Ra'ayi Riga
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Matsalar garkuwa da mutane da 'yan bindiga ke yi a Najeriya ta sake dawowa a wasu jihohin.

Bayan 'yar lafawa ta wani dan lokaci, matsalar satar da garkuwa da mutane da 'yan bindiga ke yi a arewa maso yammacin Najeriya, yanzu ta sake dawowa a wasu jihohin.

Ko a farkon makonnan an sace mata da yara kimanin hamsin a kauyen Wurma na jihar Katsina; yayin da kuma aka yi garkuwa da wasu daliban jami'a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Mene ne ya haifar da sake dawowar matsalar kuma ina mafita? Wadannan ne batutuwan da za mu tattauna a filinmu na ra'ayi riga: