Bidiyon Ku San Malamanku tare da Ustaz Husaini Zakariyya
Bidiyon Ku San Malamanku tare da Ustaz Husaini Zakariyya
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A wannan makon mun kawo muku tattaunawar da muka yi da Ustaz Husaini Zakariyya, wani malamin addinin Musulunci a Abuja, babban birnin Najeriya.
An haifi Ustaz Hussaini Zakariyya Yawale a garin Kaduna ranar 1 ga watan Oktoban 1960 a unguwar Abakwa, wanda ya yi daidai da 10 ga Rabi'u Thani shekara ta 1380 bayan Hijira.
Mahaifinsa malamin addinin Musulunci ne na Mazhabar Malikiyya kuma a hannunsa ya fara karatu.