Bidiyo: Tsibirin da yara hudu ne kawai suke rayuwa a kansa

Bidiyo: Tsibirin da yara hudu ne kawai suke rayuwa a kansa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Lyoo Chan-Hee na daya daga cikin yara hudu kacal da suka rage a tsiribin Nokdo na kasar Koriya ta Kudu kuma burinsa daya ne kawai – fatan samun karin abokai da zai rika wasa tare da su.

Tsibirin wata alama ce da ke nuna matsalar karewar mutane da kasar ke fuskanta lamarin da ke faruwa sanadiyar yawaitar tsofaffi da kuma karancin haihuwa.

Bankin Duniya ya ce tsibirin ya kasance kan gaba cikin al’ummar da ta fi jama’ar da suke fama da yawaitar tsofaffi yayin da take karancin haihuwa a shekarar 2020.