Bidiyon Ku San Malamanku tare da Dr Sani Rijiyar Lemo

Bidiyon Ku San Malamanku tare da Dr Sani Rijiyar Lemo

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Babban malamin addinin Musulunci a Najeriya mazaunin jihar Kano a arewa maso yammacin ƙasar, Dr Sani Umar Rijiyar Lemo ya ce ya rubuta tafisirin littafin Al-Ƙur'ani mai girma ne don fayyace ma'anoninsa da kuma hukunce-hukuncen da ke tattare da su.

Tafisirin dai shi ne irinsa na farko da aka buga da harshen Hausa, inda ya bambanta da na marigayi Sheikh Mahmud Gumi da marigayi Sheikh Nasiru Kabara ta wajen wajen fito da hukunce-hukuncen ayoyin da kuma ƙarin bayani kan ma'anoninsa, da dangantakarsu da Hadisai.

A farkon watan Nuwamba ne Dr Rijiyar Lemo, wanda Malami ne a Fannin Koyar da Addinin Musulunci a Jami'ar Bayero ta Kano ya fitar da Tafsirin Al-Ƙur'anin wanda tuni aka fara fansar da shi a kasuwa.

Malamin yana daga cikin malaman Najeriya da suke yawan rubuce-rubucen manyan littatafai da suke shiga duniya.

A lokacin da wakilin BBC Yusuf Ibrahim Yakasai ya je don hira da shi a shirin ''Ku San Malamanku'' ya ga ɗumbin littattafai a tare da shi, kuma ya ce tun yana sakandare yake sayensu.