Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A wannan karon, shirin Ku San Malamanku ya samu zantawa da daya daga manyan malaman Najeriya kuma babban jagora a darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

A cikin hirar, Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana yawan 'ya'yansa da malaman da ya yi karatu a wajensu da kuma haduwarsa da babban malaminsa Sheikh Ibrahim Inyass.