafa a kasar Ghana sun ce ana biyan su kasa da Dalar Amurka dubu daya ($1,000) ko fam dari takwas na Birtaniya (£800) a wata.

Kasar da aka fi biyan dan wasa albashi mai tsoka fiye da Dalar Amurka dubu daya ($1,000) a Afirka ita ce Marokko. Ko da yake can din ma ba su da wani tsaro a kan halin rayuwarsu na gaba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Duk da nasarorin da Zamalek ta samur ta samu a fagen kwallon kafa, tana kasa wajen biyan albashin 'yan wasa a wani bincike da aka gudanar

Gasar wasan kwallon kafa ta kasar Masar ana ganin ita ce mafi kwari a Afirka, wadda wasu kungiyoyinta biyu suka sami lambar yabo ta zakarun Afirka fiye da duk wata kungiya.

Al Ahly sun sami kyaututtuka takwas, Zamalek ta sami biyar. Amma kuma 'yan wasan gasar kwallon kafa ta Masar ita ce ta biyar wajen rashin biyan albashi mai tsoka a cikin kasashe goma sha uku da aka gudanar da binciken a cikinsu a Afirka.

Fiye da kashi casa'in cikin dari na 'yan wasa sun ce ana biyansu kasa da Dalar Amurka dubu daya a wata, abin da mai yi wu wa shi ne albashi mafi kankanta a Turai.

Balahirorin da suka auku a filayen wasan kwallon kafa a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu da goma sha biyar, sun jawo an hana 'yan kallon kwallo shiga kallo.

Binciken inda aka fi samun tsaikon biyan 'yan wasa albashi kuma a Afirka ne., inda fiye da rabin wadanda aka yi wa tambayoyi a binciken suka ce sun sha wuyar tsaikon biyan albashi.

A Gabon, kasar da za ta karbi bakuncin gasar wasan kwallon kafa ta Afirka a watan Janairun, kusan kashi casa'in da shida cikin dari suka koka game da tsaikon biyan albashi.

Kwantaragi

Nahiyar Afirka ce ke da adadi mafi yawa na 'yan wasan da ba su da wata rubutacciyar kwangilar wasa, inda binciken ya gano 'yan wasan da ke cewa ba su da kwafin takardar kwantaraginsu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Nahiyar Afirka ce ke da adadi mafi yawa na 'yan wasan da ba su da wata rubutacciyar kwangilar wasa

Kasashe uku da suka zama kurar baya a binciken su ne Kamaru (mai maki sittin da biyar cikin dari) da Gabon (kashi sittin cikin dari) da Ivory Coast (kashi sittin cikin dari).

Fifiko kulawar da ake yi wa baki 'yan kasar waje a Afirka a rayuwarsu ta yau da kullum ana ganin sakamakon hakan a kwallon kafar nahiyar.

A wani mataki da hadaddiyar kungiyar kwararrun 'yan wasan kwallon kafa ta duniya ta ce, yana ''kauce wa biyan haraji da wasu dokokin kare hakkin ma'aikata, da wasu tanade-tanade da za su kare ra'ayin 'yan wasa'', ana biyan da yawan 'yan wasan da ke Afirka ta wani tsarin kwantaragi wanda galibi ana biyan dan wasa bisa darajar kasuwarsa.

Abin mamaki, mafi yawan 'yan Afirka sukan sami albashinsu ta wannan fuskar, fiye da wadanda kasashen Turai masu cike da kyakkyawan fata.

A kasashen Gabon da Zimbabwe hakan ya shafi kashi talatin da biyu cikin dari da kashi talatin cikin dari na 'yan wasa.

Labari mai dadin ji

Amma kuma ba wai komai ne labari mara dadi ba game da binciken da aka gudanar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan wasan Tawagar kwallon kafa ta Ivory Coast sukan samu albashi mai tsoka

Idan ana batun ba 'yan wasa hutu, Ivory Coast da Namibiya suke kan gaba a mtsayin wani kyakkyawan misali, sakamakon yadda dukkan kasashen biyu suna ba 'yan wasa fiye da kwanaki talatin a matsayin hutu a kowacce shekara.

