Coronairus: Muna cikin barazanar kamuwa da Covid-19 in ji Ma'aikatan jinya

Coronairus: Muna cikin barazanar kamuwa da Covid-19 in ji Ma'aikatan jinya

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Yau talata 12 ga watan Mayu ce ranar ma'aikatan jinya ta duniya.

Taken wannan shekarar shi ne 'shayar da duniya zuwa samun lafiya.

Wasu daga cikin ma'aikatan da ke aiki a Kanon Najeriya sun nemi a yi masu addu'a sannan a ba su hadin kai.

Ma'aikatan lafiya da dama sun kamu da cutar Covid-19 sakamakon yaki da cutar da suke yi.