Bidiyo: Ƙauyen da aka kashe mazaje aka bar matansu cikin tasku a Afghanistan

Bidiyo: Ƙauyen da aka kashe mazaje aka bar matansu cikin tasku a Afghanistan

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A yayin da ake ƙoƙarin sasantawar zaman lafiya, ana ci gaba da samun ƙaruwar tashe-tahsen hankula a Afghanistan.

Yankin Nangarhar da ke fama da rikicin ƙungiyoyin Taliban da na IS, ya kasance wani waje da rikicin ke shafar fararen hula.

Wakilin BBC Ali Hussaini ya ziyarci wani ƙauye a yankin da ake kira ‘valley of widows’ wanda aka shafe shekara guda zuwa yanzu ana zaman makoki.

Wani harin ƙunar baƙin wake da aka kai wajen ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 60, inda aka kashe dukkan mazajen da ke cikin wasu iyalan.