A wani arashi kuma, a kasar Masar abin ba haka yake ba, inda kashi casa'in da uku cikin dari na wadanda aka tambaya a binciken, sun ce sukan sami kasa da kwanaki goma a matsayin hutun shekara.

A kasar Tunisia kuma ana bai wa 'yan wasa fashin rana guda a duk mako a matsayin hutu.

A sauran kasashen nahiyar ta Afirka kuwa, kusan kashi daya bisa uku na 'yan wasan Afirka sun ce ba sa samun hutun rana guda cikakkiya a matsayin hutu a cikin mako guda.

Kariyar Aiki

Ba kamar wata nahiyar ba, 'yan wasa da dama suna cike da tsoro game da yadda al'amaura za su kasance masu nan gaba.

Yayin da aka tambayi 'yan wasa a kan ko suna da wata fargaba game da aikinsu? Sai 'yan wasan kasashe goma sha daya daga cikin goma sha uku na gaba-gaba suka bayyana irin wannan damuwa, dukkansu a nahiyar Afirka suke, duk da arzikin da ake ganin kasashen Morocco da Gabon suna kan gaba ta wannan fuska.

Tsara sakamakon wasa

Binciken baya can da hadaddiyar kungiyar kwararrun 'yan wasan kwallon kafa ta duniya (Fifpro) ta gudanar, ya nuna cewa rashin biyan 'yan wasa albashinsu ka iya zama babban dalilin karuwar yi wu war tsara sakamakon wasa tun ma kafin a buga kwallon.

Ga kuma matsalar albashi mara tsoka, shin a yi mamaki cewa Afirka tana kan gaba game da yawan aukuwar wannan matsala, abin da aka gano ya kai fiye da kashi takwas cikin dari a binciken da aka gudanar.

Wannan yana nufin kusan kashi casa'in da biyu cikin dari ba a tuntube su ba, adadin da ya kusa kama kafar na Turai mai yawan fiye da kashi casa'in da hudu cikin dari.

Haka nan kuma fiye da kashi goma cikin dari na 'yan wasan Afirka binciken ya nuna cewa suna sane da tsara sakamakon wasa in gasar da suke karawa, wato adadin da kadan ya dara na kasashen Turai mai kashi kusan kashi goma cikin dari.

Uku daga cikin kasashe biyar da ke kuka da wannan babbar matsala a kasashen Turai suke, yayin da adadin kasashen Afirka yana kasa da haka.

Labari mara dadin ji daga Jamhuriyyar Dimokuradiyya ta Congo

Da alamu, wata kasa ta karshe da ba za ka so ka zama kwararren dan wasan kwallon kafa a cikinta a Afirka, ita ce Jamhuriyyar Dimokuradiiya ta Congo.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kashi kusan casa'in cikin dari na 'yan wasan kwallon kafa a Jamhuriyyar Dimokuradiiya ta Kwango ba su da rubutacciyar takardar kwantaragi

Kashi kusan casa'in cikin dari na 'yan wasan kwallon kafa a Jamhuriyyar Dimokuradiiya ta Kwango ba su da rubutacciyar takardar kwantaragi., wannan kuwa wani adadi ne da ya nunka na duk wata kasa daga ciki kasashe hamsin da hudu da aka gudanar da binciken a cikinsu.

Adadin 'yan wasan da suka fuskanci hari daga wasu 'yan wasan a Jamhuriyyar Dimokuradiiya ta Congo ya nunka har sau uku na sauran kasashen duniya, bugu da kari, daya daga 'yan wasan kasar Congo hudu ya gamu da hari daga wajen 'yan kallo. Wannan kuma shi ne adadi mafi girma a binciken da ka gudanar.

Hatta harin da akan kai wa dan wasa a ranakun da ba wasanni ake yi ba, shi ma ya nunka har sau uku fiye da na sauran kasashen duniya.

Daya daga cikin 'yan wasa biyar sun ce, abokan wasansu sun tsoratar da su, kuma wannan adadi sun ce an nuna matsa masu lamba wajen sabunta kwantaraginsu, wani adadin kuma sun ce ba a matsa masu lamba ba.

Wata alama da ke nuna rashin kyakkyawan yanayin aiki shi ne, fiye da adadin 'yan wasan Congo sun ce ba su da hutun kwana daya a kowanne mako.