Bidiyo: 'Ina jin kamar na kashe kaina idan ina haila'

Bidiyo: 'Ina jin kamar na kashe kaina idan ina haila'

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

PMDD wato (Premenstrual Dysphoric Disorder) wani yanayi ne mai tsanani da wasu matan kan shiga idan suna haila.

Yanayin na iya sa mata su shiga cikin tsananin damuwa da bakin ciki har ma da tunanin kashe kansu a yayin da suke haila.

An yi kiyasin cewa mace daya duk cikin 20 na shiga wannan yanayin. A bara ne hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta dauki cutar da muhimanci.

Daga cikin matakan magance cutar har da cire kwayayen haihuwa.

Karin labaran da za ku so ku karanta