Sadiq Abacha: 'An fi samun tsaro a lokacin mahaifina'

Sadiq Abacha: 'An fi samun tsaro a lokacin mahaifina'

Ku latsa alamar lasifikar da ke sama domin kallon bidiyon:

Bayan shekara 22 da mutuwar tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Janar Sani Abacha, iyalansa sun ce har yau ba su daina kewar mahaifinsu ba.

A wannan hirar ta musamman da BBC Hausa, daya daga cikin 'ya'yansa wanda yake da shekara 16 lokacin rasuwar mahaifinsa, Sadiq Abacha, ya bayyana abubuwa da yawa da suka biyo bayan mutuwar shugaban.

Sadiq ya ce 'yan Najeriya sun fi samun tsaro a lokacin shugabancin mahaifinsa.

Za ku iya kallon bidiyon cikakkiyar hirar mai tsawon minti 30 a BBC Hausa YouTube.