'Yadda ambaliya ta yi sanadin mutuwar ƴaƴana uku a Jigawa'

Ambaliyar ruwa

Asalin hoton, Getty Images

Ambaliyar ruwa na ci gaba da ɗaiɗaita al'ummomi a Nijeriya musamman a jihohin arewacin ƙasar inda take sanadin asarar rayuka da kadarori da gidaje da kuma amfani gona.

Ɗaya daga cikin jihohin ƙasar da lamarin ya fi shafa ita ce Jigawa, inda yanzu haka wakilin BBC Yusuf Ibrahim Yakasai ke wata ziyarar aiki.

A lokacin da ya ziyarci kauyen Kafin Ba-Ƙoshi, Yusuf ya taras da gini ya rufta kan wani mutum da iyalinsa, abin da ya yi sanadin mutuwar ƴaƴansa uku.

Mutumin mai suna Yakubu Usman ya yi wa BBC bayanin yadda lamarin ya auku:

Mallam Yakubu ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe biyar zuwa shida na safe bayan da "Allah ya saukar da iftila'in ruwan sama da ya janyo ambaliya a garin".

Ya ce a ƙalla za a sami ɗaki kimanin dubu ɗaya da suka faɗa bayan da ruwa ya mamaye garin.

Yadda ɗakina ya fada kan ƴaƴana

Yakubu Usman ya ce bai san lokacin da ɗakin nasa ya faɗo ba duk da cewa yana cikin ɗakin tare da iyalansa.

Ya ce su shida ke cikin ɗakin a wannan safiyar: Shi da matarsa, da kuma ƴaƴansu huɗu.

"Yadda ka san an cire min hayyaci na...ban san lokacin da ɗakin ya faɗo a. Sai da na duba kawai sai na ga cewa a wurin da yaran nawa suke kwance ɗakin ya faɗa kansu."

Shi ma wani ɓangare na ginin ya danne shi har sai da jama'a suka kai musu ɗauki kafin aka iya ciro shi.

"Mutane sun zo da mugirbai sai na ce musu kar ku yi amfani da su domin akwai mutum a karkashin wurin."

Ya ce ta da hannu aka riƙa amfani ana zaƙulo ƴaƴan nasa daga ƙarƙashin ƙasar ginin.

Da aka tambaye su ko a wane hali aak ciro yaran nasa, sai ya ce ɗaya ne kawai ya nuna alamar yana da rai:

"Mun tafi da su asibiti amma babu wanda ya tsira da ransa, kuma haka muka dawo da su gida aka yi musu jana'iza."

Amma akwai mace ɗaya cikin ƴaƴan nasa da yace Allah ya kuɓutar da ita.

Bayanan sauti

Ambaliya: Na rasa ƴaƴana uku

Mun shaƙu ni da ƴaƴana

"Shakuwa dai ba a misali tun da ko wurin kwanci ba sa son rabuwa da ni. Har faɗa suke yi ma a daren da hakan zai faru, suna cewa 'Ya za a yi wane zai je wurin baba a ce ni ban je ba'."

"Ka tuna cewa kwuikwuiyo ma za ka dauka kaga kana sonsa. To ya kuma kaga mutum?"