Abin da ya sa shirin Buhari na shimfiɗa layin dogo daga Kano zuwa Nijar ya tayar da ƙura

Jirgin kasa

Asalin hoton, Nigeria Railway

Bayanan hoto,

Wasu 'yan Najeriya na ganin shimfida layin dogon ba shi da muhimmanci amma wasu sun ce zai bunkasa tattalin arzikin kasar

Matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na amincewa da ƙudurin shimfiɗa layin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Jamhuriyar Nijar ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar.

A ranar Laraba ne kakakin shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC Hausa cewa gwamnati za ta ciyo bashi don yin aikin, wanda zai laƙume kusan dala biliyan 1 da miliyan 96.

A cewarsa, aikin zai tashi daga jihar Kano ya ratsa jihohin Katsina da Jigawa ya kuma ƙare a jihar Maraɗi da ke Jamhuriyar Nijar.

Ya ce za a gudanar da aikin ne domin bunƙasa safarar kayayyaki.

Sabuwar kwangilar shimfiɗa layin dogon na zuwa ne daidai lokacin da Najeriya ke kukan ƙarancin kuɗaɗen shiga sakamakon raguwar kuɗin da ƙasar ke samu daga cinikin man fetur.

Kakakin shugaban ƙasar ya ce ana sa ran fara aikin a watan gobe kuma zai zama babbar nasara ga ƙasashen Najeriya da Nijar ta fuskar kasuwanci.

Wasu 'yan Kudancin Najeriya ba sa so

Sai dai tuni wasu 'yan Najeriya musamman waɗanda suka fito daga kudancin ƙasar suka fara tayar da jijiyoyin wuya kan shirin na Shugaba Buhari suna masu cewa bai kamata a a fita waje gida bai ƙoshi ba.

Henry Shield ya ce: "Kun karɓo bashi domin gina layin dogo daga Najeriya zuwa Jamhuriyar Nijar. Babu wata hanya kai tsaye daga Abuja zuwa Legas ko wani ɓangare na ƙasar. Kana ɗora wa Najeriya nauyin bashi."

Shi ma Miz Kazorla ya ce bai ga amfanin gina layin dogo daga Najeriya zuwa Jamhuriyar Nijar ba yana mai tambaya: "Wanne amfani ta fuskar tattalin arziki $1.96bn za ta kawo ta hanyar gina layin dogo daga Katsina zuwa Jamhuriyar Nijar?"

Shi ma Babasola ya bayyana cewa bai kamata a gudanar wannan aiki ba a yayin da 'yan Najeriya ce cikin ƙangin rayuwa.

"A wannan lokaci da 'yan Najeriya suke shan wahala mai tsanani amma gwamnatin nan ta mayar da hankali wajen gina layin dogo tsakanin Najeriya da Nijar," in ji shi.

Amfanin gina layin dogo daga Najeriya zuwa Nijar

Amma mutane da dama sun mayar da martani ga masu sukar wannan shiri suna masu cewa gwamnatin Buhari ta yi wa 'yan kudancin Najeriya goma ta arziki kodayake ba sa ganin hakan.

Entomhe Stephen ya ce: "Ku jama'a ba ku san amfanin wannan aiki ta hanyar tattalin arziki ba, ana gina layin dogo daga Najeriya zuwa Jamhuriyar Nijar ne domin a riƙa ɗaukar manyan kaya daga Legas zuwa Jamhuriyar Nijar wadda ba ta da hanyoyin jiragen ƙasa. Kuma ƙasashen da ke maƙwabtaka da Nijar za su iya shigo ta kaya ta hanyar bi daga Najeriya, sannan kuma layin dogon zai ratsa jihohi da dama."

A nasa ɓangaren, Abdullahi Ryda ya nuna muhimmancin gina layin dogon yana mai cewa "Ana shigowa da kayayyaki da dama daga iyakokin da ke kan tudu ta hanyar Jamhuriyar Nijar inda ake shigowa da su Najeriya ta jihar Jigawa (Mai Gatari), Katsina (Jibya), Sokoto, Kebbi. Hakan yana rage dogaro ga jihar Legas."

Shi kuwa Rabiata bayar da amsa ya yi ga masu tambaya kan muhimmancin yin layin dogon zuwa Nijar inda ya ce: "Najeriya da Nijar suna da dangantaka mai kyawu kan kasuwanci. Na samu damar yin kasuwanci da wasu mutane na Jamhuriyar Nijar kuma Najeriya tana samun haraji daga wurinsu. Babban ƙalubalen shi ne sufuri. Don haka ina ganin wannan shawara ce mai kyawu."