'Na fi jin dadin zaman gidan yari fiye da rayuwar 'yanci'

'Na fi jin dadin zaman gidan yari fiye da rayuwar 'yanci'

Wani mutum da aka saki daga gidan yari a Najeriya bayan an yi masa afuwa ya ce ya fi son zaman gidan yari fiye da rayuwa a waje, kasancewar ba shi da wata madoga a rayuwar waje.

An samu Gambo Mohammed da laifin kisan kai sakamakon fada da suka yi da wani a shekarar 2000, kuma da fari aka yanke masa hukuncin kisa, sannan daga baya aka mayar da shi daurin rai da rai.

Gambo na daga cikin mutanen da aka yi wa afuwa a yunkurin rage cunkoso a gidajen yarin Najeriya saboda bullar cutar korona.

Ya samu 'yanci ne bayan shafe shekara 21 a gidan yari. Ya ce bayan sakinsa sai da ya ringa tambaya kafin ya je gidansu.

Sai dai ya ce duniya ta sake yi masa zafi bayan da ya tarar mahaifinsa ya rasu, sannan an sayar da gidansu na gado. Don haka ya samu kansa a yanayin rashin inda zai zauna.

Yanayin rayuwa da rashin kudi da sana'a sun kara jefa shi cikin wani mawuyacin hali, inda abinci da ruwan da zai sha suke yi masa wahalar samu.

Hakan ta sa shi yanke shawarar zabar zaman gidan yari fiye da sabuwar rayuwar da ya samu kansa a cikinta yanzu.

Gambo ya ce sau uku yana komawa gidan yari da niyyar neman ba shi damar ci gaba da rayuwa a gidan yarin, inda a cewarsa ko ba komai zai ringa samun abinci da zai ci sau uku a rana ya kuma samu ruwan sha ba tare da wata matsala ba.

To sai dai yace ma'aikatan gidan yarin sun ki ba shi damar komawa cikin daurarrun.

Ya ce a lokacin da yake zaman gidan yarin, ya mayar da hankali wajen karatun Alkur'ani, har ma ya yi sauka da dama.

Jin wannan labari na sa ya sa wata mata ta bayyana aniyar aurensa, sannan wani mutum ya yi masa alkawarin ba shi gidan da za su zauna, da kuma ba shi jari da zai kama sana'a.

To amma a cewar Gambo babu wani tallafi da ya samu kawo yanzu, don haka ba a daua auren na su ba tunda ba shi da inda zai zauna da iyalinsa, kuma ba shi da halin da zai rike matar.

Gambo ya nemi jama'a su taimaka masa ya gina sabuwar rayuwa.