Bidiyon mutum na farko da aka yi wa allurar riga-kafin korona a Najeriya
Bidiyon mutum na farko da aka yi wa allurar riga-kafin korona a Najeriya
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A ranar juma'a 5 ga watan Maris ne aka fara yi wa mutum na farko allurar riga-kafin cutar korona a Najeriya.
An fara yi wa Dr. Thairu Yunusa allurar ne a Babban Asibirin Ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.
A cikin wannan makon ne Najeriya ta karbi riga-kafin korona da ake sa ran fara yi wa ma'aikatan lafiya a yau.
An kuma tsara cewa za a yi wa shugaban ƙasar Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo ta su riga-kafin a ranar Asabar