Coronavirus: Ƴar shekara 90 da aka fara yi wa allurar riga-kafin cutar korona a duniya

Coronavirus: Ƴar shekara 90 da aka fara yi wa allurar riga-kafin cutar korona a duniya

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wannan bidiyon na nuna yadda aka yi wa mutum ta farko allurar cutar riga-kafin korona a duniya bayan an kammala gwajinta.

Margaret Keenan, wacce za ta cika shekara 91 a mako mai zuwa ta zama ta farko da aka yi wa allurar riga-kafin kamfanin Pfizer/BioNTech da ba ta gwaji ba.

Birtaniya ta zamo ƙasa ta farko a duniya da ta fara amfani da riga-kafin na Pfizer bayan da hukumomi suka amince da ita a makon da ya wuce.

A yanzu an kammala shirin yi wa ƴan sama da shekara 80 allurar da kuma wasu ma’aikatan lafiya, sai dai ba kai tsaye ake yi ba saboda salon yadda ake bi ana adanata.

Wasu labaran da za ku so ku karanta