Hanyoyin da za ki mallaki miji ba tare da illata abokiyar zama ba

Hanyoyin da za ki mallaki miji ba tare da illata abokiyar zama ba

Ana yawan samun rahotanni cewa kishiyoyi suna azabtar da kishiyoyinsu, musamman ma duk lokacin da aka ce mijinsu zai kara aure.

A baya bayan nan an samu rahoton wata uwargida da ake zargin ta kashe amaryar da aka yi mata a birnin Minna na jihar Neja a arewacin Najeriya.

Lamarin ya tayar da hankalin 'yan kasar.

Masana na ganin akwai hanyoyi masu dimbin yawa da mace za ta bi ta mallaki mijinta ciki ruwan sanyi ba tare da ta hada da barazana da rayukan wasu ba.

Badriyya Kalarawi ta yi duba kan wannan batu.