Bidiyo: Me ya sa waɗannan mazan suka harbe matar da take gudu tsirara?

Bidiyo: Me ya sa waɗannan mazan suka harbe matar da take gudu tsirara?

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Rikici na ci gaba da ƙamari a yankunan arewacin Mozambique.

Ana zargin dukkan ɓangarorin biyu na ƙungiyar da ta yi wa IS mubaya’a da kuma sojojin Mozambique da cin zarafin fararen hula.

A cikin wani bidiyo da ya bayyana a baya-bayan nan daga yankin, an ga wasu mutane masu dauke da makamai suna yi wa wata mata da take tsirara kisan gilla – amma, a ina ainihin lamarin ya faru kuma su waye mutanen?

Editan BBC Afrika Andrew Harding ya yi magana da masu bincike na ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam na Amnesty International da Human Rights Watch, da kuma wasu masu bincike na daban kamar su @il_kanguru, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa, don gano ainihin yadda lamarin ya faru.

Rundunar sojin Mozambique ta ce ba ta yarda da ‘’duk wani mummunan abu da ke da alaƙa da tayue haƙƙin ɗan adam ba.’’

Gwamnatin ta yi alƙawarin yin bincike kan bidiyon, amma ta ce an sassauya wasu abubuwa da ke cikinsa.

A baya dai an san masu tayar da ƙayar bayan da yin sojan gona ta hanyar sanya kakin sojoji.