Me kuka sani game da gidan Sardauna Ahmadu Bello da ke Kaduna?

Me kuka sani game da gidan Sardauna Ahmadu Bello da ke Kaduna?

Latsa hoton sama domin kallon ɗakin Sardauna a Kaduna

Gidan Arewa, shi ne asalin gidan Sardauna, kuma yanzu Cibiyar Bincike da Adana Tarihi na Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, Najeriya.

An kafa cibiyar ne bayan kisan gillar da aka yi wa Firimiyan Arewa na farko Sardauna, a juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 1966.

BBC ta samu shiga wannan cibiya kuma har cikin ɗakin Sardaunan Sakkwato Ahmadu Bello Firiminiyan Arewa.

Daga cikin abubuwan tarihi da BBC ta gani a Gidan Arewa akwai 'inda aka samu gawar Sardauna, wanda yanzu aka killace domin nuna alama.

Mun samu damar shiga falon Sardauna inda muka ga kayan da ya yi amfani da su. Mun ga gadonsa da agogonsa da darduma da carbi da littafin addini.

Ɗaukar bidiyo da tacewa: Yusuf Yakasai